KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

Halsey tace muga paper din, ihu ta kwalla lokacin da taga cewa dakinsu daya tace dakin mu daya muje! muje! muje! Unpacking kayan zayya sukayi halsey na fada Mata duk wani information da ya dace ta sani da yar iskar makarantar tasu.

Wayanta halsey ta dauko suka dauki selfies. Daddare zayya ta dauko diary dinta ta fara rubutu:

MONDAY¨C 6 JUNE

Yau nazo sabon makaranta na kuma wallahi kyau gareshi gashi nayi kawa mai suna halsey saide akwai wata banziya wai ita vanessa amma zanyi maganinta idan ta shiga sabga ta.

Don’t forget to VOTE, comment and share love you all.

Miss Untichlobanty ?

15th April, 2020.

?? KURUCIYAR MINAL??

? By miss Untichlobanty ?

? CHAPTER 85?

RECAP

Wayanta halsey ta dauko suka dauki selfies. Daddare zayya ta dauko diary dinta ta fara rubutu:

MONDAY¨C 6 JUNE

Yau nazo sabon makaranta na kuma wallahi kyau gareshi gashi nayi kawa mai suna halsey saide akwai wata banziya wai ita vanessa amma zanyi maganinta idan ta shiga sabga ta.

CONTINUATION

Halsey ne tace zayya ki tashi muje muci abinci, zayya tace okay tare da rufe diary dinta suka fita. A layin siyan abinci ma haka aka dinga kallonta itako babu abinda ya shafeta.

Cikin dare suna bacci sukaji ansaki key a kofar dakinsu za’a bude. Textbook zayya ta dauka yayinda halsey ta dauki takalmi. Zayya ne ta bude tare da rafka ma Wanda ke bakin kofan textbook ashe hostel incharge ce ta kawo musu roommate dinsu me suna “na yeonsil” yar southern Korea ce.

Washe gari aka fara karatu zayya da taga ba gane komai take ba kawai tayi kwanciyarta.
Mafarki ta fara yi wai gata a kwace sanye da? kayan snow white sai? ga yarima yazo ya sumbace ta murmushi tayi ta fara bude idonta a hankali amma me tana bude idonta ta soma ihu tsabar muninsa.

Aiko ihun ta kwalla a gaske tana mai goge bakinta da tufarda da yawu, bai tsaya a ko ina ba sai fuskar malamin su yayinda kowa ya tsura Mata ido.

Detention ticket (tikitin ladabtarwa) aka yanka Mata, cikin harshen hausa tace kai nikam na shiga uku tun ranar farko zan fara shiga detention? Malamin nasu Dan Korea ne yace kimin shiru kamin na mauje ki sannan yaci gaba da darasi.

Lokacin break suka shiga ban daki domin gyara kwalliyar su kamar yadda kukasan al’adar farin fata. Zayya kam watsawa fuskarta ruwa tayi tare da sauke ajiyan zuciya tace in tambayeki mana halsey.

Idan mutum yayi mafarkin Dan sarki me hakan ke nufi? Halsey tace me kukayi dashi a mafarkin? Dan Sosa kai tayi tace kawai rike hannu mukayi. Tunani halsey tayi tace nide ban gane ba. Yeonsil dake kan shadda idan ta fadi ko wani kalma sai tayi nishi tace hakan na nufin zaki hadu da masoyinki a gaske. Juyowa sukayi su duka biyu suka kalli kofar ban dakin da take sai ki kake fatatata ta saki zawo.

Zayya kuwa gira daya ta daga ta ce WAYE SHI?…….
Bayan an tashi gaba daya zayya tayi sneaking ta fita daga makaranta ta siyo popcorn tana tafe tanacin abinta. A hanyarta na dawowa makaranta tayi Tuntube ya zube hakan yasa ranta ya baci ga su halsey na kiranta wai tayi sauri ta dawo kar a gane batanan. Tuno baki tayi tana tafiya tana kwallo da duk abinda ke gabanta.

Sahir ke take totir din motansa me budadden sama kawai yake Dan ya samu yancin watayawa babu speed limit a Nigeria shiyasa ma yaki fitowa tare da safwan.

Zayya kuwa wani gwangwani ta gani a gabanta cikin nauyin zuciya tayi shot dashi bai fada a ko ina ba sai goshin sahir aiko ya daki streetlight Wanda hakan yasa ya fara habo yayinda taci gaba da tafiyarta tanaji kamar tayi kuka.

Fitowa yayi tare da daukan gwangwanin dadin abun hanyar babu kowa. Yace hey! Ke ! Ke me UNIFORM! Juyowa tayi cikin harshen turanci yace bakida hankali ne? Tace kai kuma waye kai? Yace waye ni? Mamallakin wancan motar tare da nunawa da yatsarsa. Tace toh sai akayi yaya? Me alakata a ciki? Ta fadi haka fuskarta na nuna alamun rashin fahimtan inda ya dosa

Iska ya furzar tare da nuna Mata gwangwanin yace ke kika jefar da wannan? Tace bani bace. Yace amma ke kikayi kwallo dashi ko ta daga kai. Cikin masifa yace kaji karamar yar iska kin dauka lamarinnan wasa ne? Saura kiris ki kasheni !

Itama cikin daga murya da canja Fuskar abin tausayi zuwa yatsine tace me kake nufi ? ai ba da gangan nayi ba. Kuma wallahi ka fita daga idona na rufe Dan yanzu haka raina a bace yake.

Yace dalla dubata ni zakiyi wa barazana? Yanzu abar wannan magana zuwa anjima. Ya zakiyi da motata?
Fuskar kulya tasa adan shagwabe tace da alamu kai Dan masu kudi ne, abar maganan kaji? Yace kai ni warin talauci ma nakeji. Kasa kasa tace koma dai menene banza me mako kawai. Yace me kika ce? Tace karka damu zan biya kudin gyaran nawa ne? Yar bazawar dariya yayi yace kinsan nawa ne kudin motan nan kuwa?

Tace nawa ne? Murmushi yayi yace bar wannan zancen, tunda ke daliba ce zan miki ragi muyi 50 50 ki bada rabi in bada rabi. Tace nawa kenan yace ki kawo dala dubu Goma $10,000. Ido ta zaro tare da Jan numfashin da bata shirya ba tace mene? Yace bakiji ba? Cewa nayi $10,000. Tace la ga yan sanda nan sunzo ma. Juyawa yayi yana juyowa yaga wayam ta arce iska ya nausa tare da fesar da iskar. Yana shirin juyawa yaga wallet dinta. Dauka yayi yaga student ID card dinta a ciki yace hmm zamu hadu sannan ya shige mota.

???Zayya tana kwance a hostel tana bacci taji Karan motan yan sanda ta cikin speaker sukace zayyana mainasara you are under arrest kiyi saranda ko mu miki karfa karfa, kin dauka zaki rusa masa mota ki tsira ne?? Da sauri ta leka window aiko motocin yan sanda ne guda 10 gaba daya sun saita window dinta da bindiga. Shugaban yaci gaba da cewa bazaki iya arcewa ba kiyi saranda kawai ko muyi harbi sauri tayi ta rufe window ta hanyo hularta da akwatinta sai ruwan bullet kakeji aiko ba shiri ta kwanta luf.???

Vibration din da wayanta yayi yasa tayi firgigit ta tashi daga mafarkin da take tare da sauke ajiyan zuciya ta goge gumin da ya tsattsafo Mata tare da kara wayar a kunnanta tace hello ? Ta dayan bangaren yace NINE! Tsaki taja tace me kuma kakeso yace AI bamu gama da case dinmu ba. Cikin tsiwa tace wani case kuma Bayan an wuce wajen? Tsk ince nabar muku makarantar Dan haka ka dena takura mini kaji ko? Ta karashe tana mai daga murya. Kallon wayan yayi kamin yace lafiyarki kuwa? Ko kan da matsala ne? Tace kai Aminu Yusuf kanason ka mutu ne? Yace Aminu Yusuf? Waye shi? Nifa SAHIR YAZEED ABDULMAJEED? UMAR ne.

Tace mene? SAHIR YAZEED ABDULMAJEED UMAR? hmm waye kai? Yar murmushi yayi yace nine mamallakin Lexus dinnan da kika bata ko ince kika rusa.? Zaro ido tayi tare da zare sim din wayar ta fara kukan shagwaba.

Bayan Sati daya minal da feena sun fito shopping kawai sukaji ana sanarwa wai customers suyi hakuri su fita baban mutum zai shigo. Minal tace wallahi babu inda zani ko shugaban kasa ne zai shigo, yo menene za’a wani shiga hakkinka. Ince duk Abu zamu siya? Feena ne tace nide yaya minal kinga tafiya ta minal tace jeki.

Yazeed yana cikin shopping din inner wears dinsa Dan baiyarda a siyo masa saboda kar a cutar dashi. Yaji kamar karan takalmi coge ta dayan bangaren kewaya wa yayi yaga wata macece amma bayanta yake gani tana siye siyenta. Body guard dinsa ne yace malama ke kurmace da za’ayi sanarwa a fita ke ki zauna a ciki kin wani dibo hijab kamar….. yazeed ne ya daga masa hannu yace karka zagi hijabi domin yanada muhimman ci a addini amma mafiya yawa Mata basusan da hakan ba Dan haka ka daraja mai hijabi balle ma irin su Abuja ai sai an daure za’a saka shi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button