TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL
A palo ta fara tsayawa tana bawa yaran ta directives na yadda zasu gyara gidan, sannan tayi musu sallama ta hau sama. Dakin ta ta shiga ta fara yin wanka ta shirya cikin kayan bacci masu daukan hankali ta dauko ajjiyoyin kayan matan ta ta sha na sha ta shafa na shafawa. Tunda suka yi aure bai taba resisting dinta ba kuma bata jin zai fara daga yau.
Tunda Ruqayyah ta juya ta fita Hassan ya zame ya zauna a bakin gado ya dafe kansa da hannayensa biyu. “What just happened? What happened to his perfect precious wife? Did she just said what she said ko kuma zuciyarsa ce take playing tricks on him? Ta tabbas there must be an explanation to her behavior ko dai yayi mata wani laifi ne mai girma da out of anger ta fada masa haka? Amma shi duk a tunaninsa bai tuno wani abu da yayi mata marar dadi ba.
Ya tuna a yanayin da ta gaya masa maganar, babu wani emotions irin kamar normal mutum yana magana ne directly from her heart, daga dukkan alamu itama bata san ta fada ba sai bayan data fada din. Zuciyarsa tana ta kokarin kawo masa wani excuse da zai kare ta amma kwakwalwar sa taki karbar excuse din, sai ma wadansu maganganu da suke fado masa a rai.
Farko maganar Baba “zan so ka janye auren Hassana ka auri Hussaina a madadin ta”
Hussain “in har zata iya yaudarar top criminals ta haka mudu rami su fada ciki why not you?”
Sumayya “kayi ta hakuri, kana addu’a kuma kana saka ido”.
Ya mike yana jiyo karar kidan da suka kunna a kasa, Yusuf ya fara kuka, ya dauke shi yana rarrashinsa, Aminu ya saka kuka shima yana miko masa hannu, ya durkusa shima ya dauke shi yana zagaya wa dasu a hannunsa yana raba idonsa a tsakanin fuskokin su. Sai ya samu kansa da tambayar kansa
“Did he make the worse choice for the most important thing?”
“Did he chose a bad wife for himself and a bad mother for his children?”
Where was his carefulness?
Ya shiga da yaran toilet dinsa ya saka su a wash hand basin ya wanke musu jikin su da ruwan dimi, suna ta wasa suma jika shi, ya fito da su ya kashe acn dakin ya goge musu jiki sannan yaje dakinta ya samo musu kaya yazo ya saka musu, ya koma ya dauki madara ya hada musu ya basu, a take suka yi bacci ya kwantar dasu yana kallon su sannan shima ya kwanta a tsakiyar su tare da rufe idonsa, amma bacci shine abu na karshe a zuciyarsa.
“At least haka akeyi a gidan arziki, da Hussain ne da haka zaiyi va wai ya zauna yana complain akan abinda akayi shekara guda data wuce ba”
Ya girgiza kansa yana son ya cire maganar ta daga cikin kansa amma ya kasa. A haka yaji ta bude kofar dakin ta shigo ta tsaya tana kallon su
Ta dan jima a tsaye tana assessing din sa shi da yayansa, yaran bacci suke yi amma shi tana kallonsa ta san idonsa biyu rufe idon kawai yayi. Ta karasa tare da dauke Yusuf ta mayar dashi kusa da dan uwansa sannan ta zauna a inda ta dauke shin tana dora hannunta akan goshin Hassan. Ya bude ido yana kallon ta, tayi masa murmushi “dama nasan ba kayi bacci ba shine ka wani rufe ido ko?” Bai ce mata komai ba amma ta hango wani bakon al’amari a cikin idon nasa, tace “wai fushi kake yi dani mijina? Kayi hakuri mana dan Allah ai kasan dai babu wani wanda yake baya kuskure a rayuwa ko? Nayi kuskure, raina ne naji ya baci a lokacin ka yafe min kaji mijina?” Sai taga yayi dan murmushi, a take taji hankalin ta ya kwanta, dama ta san babu inda fushin nasa zai je in dai har ta bayar da hakuri musamman kuma ace da wannan shigar a jikinta tana kuma wannan kamshin ai magana ta riga ta wuce. Sai taji yace “ranki ne ya baci ko? Kinsan wani abu. A lokacin da ran mutum ya baci a lokacin ne yake fadar duk abinda yake cikin zuciyarsa, so chances are very high cewa abinda yake zuciyarki shi kika fada min” ya fada idanuwan sa cikin nata.
Ta fara jujjuya hannunta tana kokarin controlling anger dinta tace “don’t be like that mana, haba mijina, ya kamata kayi min uzuri mana. Nima fa ina da zuciya a kirjina, kuma zuciyata tana son irin rayuwar su Hussain da matarsa yadda suke wadaka da dukiya suna zuwa duk ƙasar da suka ga dama a lokacin da suka yi niyya. What do you expect your wife to do? How do you expect me to feel bayan ka kawo ni ina zaune da kanin ka da yake da everything while you have nothing?”
Ya mike zaune yana kankance idonsa a kanta, “do you just said “nothing”? Do you mean I have nothing?” Ta juya idonta, yau me yake faruwa ne da ita? Me yasa bata da sa’ar magana ne? Daga dukkan alamu yau da hannun hagu ta tashi daga bacci.
Tace “ah ah. Me kake so ne ince mijina? Ina nufin kamfani nasa ne, gidan nan da muke ciki nasa ne, motar da kake hawa tasa ce, motar da nakr hawa shi ya siya. Komai da muke takama dashi a rayuwa nasa ne” ya ture hannunta daga jikin da ya mike tsaye, idanunsa sunyi ja jijiyoyin kansa sun fito, ya bude bakinsa zaiyi magana amma voice din ya kasa fitowa saboda ciwon da zuciyarsa take masa, da kyar yace “I understand. I now understand everything. Ni da ke Hassana yanayin yadda muke kallon rayuwa ba iri daya bane ba. Rayuwa ni a gurina ba wai tana revolving around yawan kudin da kake dashi bane ba, tana revolving ne around things that are much more important than money, like love, honor, friendship. But you have no idea me wadannan suke nufi do you? Yes, Hussain yana da kudi, but that doesn’t mean ni bani da komai. Yes, gidan sa ne wannan shi ya gina da kudin sa but that doesn’t mean ni bazan iya gina nawa ba. Na karba na zauna a ciki ne dan in faranta masa tunda burinsa shine mu zauna tare mu da iyalin mu, saboda yana so na, nima kuma na karba saboda ina son sa. Na fasa gina mana namu gidan ne saboda in siya wa Baba gida, saboda naga yafi mu bukata, saboda ina ganin sa kamar family na ne shima”
“Ruqayyah bayan rai da lafiya da imani da Allah ya bani sai ya bani family, Aunty da siblings dina, masu sona sosai yadda na tabbatar ko da bani da komai zasu kula dani, ko d abana duniya zasu kula da bayana. Sannan ina da aikin yi ba zaman banza nake yi ba, wahalar da nake yi a aikin nan shi kansa Hussain yasan cewa ko shi baya yiwa kamfanin nan wahalar da nake yi masa. Ke kinfi kowa sanin cewa albashi na can more than sustain me, you and ko yaya nawa zamu haifa. And I have these….” Ya fada yana nuna babies din da suke bacci abin su “I have abinda babu wanda ya isa ya samar wa kansa sai Allah ya bashi. Do you know that last week Fatima ta matsawa Hussain sun fara zuwa ganin fertility doctor? Suna nema but mu Allah ya bamu gida biyu” ya tsaya yana kallon ta da jajayen idanuwan sa yace “I tot I also have a pious wife. Ashe I was wrong” ya bude toilet ya shige ya rufo kofa. He just can’t stand the sight of her.
Ta mike tsaye tana kallon kofar toilet din, tunda taaure shi tasan baya son nonsense shi yasa kullum in suna magana take jinta kamar mai tafiya akan tight rope kamar slight mistake in tayi zata fada ramin da ba zata iya fitowa daga ciki ba. And yau ta tabbatar da haka.
Ta mike itama ta fice daga dakin ta koma nata dakin, tasan dama dole watarana sai haka ta faru a tsakanin su amma bata dauka hakan zata faru da wuri ba, plan dinta shine ta haifa masa as many yaya as possible yadda babu yadda zai yi da ita. Ta tsaya tana kallon sticker din data lika a jikin mirror dinta