BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Episode 9

…………..GOVERNMENT HOUSE

    Sosai jam'iyya mai mulki ke shirin kamawa da wuta a wannan ɗan tsukun a dalilin shirun party Chairman da shugaban ƙasa game da batun ɗan takara. Bakajin komai sai tsugunne-tsugunne da kace nace. Dan a wannan gaɓar ba wai jinta bakin su party Chairman ne kawai keda amfani ga jamiyya ba. Hatta manyan jam'iyar an zuba musu na muzurune game da kaiwa da kawowa da suketa famanyi cikin duhun dare.
  Wasu a cikinsu na goyon bayan shugaban ƙasa ne kai tsaye, yayinda wasu ke kaiwa da komowane akan nasu ƴan takarar da suke fatan a tsaida domin cancanta ko wani burinsu na daban tamkar yanda shima shugaban ƙasa keda tasa manufar shi da muƙarabbansa na bayan fage, harma da wanda suke a cikin tafiyar mulkin tsundum.

01:32am

     Agogo ya nuna a sirrintaccen falon dake fadar shugaban ƙasa ke ganawa da shaƙiƙansa na siyasa masu faɗa aji a bayan fage dama a zahiri ga jam'iyyar. A zahiri su ɗin manyane na ƙasa da ko kwatancen arziƙi sukai da kai idan da rabo sai ka haye. Da taimakonsu shugaban ƙasa ke mulki bayan UBANGIJI ya ƙaddara hakan, duk da dai akwai wasu gwasaken ɓoyayyu. Inda yay biyayya ga dukan tsarinsu ya mora suka mora. Daɗin hakan yasa basa buƙatar kuɓucewar mulkin a hannunsu, gudun kar wanda zai faɗa a hannunsa ya gagara zama ƙarƙashin mulkin mallakarsu da faɗa aji. Hakan yasa su yanke shawarar sake ɗora wanda zai iya binsu sau da ƙafa, sai dai sun hanga sun hango matsalolin dake cikin hakan ga dukkan waɗanda suka hasaso ɗin kai tsaye. Da ga ƙarshe bayan wasu dalilai suka yanke shawarar bama tsohon Alƙali kuma shahararren ɗan kasuwa Alhaji Hameed Taura takarar, da shirin bayan anyi komai an gama mulki ya samu zasu salwantar da rayuwarsa wanda zasu bama mataimakinsa ya maye gurbinsa. Sunyi wannan tunanin duk da cewa Alhaji Hameed Taura ɗayane da ga cikinsu, sai dai sam baisan akwai wata alaƙa a tsakaninsu su huɗu da suka killace kansu da itaba wadda babu shi. Sannan baisan ɓoyayyar manufarsu mummuna akansa ba tun shekaru masu yawa da sukasha auna rayuwarsa ba'a dace ba, saboda kwanansa basu ƙareba dan a hannun ALLAH suke. Babban dalilin zaɓarsa domin sake kawo kujerar shugaban ƙasa yanada alaƙa da farin jinin da ALLAH yay masa ga al'umma saboda ɗunbin ƙyautatawarsa ga talaka. Bashi da ƙyashi balle wulaƙanci. Ya cicciɓa mutane da yawa talakawa da sukai arziƙi a ƙarƙashin dukiyar da ALLAH ya mallaka masa. Bashi da girman kai, bashi da izza. Sannan baya ɗaukar raini ga dukkan wani maiji da kansa koda ace ya fisa arziƙi ne. Bai taka kowa bai yarda a takashiba shima.
  Su kansu kusan kaso biyu bisa ukun dukiyoyinsu kaso biyu na Alhaji Hameed Taura ne. Wannan yana ɗaya daga cikin manyan dalilan da yasa zukatansu suke jin tsoron kar wataran ya amsa su koma baya. Shiyyasa suka sha auna halaka rayuwarsa amma ALLAH baisa sun dace ba. Hatta ɗansa *Basheer Hameed Taura* sunsha kai masa hare-hare ALLAH na kareshi. Rashin nasarar hakan ta sakasu komawa kan jikansa namiji tilo shima guda ɗaya a cikin ƴaƴa goma sha shidda da ɗan nasa Basheer Hameed Taura ya haifa mai suna *_RAMADHAN B. HAMEED TAURA_*. Sun so tsunduma rayuwar Ramadhan a harkar shaye-shaye tun yana secondary school ALLAH ya tsallakar dashi. Dan kuwa bai jima da farawaba ALLAH ya fargar da Uwargida kuma amarya ga Alhaji Hameed Taura, *Hajiya Firdausi Amin Taura* kenan. Mace ce jajirtacciya kuma tsayayya akan ahalinta. Sam bata da wasa koda akan fuskane. Mace ce mai addini matuƙa da son taimako. A hannunta Ramadhan ya girma tun daga yaye, duk da kuwa suna gida ɗaya mahaifiyarsa sam bataso hakan ba, musamman da taga bayanshi bata sake haihuwar wani ɗa namijinba a cikin ƴaƴa shidda mata data sake haihuwa da Basheer Hameed Taura. Bama itaba kaf sauran matan Alhaji Basheer Hameed Taura ɗin guda biyu duk basu da ƴaƴa maza sai mata. Sai dai babu yanda ta'iya, dan sam Anne ba sakarar uwar miji bace da matar ɗa zata taka koda da kirsane. Babu ruwanta da rayuwarsu bare harkarsu, dan bata taɓa sakama matan ɗan nata idoba balle damuwa da mi suke ciki. Dan da ace ita ɗin sakaraice da tasha matuƙar wahala a hannun Gimbiya Su'adah.  
    Gimbiya Su'adah mace ce mai izza da tsananin taƙama kasancewarta ɗiyace ga sarkin jihar Bina. Sannan ƴar gata kuma sangartacciya mai ji da mulkin gidansu. Mace ce mai shegen girman kai da ƙyamar talaka, dan sam bata biyo ƙyawawan halayar mahaifinta ba. A ƙasar amuruka suka haɗu da Alhaji Basheer Hameed Taura yayin karatu, inda soyayya mai ƙarfi ta ƙullu harta kaisu ga aure kasancewar su ƴaƴan ƙwarya tabi ƙwarya.    
    Bayan ceto rayuwar Ramadhan da Anne tayi daga faɗawa shaye-shaye suka sake harar rayuwarsa akan neman mata. Sai dai anan ALLAH ya karesa, dan baima saka matan a gabansaba balle su damesa. Musamman daya kasance yanada ƙananun shekarune dama a wancan lokacin. Abokan banza suka ƙirƙirar masa da sukaso fara jansa yawon dare, tunda ya farga da halayensu ya janye jikinsa. Dan Ramadhan mutumne daya gado halayen iyayen nasa ta ɓangarori biyu. Akwai halin mulki na ɓangaren mahaifiyarsa tattare dashi. Akwai kuma halin dattako na ɓangaren kakansa dake yawo a jikinsa. Hakanne ya sakashi zama mai murɗaɗɗen hali tun daga yarinta har girma. Bazamu ce dashi miskili ba. sai dai zamu kirasa mutum mai tsananin girman kai da ɗagawa. Ba komai yake so ba, ba komai ake saka yaso ba, sai idan shine yaso a karan kansa. Da yawan lokuta Anne ce kawai ke iya tanƙwarashi ta ƙarfin tsiya saboda itama tanada zafi sosai.
   Su *Alhaji Wali Bajau* basu daina bibiyar rayuwar iyalan Alhaji Hameed Taura ba musamman Ramadhan da suke kallo matsayin zuciyar gidan har yakai girma. Da tsiya-tsiya da makirci Alhaji Haladu Gwandu ya ƙulla soyayyar ɗiyarsa da Ramadhan har takaisu ga aure a shekarar daya kammala karatunsa akan lauya. *Amnah* yariyace ƙyaƙyƙyawa kuma ƴar gayu kamar yanda Ramadhan ke buƙata. A shekaru kaɗan ya ɗarata hakan ma dai-dai da ra'ayinsa ne, dan sam baison auren yarinya ƙarama yace sun cika shirme da ƙuruciya wa miji. Soyayya ce ta haɗa Amnah da Ramadhan a zahiri, a baɗini kuwa su Alhaji Gwandu sun shirya hakanne da manufa, dan ta bayan fage suka dinga amfani da Amnah suna cutar da Ramadhan. Burin Ramadhan aikinsa na lauya, tare da faɗaɗa karatunsa na Addini dan tun yana shekara sha bakwai ya sauke alkur'ani mai girma ya fara hadda, saboda Anne bata da wasa, ga shi ALLAH ya bashi ƙwalwar karatun shima. Sai dai burin mahaifiyar Ramadhan gimbiya Su'adah ba haka bane. Burinta duk dukiyar Taura Family ta dawo hannun Ramadhan ne, dan haka taita ƙoƙarin jan hankalin mijinta harya amince da jawo Ramadhan ɗin cikin babban kamfanin (company) na taura aka ɗaurasa matsayin oga kwata-kwata. badan ya so ba ya amsa, dan shi hakan baya cikin burinsa. Amma nasihar tsoho Hameed Taura ya sakashi amincewa akan tilas ya fara musu aiki. Lokaci-lokaci kuma yana taɓa aikinsa na lauyanci a ɓoyo dan gudun ɓacin ran mahaifiyarsa mai zafin zuciya da son nuna gadara ga kowa.
    Suna shekar ta uku da aure Amnah ta haihu ƴarta mace, sai dai kuma an haifeta sikila ne tamkar uwar tata data kasance sikilar ce dama. Ko kusa hakan baisa ubanta ƙin son kayarsa ba duk da sam gimbiya Su'adah basan auren takeba. Amma kasancewar itama uban Amnah ɗin ba koma baya bane akan juya kuɗi ya sata ɓoye ƙiyayyar auren a ƙasan zuciyarta, sai idan abin nata ya motsane taita azabar masifa.
 Hawan Ramadhan MD a Taura company matsaloli sukaita faruwa na ɓatan kuɗaɗe da wasu asarori da aka rasa musabbabinsu. Tun su Alhaji Hameed na kawaici hartakai shida mahaifin Ramadhan Alhaji Basheer Taura sun zaunar dashi sun masa ƙorafi da tambayar mike faruwane haka company keta baya maimakon gaban da suke fita da nasarori?.
 Amsa ɗaya ce shima baida masaniya. Amma yana kan bincike da ƙoƙarin daƙile komai. Tun ana tattaunawa iya su uku harta kai Anne ta shigo tafiyar, hakama sauran matan gidan sun sani. Kowa yana ɗaura zarginsa akan Ramadhan da tunanin ko yana wata harkar banza ne ta kuɗi a ɓoye?.
A ranar da su Alhaji Balarabe Gizo suka shirya kai rayuwar Ramadhan ƙasa yayi dai-dai da ranar birthday ɗin ƴarsa Haseenah ƴar shekara biyu cif a duniya. An shirya liyafa ta gani ta faɗa tare da gayyata ta mutanen arziƙi Alhaji Haladu Gwandu ya baiwa Amnah ruwan addu'a da aka gauraya da guba akan ya amso ma Ramadhan ɗinne saboda ciwonsa na diabetis, Ramadhan nada diabetis  sakamakon ya zame musu tamkar gado ne. Alhaji Hameed Taura nada shi, hakama Alhaji Basheer Taura, shima Ramadhan ɗin haka da wasu daga cikin yara matan gidan. Sam Amnah batai tunanin mahaifinta zai iya cutar da Ramadhan ɗinta ba. Dan haka ta ɗauka ruwan addu'a da ƙyaƙyƙyawar zuciya takai masa. Sai dai an samu akasi bayan gama birthday party lafiya an watse ta buɗe fridge a gajiya ta ɗauka goran da ruwan addu'ar yake da tunanin ruwa ne saboda fitilar kitchen dake a kashe saita falo data ɗan hasko kaɗan ta sha. Tana sha Haseenah najan hannunta da mata gwarancin ruwa ruwa. Sai da tasha sosai sannan ta bata tasha itama.
  Wannan magani da Amnah tasha da ƴarsu Haseenah ya zama sanadin barinsu duniya. Dan kuwa azababben ciwon ciki ne ya baibayesu ita da ɗiyar har sai da aka kaisu asibiti, inda tunkan suje ma Haseenah ta rasu saboda ƙarfin gubar, Amnah kuwa sai kusan asuba itama tace ga garinku nan. Likita ya tabbatar musu hanjinsu ya kakkatsene ita da ɗiyarta saboda ƙarfin gubar da suka sha.
   Kwatanta irin tashin hankalin da Ramadhan ya shiga a wannan lokaci ɓata bakine. Bama shiba kowama da ke da alaƙa dasu wannan al'amari ya taɓa masa zuciya. Dan kowa dai ya fahimci guba aka ajiye musu. Sai dai ba'asan kowa ya ajiyeba saboda Amnah ita babanta yaba hannu da hannu batare da kowa ya sani ba. Ya kuma jaddada mata maganin diabetis ne kar Ramadhan yasha sai randa yake aiki musamman motsa jikinsa. Ita kuma ALLAH baisa ta bashi maganin ya sha da rana ba ta bari sai an tashi a birthday ɗin Haseenah. Ashe da rabon ajalinsune a ciki.
 Sosai Ramadhan ya fita a hayyacinsa. Dan yana mayuƙar son matarsa da ƴarsa duk da lalurar dake tare da su ta sikila. Iya bincike anyi a gidan babu wani bakin zare da aka samu sai tunanin cikin masu zuwa birthday ne suka ajiye gubar kawai. Tsabar yanda Ramadhan ya tada hankalinsa akan son gano wanda ya aikata ya saka su Alhaji Haladu Gwandu da abin yay matuƙar taɓawa da tunzurawa sakawa aka kai Ramadhan ƙasar Ukraine wai ganin likita. Sune suka tsarama likita ƙaryar da yace kar a sake yarda Ramadhan yay zaman NAYA sai bayan wasu shekaru harya manta da abinda ya faru. Sunyi hakanne domin su nisantashi daga bincike ko bibiyar ainahin gaskiyar lamarin da suka san reshe ya juye da mujiyane. Dan haukane kawai Alhaji Haladu Gwandu baiyiba a dalilin rasuwar shalelensa data bar duniya a dalilinsu.
Ƙura ta lafa, abubuwa sun canja, shekaru sunyi gudu har kusan biyar da faruwar komai. Ramadhan yayi jiyyar zuciya data gangar jiki harya warke, amma anyi-anyi ya dawo NAYA yaƙi. An kaɗa dambu da takiya yace shi da NAYA har abada. Babu irin roƙo da lallaɓa da basu masaba musamman gimbiya Su'adah da take kasa ɓoye ɗunbin soyayyar da take masa koda a idanu ne amma ya kafe akan bakansa. Da ga ƙarshe ma sai ya koma U.S da zama. Kafiyarsa da murɗin hali yasaka kakansa Alhaji Hameed Taura yin fushi yace su barsa ya dawwama acan dan ALLAH karya dawo. Ya kuma saka sharaɗin koda wasa kar wanda ya sake zuwa dubashi har Mahaifinsa da gimbiya Su'adahn. Inko ba hakaba zai saɓama mutum a gidan.
Wannan shine dalilin da yasa Alhaji Hameed Taura baya son ko maganar Ramadhan ai masa a gidan, duk da yana tsananin kewarsa a kusa da shi da begensa shima. Dan shi kaɗai ke zuwa dubashi a ɓoye batare da shi kansa Ramadhan ɗin ya sani ba.
 Yayinda Ramadhan kuma har yanzu zuciyarsa ke cike da burin binciko koma wanene da alhakin kashe masa iyalinsa, dan haka a tsahon shekarun nan babu abinda yake saƙawa da kwancewa bayan kasuwancinsa daya maida hankali dayi shi kaɗai sai hanyar dazai yi binciken yanda rayuwar matarsa da ƴarsa ta salwanta. A cikin wannan halin kuma Anne ta kawo shawarar Ramadhan B. Hameed Taura ya maye gurbin kakansa a kujerar shugaban ƙasa da akai masa tayi. Inda dudu shekarun Ramadhan B. Taura 36 a duniya. Ya rasa iyalansa yanada shekaru 31. Yanada ashirin da bakwai yay aure. A yanzu shekaru 5 cif da faruwar komai kuma.
 A hasashe ba'a taɓa samun wani shugaban ƙasa mai adadin shekarunsa na ƙuruciya ba a ƙasar ta *NAYA* ba sam.


“Kana nufin dole kenan mu amince da zancen Alhaji Hameed Taura indai muna buƙatar cikar burinmu Your Excellency?”.
Monday Mazier ya faɗa a ɗan hasale.
Shugaban ƙasa da Alhaji yaro glass suka kalli juna suna murmushi mai kama da takaici suma. Yayinda Alhaji Haladu Gwandu ya dafa kafaɗar Monday Mazier ɗin yana faɗin. “Mr MM cool down abeg. Muma duk irin zafin da kakeji munjisa a lokacin daya tabbatar mana ya amsa tayinmu, amma kuma jikansa ne zaiyi bashi ba. Ƙwarai da gaske ya shammacemu, shammata maiban mamaki. Dan yayi hakane dan mu janye buƙatarmu kodan kasancewar jikan nasa yaro, tunda yana ganin ba’a taɓa shugaban ƙasa mai ƙarancin shekarunsa ba a wannan ƙasa ta NAYA. Sai dai kodana zauna nai zari sai banji komai ba, domin Ramadhan baida maraba da hoton bango da kowa zaizo ya kalla ya wuce manne a falo batare daya amfana masa komaiba. Shine surikina da yarinyata ta rasa ranta a dalilinsa, yana can U.S tsahon shekaru biyar tamkar zararre. A ganina wannan damace a garemu mai sauƙi, duk da naji a raina Taura yayi hakane danya dawo da hankalin yaron gida kamar yanda sukaita fata a shekarun baya yaƙi hakan. Amma idan Taura yasan wata ai baisan wataba, Idan muka fitar da yaron matsayin ɗan takara zamu kawo wani sabon abu a ƙasar nan da ba’a taɓa yiba, sannan matasa zasu yarda da gaske muna tare da su. Babu tantama mulki zai cigaba da kasancewa a hannunmu ne”.
“Woow exactly my man”.
Mr MM ya faɗa yana bama Alhaji Haladu Gwandu hannu suka tafa bakinsa washe da dariya tamkar yanda shugaban ƙasa da Alhaji Yaro glass da Alhaji Balarabe Andu keyi suma alamar hankalinsu yaɗan fara dawowa jikinsu.
Alhaji Yaro glass ya gyara zama da faɗin, “Tabbas nima sai yanzu na fahimci manufar Taura na yarda cikin sauƙi, kuma hakan yamin daɗi, dan mu idan bai saniba wata damace ta ɗaukar fansa sau biyu akan abu guda. Ramadhan zai hau mulki na tsahon shekaru biyu kacal, sannan zai mutu sau biyu……”
“Sau biyu kuma?”.
Shugaban ƙasa ya katse Alhaji Yaro glass cikin rashin fahimta.
Alhaji Yaro dake murmushi yace “Ƙwarai kuwa sau biyu, dan dole ne mu ɗauka fansar Amnah data mutu dominsa, sannan mu kashesa adalilin taurin ran kakansa da ubansa. Na farko zai kasance cikin nasararsa da jin daɗin mulki a shekarar farko, a shekara ta biyu zai fara ciwo a dalilin guba da zata zagaya jininsa zuwa ɓargo da jiki. A shekara ta uku muyi bikin mutuwarsa da biznesa vice president ya hau kujera ya shekara biyu biyar cif kenan. Shekar ta ƙarshe a sake sabon zaɓe wannan shine amsar mutuwa biyu”.
Ya ƙare maganar yana ƙyalƙyalewa da dariya, suma sauran suna tayasa kamar wasu zararru. Sai da sukai mai isarsu kafin suyi shiru suka koma shan shayi da cigaba da ƙulla tsiyatakunsu……..✍

????????Hummm wani lokacin ma rasa abun magana ake.

ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA????????????????????

1~ KUFAN WUTA????
Safiyya Huguma

1~ BAQAR INUWA????
Billyn Abdul

1~ RAYUWAR MACE????
Hafsat Rano

1~ MASARAUTA????
Miss Xoxo

1~ NOOR ALBI❤‍????
Mamuhgee

Guda 1????300
Guda 2????400
Guda 3????500
Guda 4????700
Guda 5????1k

ZAKU BIYA KUDINKU ANAN????????

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya????????

09032345899

KATIN MTN????????

09166221261


JAMA’AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan????????

Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F

ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA????????

+227 95 16 61 77

TEAM ZAFAFABIYAR????????????????


BAƘAR INUWA…????????

https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09

Da ɗumi-ɗuminsa????????????????????????????????

Please
Follow me
Share
Comments akan abinda ya shige maka duhu.

     _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar????????????????????????_

YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za’a cike Form ɗin kamar haka: –

Enter your name: (Cikakken sunanki)

Enter your mail: (Email ɗinki)

Enter an username (Sunanki)

Enter your password: ( misali 12341234)

Confirm password: (misali 12341234)

Sai a taɓa Sign Up shikenan an buɗe account a ArewaBooks????????????.

Continue with Google – Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za’a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

Register – Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.

AREWABOOKS LINK kai tsaye

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3

Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com

Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App… Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine.

MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER

+234 903 177 4742

Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan????????????????????????.
Typing????

Episode 10

………….WASHE GARI shugaban ƙasa yay waya da god father nasu na siyasa dake faɗa aji a ƙasar baki ɗaya, sai dai a siyasance babu mai iya jin sunayensu. Ya sanar musu dukanin tsare-tsarensu. Sosai nasu tsarin yay masa shima harya yaba musu, dan yasan komai sai dai suna bayan fagene, ya kuma tabbatar musu komai zai tafi dai-dai dan Alhaji Hameed Taura a tafin hannunsu yake.
Cikin farin cikin yabon da shugaban ƙasa ya samu yace, “Na gode ranka ya daɗe. ALLAH ya ƙara girma da ɗaukaka. Badan ku ba babu mai ganin koda hotonmu a ƙasar nan. Shiyyasa muke addu’ar tsahon rai a gareku domin muyita cin karenmu babu babbaka”. (Ashe kasan shi mai mutuwane, rayuwarsa mai ƙarewace excellency. Inhar kuwa zai mutu to bai isa amfana maka komaiba face wanda yazo cikin ƙaddarar duk wanda kuka hara. ALLAH ka bamu shugabanni na gari????????????????).
Bayan ya gama masa kirari da yabon dake sake buɗa masa kai ya ɗora da bayanin…
“Ranka ya daɗe a yanzu haka mun gama yanke shawarar ganawa da shi yaron kawai muji ta bakinsa shima”.
“Tunani mai ƙyau, sai naji ku”. Daga haka ya yanke wayar. Shugaban ƙasa ya cireta a kunnensa yana jan kakkauran tsaki da ballama wayar harara. Cikin ƙunƙuni yace, “Mugu ƴan hana ruwa gudu, ALLAH dai ya kusa kasheku muma mu babake ko’ina, daga sama har ƙasan ta zama tamu. Dan badan kuba da mune taurarin duniya ta kowanne fanni.”

(Kai jama’a kamar bashi bane ya gama masa ƴar murya yanzun????, siyasa shegiya????).

TAURA HOUSE

    Kamar yanda al'adun ƙasashen da  hausawa yake dama musulinci baki ɗaya, irin wannan lokacin ko nace wannan ranar ranakune masu muhimmanci na shirye-shiryen bikin salla. Tamkar kowanne gida dake shiri haka Taura family house ma keyi ƙwansu da kwarkwata. Danko duk ƴammatan gidan zaka gansu da zanen lalle baƙi ko ja. Wasu sunyi kitso wasu gyaran gashi kawai. Hakama matan Alhaji Basheer Hameed Taura babu koma baya dan duk ɗinsu ƴan gayu ne kuma ƴaƴan manya, dan kowacce tana alfahari da irin gidan data fito ne.
  Misalin ƙarfe tara na dare da yay dai-dai da sanarwar ganin jinjirin watan shawwal daga bakin mai girma sarkin musulmi ƙararrawar dake sanar da taron meeting na iya manyan gidan ta kaɗa. Ba sabon abu bane hakan a duk daren kowacce salla, sai dai a wannan karon taron meeting ɗin yazo da banbanci. Sakamakon manyan gidan kawai ake buƙata banda yara.
 Cikin tunani da taraddadin lafiya duka matan Alhaji Basheer Hameed Taura suka kimtsa kawunansu zuwa sashen surukan nasu domin amsa kira. Sai tsoffi guda biyu da suka kasance ƙanne ga Alhaji Hameed Taura da suma suke zaune a gidan a halin yanzun. Sai ƙanin Alhaji Hameed Taura ɗin autansu da ya iso da iyalansa daga ƙasar Dubai a daren jiya domin halartar bikin salla da sukanzo a kowacce shekara...

      Duk wani wanda ake buƙatar gani a katafaren falon na alfarma da an tsarasane kawai domin gudar da meeting na ahalin gidan ya iso. Kowa ka gani zaune yake cikin mutuntawa ga dattijo Alhaji Hameed Taura da matarsa Anne. Dan dukan matan Alhaji Basheer kansu a ƙasa yake kasancewar suna gaban surukai.
Bayan an buɗe taro da addu'a Alhaji Hameed Taura da ahalin gidan ke kira da suna Bappi yay gyaran murya da tasaka kowa sake nutsuwa a wajen.
  “Da farko dai ina tayamu murnar ganin wannan wata na shawwal da rai da lafiya. Ina roƙon UBANGIJI ya amshi ibadunmu da mukayi, ya yafe mana kura-kuranmu. Yasa muna da rabon ganin na gaba da rai da lafiya.”
 A tare suka amsa da (amina).
Ya cigaba da faɗin, “Nasan zakuyi mamakin canzawar zaman meeting ɗin yau, dalilin hakan kuwa ya dangantane ga Ramadhan kacokal”.
 Da dauri Gimbiya Su'adah da yaran ke kira da (Maa) ta ɗago jin an ambaci sunan gudan jininta mafi soyuwa. Yayinda firgici da taraddadi ya bayyana cikin ƙyawawan idanunta. Dan batason mi kuma ya samu Ramadhan ɗin ba koya aikata. Tunda yau kusan satinsu biyu rabon da suyi waya sakamakon ta masa maganar ya daure yazo musu salla gida......
    .... ya katse mata tunani da cigaba da faɗin, “Wani babban al'amarine ya tasoma gidan nan, sai dai mun ɗaukesa kacokan mun rataya ga shi Ramadhan saboda wasu dalilai. Na farko yin hakan zaisa ya dawo kusa damu dole. Na biyu zaisa yazo shima yay aure. Na uku ya isar da abubuwan da muka kasa isarwa ga sauran mutane bisa ga abinda ALLAH ya azurtamu da shi.”
 Duk da a dunƙule yay dukan bayanin hakan bai hana farin ciki bayyana a fuskar Maa ba. Ji take tamkar Bappi ya mata albishir ne da wani yanki na farin cikin samun ƙyaƙyƙyawar makoma. Tana matuƙar burin ganin yaronta a kusa da ita. Tsabar jin daɗin hakan harta gama yanke masa matar aure a ranta. Dan wannan karon tanason zaɓama yaron nata matar aure ko hakan zaisa ta sanadin matar ya dawo gareta ba wajen Anne ba....”
   Dogon tunanin da gimbiya Su'adah ta tafi yasa har Bappi ya kammala jawabinsa ma bata ƙarasaji wasu abubuwan ba. Sai murmushi take wanda ya kasa ɓoyuwa bisa fuskarta.

  Ana tashi da ga taron tun kan ta ƙarasa sashenta ta fara kiran wayar gimbiya Asma'u yayarta da suke uwa ɗaya uba ɗaya (Adda Asmah). Su baƙwai mahaifiyarsu gimbiya Naja'atu da ake kira fulani ta haifa, sai dai sauran duk mazane su biyune kacal mata, kuma sune manya. Hakan yasa musu wata shaƙuwa da son juna na musamman dan sun tashine tamkar tagwaye. Kasancewar kuma irin gidansu gidane na tsantsar ƙabilanci da ƴan ubanci yasa kowa da nasa yake shaƙuwa.
   Dai-dai tana saka ƙafarta a ƙawataccen falonta na alfarma da yaji kayan more rayuwa har zaman musaltashi zai iya zama ƙauyanci gimbiya Asma'u ta ɗaga wayan. Itama tayi aure tuni, anan cikin garin Bingo ma take, rana ɗaya ma akai musu aure. Sai dai ita tayi kusan shekara biyar bayan aurensu kafin ta samu haihuwa. Yaranta biyu kuma kawai. Mace da namiji.
  Batare data dubi su Zuhrah dake zaune a falon kowa na harkar gabansaba ta shige tana mai zolayar yayar tata da faɗin, “Haba ƙasa badai har kin fara barcin naki ba ko?”.
  Amsar da aka bata daga can ta sata sakin ƴar dariya tana tura ƙofar glass na corridor ɗin bedrooms ɗinta ta shiga. Ta kan wani tattausan carpet dake a tsakkiyar corridor ɗin ta taka zuwa ƙofar tsakkiya. Ɗaki ne da musaltashi ɓata lokacine. Dan haka kowa ya musalta da kansa. Ƴar sarki matar Alhaji Basheer Hameed Taura. Ta kai zaune tana sake ƙawata murmushin fuskarta da faɗin, “Amin Adda Asmah. Dama albishir na kiraki nai miki”.
  Tai dariya saboda zumuɗin Adda Asma daga can. “Oh god hajiyar ruɗu kwantar min da hankalinki. Bafa wani abu bane yaronkine kawai zai dawo NAYA, dalilin kiran naki kuwa maganar aure da mulki da ya sakko a ciki ne. Inaga lokaci yayi da zamu cika burinmu na haɗa auren Ramadhan da Aina'u tunda ta kammala karatunta”.
 Dariya ta kuma saki wadda inba Asma ɗin ba babu mai iya ganinta a saman fuskar Gimbiya Su'adah saboda izzarta da girman kai. A take a wajen suka gama yanke hukunci komai game da auren ƴaƴan nasu, batare da gimbiya Su'adah tayi wani dogon tunani ko bincike akan mike a ran Bappi ba.

★★HAJIYAR BIRNI HOUSE★★

        Tun shigowarta ɗakin kwance kawai take tana faman murmushin samun mafitar damuwar data shigo da ita cikin gidan. Dan tabbas da damuwa ta shigo kamar yanda hasashen ƴan uwan nata yake, damuwar da keda nasaba da zuwanta wajen first lady.
  Ita ɗin mace ce ƙyaƙyƙyawa kuma gogaggiya, inda a dalilin harkar barikinta ta haɗu da Alhaji Yaro glass babban ɗan siyasa dake riƙe da babban muƙami a ƙasar ta NAYA. Tun a haɗuwarsu ta farko taji sonsa a ranta, inda akai dace shima ya kamu. Dan haka sukai aure cikin ƙanƙanin lokaci. Sai dai abinda bata saniba Alhaji Yaro glass a ƙarƙashin mulkin mace yake a cikin gidansa. Dukkan faɗa ajinsa iyakarta waje ne. Daya taka gate ɗin gidansa sunansa mijin hajiya Fanta. Tabbas ta fuskanci ƙalubale kala-kala a zamanta da Hajiya Fanta da bazasu musaltu ba, har takai sai da ta tsigeta a gidan hankalinta ya kwanta. Ta kuma kauda hankalin Alhaji Yaro glass da ga gareta baki ɗaya, duk da ƙulafucin son komawa garesa da takeyi musamman saboda ƴarsa ɗaya tilo da suka haifa tare dake wajenta. Tun farkon zuwanta gidan suke ƙawance da Hajiya Bushira hamada, wadda sam bata shiri da Hajiya Fanta duk da kuwa mazajensu abokaine shaƙiƙai. Koda yake ance ada ƙawayene suma na amana, sai dai ƙawancen ya watse ne a dalilin ƴaƴansu. Mafari kenan Hajiya Bushira taita tunzura Alhaji Yaro glass ya ƙara aure, tun baya biye mata har yaji sha'awar yin hakan lokacin daya haɗu da Aunty Hannah. 
 Bayan fitowarta a gidan hajiya Bushira tayi iya ƙoƙarinta na ganin Aunty Hannah ta koma gidan Alhaji Yaro glass amma hakan ya gagara, har suka samu nasarar ɗarewa kujerar mulkin ƙasar ta NAYA. Inda Prof... Usama D. Hamada ya samu nasarar zama shugaban ƙasa bisa ƙoƙarin su Alhaji Hameed Taura. Su kuma su Alhaji Yaro glass suka koma gefe matsayin manya sunacin karensu babu babbaka. Dan ko muƙami ɗaya basu amsaba a bayan fage suke nasu mulkin su.
 Hankalin aunty Hannah ya sake tashi dan tana son Alhaji Yaro glass sosai, amma sai Hajiya Bushira Hamada (First lady) ta kwantar mata da hankali akan karta damu, inhar tana raye sai ta koma aure gidan Yaro glass. Aunty Hannah tana cikin manyan ƙawayen first lady da suke mata ayyuka a ɓoye, amma tana ɓoye kantane saboda Alhaji Yaro glass.
    A yau ma first lady ce ta buƙaci ganin aunty Hannah ɗin tun daren jiya akan wani aikin sirrinsu, a hirarsu ne first lady keɗan tsoguntama aunty Hannah batun wanda su shugaban ƙasa suke son tsaidawa takara, tare da burinsu na salwantar da rayuwarsa daga baya Alhaji Yaro glass ya maye gurbinsa, dan shine sukeso ya zama mataimakinsa. Wannan al'amari ya matuƙar saka Aunty Hannah a farin ciki matuƙa. Har takejin zata iya bada gudunmawarta akan wannan al'amari. Sai dai maganar data biyo bayan hakan ce ta sakata a damuwa, dan kuwa first lady ta sanar mata sun tattauna da shugaban ƙasa akan suna son samawa yaron matar auren da zata dinga musu aiki a kansa batare da sanin kowa ba, amma suna tunanin ta yadda zasu ɓulloma Alhaji Hameed Taura game da hakan. Dan samawarwa Ramadhan matar aure daga ɓangarensu ne kawai mafita da hangen nasararsu a tafiyar. Hakan yasa tacema aunty Hannah taje ta tayata tunani da nazarin mafita dan tana son ita ta fara kawoma shugaban ƙasa mafita koda ƙara samun ɗaukakarta na mata garesa, sannan ita kuma ta zama first lady kodan cusama hajiya fanta baƙin ciki. Dan ba hawan Alhaji yaro glass bisa kujerar matamakin shugaban ƙasa ko zama shugaban ƙasa bane matsalarta ita. Hajiya Fanta ta samu muƙami dai-dai da wanda ta taka shine damuwarta kawai. shiyyasa take so ta shiga ta fita wajen ganin ta nakasa Hajiya Fanta kafin lokacin Aunty Hannah ta koma gidan ta zama tauraruwa a mulkin da Alhaji yaro glass zaiyi. 
     Wannan shine dalilin shigowarta da damuwa gidan. Sai dai kuma abinda ta tarar na boran Raudha ya kawo mata mafita cikin sauƙi da take tunanin first lady zatayi matuƙar farin ciki da ita har itama ta samu cikar burinta na komawa gidan Alhaji Yaro glass matsayin matar vice president.

 Ta saki murmushi mai ƙayatarwa tare da jawo hamshaƙiyar wayarta 1phone ta shiga sarrafata. Kai tsaye number first lady ta laluba. Harta tsinke ba'a ɗaga ba, dan haka ta yanke shawarar sake kira dan tasan saƙon da take shirin kaiwa mai matuƙar muhimmanci ne.
 Cikin sa'a kuwa tana gab da tsinkewa first lady ta ɗauka. “Hannah am sorry ina amsa wani call ne. Ina fatan har an samu mafitar ne da gaggawa haka?”.
   “Sosai ma kuwa your excellency. Zumuɗin hakanne ma yasa na kasa haƙurin bari sai nazo nace bara na kiraki”. Aunty Hannah ta faɗa cikin washe haƙora kamar tana gaban first lady. Itama daga can first lady ta amsa ne cike da zumuɗin son jin yaya akai? Dan haka kai tsaye aunty Hannah ta fara jero mata bayani....
    “Akwai yarinyar ƙanwata dake aure acan jihar Ɗillo. Sai dai a wani ƙaramar hukuma suke mai suna hutawa. Yarinyar ƙyaƙyƙyawa ce son kowa ƙin wanda bai samu ba. Gata ƙarama sosai sweet 17. Tanada yanayi irin na mutane masu haƙuri da komi zatai baza'a zargeta ba. Sannan inada yaƙinin zata shiga ran Alhaji Hameed Harith Taura cikin ƙanƙanin lokaci. Kai harma da uban gayyar kansa dan da gaske yarinyar ta haɗu your excellency......”
    “Ban katsekiba Hannah, amma mu minene alaƙar shirinmu da ƙyawunta ko sanyin halinta? Mufa wadda zatai mana aiki kawai muke buƙata batare da matsala ba”.
   “Hakane your excellency amma bara na kaiki. Alhaji Hameed Taura mutum ne mai son mu'amula da mutanen kirki, a dalilin hakane mazajenmu suka ɓoye masa ainahin fuskarsu suka aro ta mutuntaka suka yafa ma kansu har takai abotarsu yin tsaho zuwa yanzun. Dan haka bazai yuwu mu samo yarinya mai rawar kai ba akan wannan shirin. Dole ta kasance mai irin suffar Raudha, sannan ƙyaƙyƙyawa. Abu na biyu dole ta kasance ɗiyar masu ƙaramin ƙarfi da basu da wata power ɗin zamtowar yarinyar mai buɗaɗen kai da komai zata iya fahimta idan an sakata tayi, sannan kuma zamu iya juyata ita da iyayenta yanda muke buƙata muma cikin sauƙi dan batasan komai ba sai abinda muka ɗorata a kai”.
     First lady ta ƙyalƙyale da dariya da faɗin, “Kai Hannah shiyyasa nake bala'in sonki wlhy. Dan kuwa kanki na ja matuƙa. Sai dai matsalar ɗaya zuwa biyu ce. Matar shugaban ƙasa ƴar 17years, kuma mai kwalin secondary school kawai. kuma ɗiyar ƴar uwarki bayan kinsan shirinmu shine itama idan ta kammala mana aiki rayuwarta zata iya salwanta”.
      Aunty Hannah tai ɗan murmushi tana sake damƙe filo a jikinta. Dan ita inhar buƙatarta zata biya salwantar rayuwar Raudha ba komai bane ba a gareta. “Your excellency matsala ta farko ba matsala bace ba. Dubi da shima ɗin yaro ne matashi da zai zam na farko bisa kujerar mulkin ƙasar NAYA. Karatu kuwa ko tana gidansa za'a iya sakata ta fara badan zai amfanemu ba sai dan kawai zai bada kariya ga masu ƙorafin matar president iyakarta secondary. Na uku kuwa karki damu, dan mun rasa iyayenmu ma munyi haƙuri balle ƴaƴa. Ko Samha ce zan iya sadaukar da ita domin samun cikar burinmu (ƴarta fa????, anya kuwa gsky aunty Hannah ke faɗa????????). Abinda kawai zamu maida hankali yanzun shine koya mata rayuwar manyan mata da abubuwa.”
   “Okay na gamsu da bayaninki, sai dai kuma taya zamu haɗa alaƙar su kuma?”.
  “Wannan shine dalilin kiranki your excellency...........”✍

(Tofa, su Aunty Hannah kumafa????????????).

*Yaya kuke gani masu karatu? Shin Ramadhan zai amince ya amsa kiran Alhaji Hameed Taura kuwa zuwa ƙasar NAYA? Harma da tayin zama shugaban ƙasa?? Kokuwa ƴan ƙasar ta NAYA zasu yarda da wannan sabon al’amari na hawan matashi mai jini a jika irin *_Ramadhan B. Hameed Taura* ne matsayin shugaban ƙasarsu ne?. koba shekaru ba karku manta akwai matsalar sauran ƴan jam’iyya, akwai ta shekaru, akwai!! Akwai akwai da yawan gsk. Muje zuwa donjin shin yaya zata kaya ne?????????_*

ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA????????????????????

1~ KUFAN WUTA????
Safiyya Huguma

1~ BAQAR INUWA????
Billyn Abdul

1~ RAYUWAR MACE????
Hafsat Rano

1~ MASARAUTA????
Miss Xoxo

1~ NOOR ALBI❤‍????
Mamuhgee

Guda 1????300
Guda 2????400
Guda 3????500
Guda 4????700
Guda 5????1k

ZAKU BIYA KUDINKU ANAN????????

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya????????

09032345899

KATIN MTN????????

09166221261

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button