BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

TAURA HOUSE

  Tun fitarsa take ƙame a tsaye, sai da ta fahimci jinin jikinta sulalewa yake zuwa ƙasa sannan tai jarumtar jawo numfashin dake neman barin ƙirjinta yana bin jininta dake sauka a ƙafafunta. A ƙa'idar kowanne ranakun bikin salla na babba da ƙarama washe gari a masarautarsu take yinta ita da dukan iyalanta dama ahalin masarautar garin ta Bina. Shiyyasa a yanzu haka jirgin da zasu bi a shirye yake tsaf zuwa jihar BINA fitarsu kawai ake saurare.
  Waya ta jawo da sauri dan bazata iya jira har sai ta isa garin Bina ba zuciyarta zata iya fashewa. A yanda take ƙoƙarin dialing numbern na ƴar uwarta Asma zai baka tabbacin a ruɗe take. Ta saka wayar a hansfree dai-dai shigarta. Bugun shigar kiran na bugawane dai-dai da bugun zuciyarta. Sai dai abin takaici harta tsinke ba ɗagaba. Sake kira tai nan ma babu amsa. Sai da ta jera kusan kira biyar amma ba'a ɗaga ba. Lallai babu lafiya, dan a ƙa'idar gimbiya Su'adah daga kira ɗaya bata sake yima mutum ko yaya suke, mai-martaba ne kawai keda wannan alfarmar da arziƙin a gareta. Amma a yau sai gata da jera har biyar batare da taji ta gundira ba.
 Da sauri ta maida akalar kiran nata ga mai-martaba saboda zuciyarta ta ayyana mata shine kawai maganin kukanta a yanzu bama Asma ba. Cikin sa'a kuwa tana gab da tsinkewa a ka ɗaga, domin kuwa abune a bayyane kowa yasan gimbiya Su'adah ƴar gaban goshin mai-martaba ce saboda sunan wadda ta riƙesa da yakema kallon uwa aka saka mata.
Cikin girmamawa tamkar tana a gabansa ta rissina tana gaishesa. Daga can ya amsa da sakewa cike kuma da ƙasaita irin ta masu mulki. 
  “Mamana kun iso ne?”.

Cikin girgiza kai da sake raunan murya ta ce, “A’a Abi bama mu taho ba. Dama Ramadhan ne yazo NAYA jiya, bamma san da zuwan nasa ba sai a safiyar yau. Koda ya shigo gaisheni yayiminne tamkar maƙiyarsa ba mahaifiyarsa ba. Daga ƙarshe yake sanarmin a yau zai koma America. Nama tabbatar yanzu yana gab da barin ƙasar..” ta ƙarasa faɗa tana sakin wani kuka mai ban tausayi gamai saurarenta.
Mai-martaba ya saki ƙasaitaccen murmushi yana gyara kishingiɗarsa. “Ni ban san randa Mamana zata girmaba har yanzu. Yanzu dai akan Ramadhan kike ɓatamin hawayenki? To sharesu ki kwantarmin da ranki. Yanzu babu jimawa mukai waya da Alhaji Hameed akan zasu ƙaraso nan tare da shi, suna airport ma a yanzu haka”.
Wani irin wawuyar ajiyar zuciya ta saki da murmushi lokaci guda. Sai hawayenta data kai hannu ta share da faɗin, “Nagode Abbi”.
“Godema ALLAH”.
Ya bata amsa yana yanke wayar.
Tuni ta manta da hawayen fuskarta ta hau sakin murmushi. Koda Addah Asma ta kirata batabi takan kiran ba dan tasan yanzu zasuje su haɗu ai….

TK SPECIAL HOSPITAL

      Ita ɗin yarinyace mai kaifin basira da hangen nesa. Hakan yasa tun bayan barin su Ramadhan ɗakin ta shiga cikin zurfin tunani da fassarar kalamansa. Sai dai kafin ta samu damar samo amsar sallamar ƴan uwanta da su Asabe harma da kakarsu Hajiyar birni ya katseta. Taji daɗin ganinsu dan dama tunda ta farka take tambayar likita ina suke. Dan da farko ta tsorata da tsadajjen asibitin da taga kanta a ciki.
  Rungumeta Asabe tai tana kuka, dama shi ta kwanayi a daren jiya. Dan gani take Raudha ta rasu ne su aunty Hannah na ɓoye mata. Hakama Yasmin tana kallon ƙafar Raudha ɗin ta fashe da kuka, kukanta kuma yaja hankalin su Samha suma dake ƙananan yara suka fara.
   Sai da hajiya mama ta ɗan musu tsawa ne ganin aunty Hannah na lallashinsu sunƙi su nutsu. Yanzu kam tsit sukayi sai Asabe ce ke nata tana jerama Raudha addu'oin samun lafiya....

Kasancewar Alhaji Hameed Taura ba ƙaramin mutum bane cikin ƙanƙanin lokaci zancen sake ziyararsa asibiti tare da jikansa ta baje kafafen yaɗa labarai dana yanar gizo. Harma abin ya bama Bappin mamakin tunda yasan baici karo da ɗan jarida ko gudaba. Sai dai tunawa da cewar yanzu waya ta maida kowa ɗan jaridar kansa ya sashi watsar da kokwanton.
  Yabo dai kam yana samu akan ƙoƙarin tsayawa tsayin daka ga Raudha. Dan yanda kowa yasan wanene shi ba'ai tunanin zai bada lokacinsa gareta ba. 

JIHAR BINO PLACE

      Duk da Ramadhan nata ɓata fuska a cikin jirgi hakan bai hanashi jin daɗiba a ransa sanda suka iso cikin masarauta. Dan suna sauka a airport ƙayatattun motoci na alfarma guda huɗu wanda uku ke tare da hadimai, ɗaya ta ɗaukarsu suka iso filin jirgin.
    Alhaji Hameed Harith Taura kowa yasan abokine ga Sarki Abdul-wahab tun da ƙananun shekaru. Dan kuwa tarihi ya tabbatar da sunyi karatun degree na farko tare a jami'ar Bino. Sannan harkokin kasuwanci sun sake haɗasu a wasu fannoni kafin mai-martaba ya haye karagar milkin jihar ta Bino. Sai kuma gashi sun zama surukai a dalilin auren ƴaƴansu.
   Yau ranace da masarauta ke cike da baƙi tako ina. Amma hakan bai hana a samarma da su Ramadhan tarba ta musamman ba. Ramadhan na gama gaisawa da mai-martaba daketa tsokanarsa akan ya'akai kuma ya baro masu jajayen kunuwan?. Ko sun gaji sun koroshine da kansu. Shi dai murmushi kawai ya dingayi dan ba kasafai irin wannan wasar ke shiga tsakaninsa da kakannin nasa ba. Daga su Bappi har su mai-martaban sunyi trianing nashi ne like iyayensa ba kakanni ba. Garama Fulani takan ɗan tsokanesa. Sai dai kuma shi ɗin bawai ya iya wasan baneba iyakarsa murmushi ko ada can ma balle yanzun.
 Fahimtar magana su mai-martaba kesonyi ya sashi zame jikinsa zuwa cikin gida domin ya gaisa da kakar tasa da iyaye da ƴan uwa. Yako karancesu da ƙyau, dan yana fitar suka hau tattauna dalilin zuwan Alhaji Hameed ɗin dan awa ɗaya kacal suke da ita saboda mai-martaba na amsar baƙuncin manyan mutane masu barka da shan ruwa da barka da salla.
 Abubuwa masu muhimmanci guda biyu suka tattauna. Wanda ya shafi auren Ramadhan da Bappi atake ya sanar ma mai-martaba har yayi masa mata. Da kuma batun fitowa takara da zata bayyana nan da ƙanƙanin lokaci. 

Duk gaba ɗaya mai-martaba yayi farin ciki ya kuma sanya albarka da fatan alkairi a cikin lamarin, tare da bada goyon baya dan a ganinsa ai babban cigabane jikan nasu ya samu. Daga haka ya ƙara da nasa shawarwarin shima………..✍

Barkanmu da dawowa.????????????????


mg’s skincare

Shin Ina matan suke????️????️????️maza kuhanzarta kumatso kusa kuma kubani aran kunnuwanku domin sanin albishir dawannan shahararran company yazo muku dashi????????
Hakika tabbas duk macen data amsa sunanta bazataso afita b Koda da kwayar zarra domin hakane wannan shahararren company yazomuku da ingantattun hadaddun kayan gyaran jiki masu matukar gyara fata cikin kankanin lokaci batare da sunyima fata lahani ba domin kayan mg’s organic products ne bawai na bleaching ba zasu gyara ma mutum fatane yafiddomashi da ainihin natural beauty din mutum????hakika duk wacce batayi anfani da kayan mg’s b anbarta acan karshen bayama kuwa domin Koda sabulunsu kadai kuka dana fatanku seya fita dasauran mata ballentana Kuma kuyi anfani da gbdy beauty kit dinsu wohoho wani abun baa mgn sewanda yajaraba shine zai tabbatar❣️
Shin kinafama da
Pimples, black spot,sunburn, stretch mark,acne,black head, wrinkles,knuckles dama duk wani matsalan fata?
Shin fatanki tana tattarewane ko kinshafa cream yabatamiki jiki????
Shin inamasu cewa sunjaraba Basu dace b bi’iznillah sister’s duk Wanda yayi using mg’s sai godiya domin Koda iya herbal whitening black soap din kikayi anfani dashi zakiga ynd fatanki zaiyi clear Yana walwali jikinki zeyi fresh kina glowing my dear bare Kuma ace set dinne gbdy ????ga amare uk wnd yy using bridal set dinnan baya bukatar kowani gyaranjiki domin yadda jikinki zekoma yazarce misali DNT be left behind
Bridal kit:18k
Beauty kit:11k
Student package:7k
Herbal whitening soap:3k
Chat
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Facebook: mg’s skincare
Instagram:glow_with_mgs
Take note pls iya wadannan numbers dinne kawai zakusamu kyn mg’s babushi akasuwa????
Do you guys wanna achieve that milky skin that turns head wherever you go????
Then @mgs skincare gat you covered ????
Now is time to glow????
Pamper ur skin????
Shine like bride????????‍♀
Glow????‍♀️

???? tested nd trusted????
Guarantee

Sannan muna da hadaddun frames masu kyau gamai bukata yayi mgn 07046881166


https://arewabooks.com/chapter?id=629a77b967809ad6daab2109

Chapter 13

BAƘAR INUWA…????????

Da ɗumi-ɗuminsa????????????????????????????????

Please
Follow me
Share
Comments akan abinda ya shige maka duhu.

     _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar????????????????????????_

YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za’a cike Form ɗin kamar haka: –

Enter your name: (Cikakken sunanki)

Enter your mail: (Email ɗinki)

Enter an username (Sunanki)

Enter your password: ( misali 12341234)

Confirm password: (misali 12341234)

Sai a taɓa Sign Up shikenan an buɗe account a ArewaBooks????????????.

Continue with Google – Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za’a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

Register – Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.

AREWABOOKS LINK kai tsaye

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3

Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com

Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App… Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine.

MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER

+234 903 177 4742

Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan????????????????????????.

ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????
Typing????

Episode 15

……….Su Bappi basufi mintuna talatin da isowaba Gimbiya Su’adah da tawagar ƴaƴanta mata suka iso suma. Anan ne ta samu damar haɗa hannu da fulani (mahaifiyarsu Uwargidan sarki) da Adda Asmah suka rufe Ramadhan da faɗa sosai akan abubuwa da dama, ciki harda batun zamansa babu aure, duk da dai basu fiddo maganar zaɓa masa mata ba.
Shiko dai ya cinkushe fuska yana saurarensu kawai. Sai da sukayi mai isarsu ya basu haƙuri kawai yay fitowarsa. Dan Bappi ya kirasa akan ya fito su wuce. Idan kuma ya barsa anan to?. Da sauri yacema Bappi a’a zai bisa, dan so yake yaje ya wuce loss, sai dai bai faɗama bappi ƙudirin nashiba kai tsaye.

Yanzu kam ya iske mai-martaba tare da Bappi da Pa da suka iso da Gimbiya Su’adah. baiyi mamakin ganin Pa ɗin ba, tunda tun yana ƙarami yasan a irin wannan ranar ta washe garin salla suke zuwa gaishe da mai-martaba ɗin daman. Zama yay gefen mai-martaba daya nuna masa yana satar kallon Pa da fuskarsa ke a haɗe alamar har yanzu yana kan fushinsa na jiya. Koda yake har suka baro Bingo dama baiko kallesa ba duk da har falonsa yaje ya gaishesa.
Sai da suka tabbatar da nutsuwarsa sannan Bappi ya fara magana cikin nuna alamar babu wasa tattare da shi.
Ramadhan ya ɗago a firgice yana duban mai-martaba. Kafin ya maida dubansa ga Pa da baice uffan ba.
“Bappi!”.
Ramadhan ɗin ya faɗa cikin rawar harshe.
Bappi dake kallonsa cike da tausayawa a can ƙasan ransa. A fili kam ya dake ya jinjina masa kai. “Umarnine wannan ba shawara ba Ramadhan. Domin nasan zaka iya insha ALLAH. Zaka kuma kawo cigaban da muke fata wa ƙasar nan ta hanyar basira da ƙuruciyar da ALLAH yabaka. Domin NAYA irinka take buƙata, tabbas irinka take buƙata.”
Miƙewa Ramadhan yayi yana girgizama su Bappi kansa. Ya kai hannu ya tura hular kansa baya saboda zufa dake ɓillowa a kowacce ƙofa ta gashinsa. Babu abinda zuciyarsa ke ambata sai sunayen ALLAH. Ya sake buɗe baki zaiyi magana Pa ya dakatar da shi….
“Biyayya ga iyayena dole ne a gareka, domin bazasu taɓa jefaka a hanyar halaka ba. Tunda har su Bappi suka amshi tayinsu, dolene kaima ka amsa da ga garesu kayi biyayya. Idan ba hakaba babu ni babu kai da ga yau da ga wannan likaci….”
“Pa Please yayi girma da yawa….”
“Baiyi ba Ramadhan. Domin kaima kayi abinda kakeso a shekaru biyar muka kuma ƙyaleka, duk badan kafi ƙarfinmu ba. Dolene yanzu kaima kabi abinda mukeso dan lokacinmu ne.”
“Ya ALLAH”.
Ya faɗa cikin sake shiga tashin hankali yana komawa baya ya sake zubewa a cikin kujerar da ya tashi. Gaba ɗaya ƙwayoyin idanunsa sun sake canja kala a lokaci ƙanƙanin. Ɗan sassaucin daya samu na damuwar jiya wadda ta fita ta sake maye gurbinta. Gaba ɗaya gashin jikinsa ya mimmiƙe sai faman tura yatsun hannunsa yake cikin sumarsa dan son control ɗin abinda ke taso masa…
Duk da Bappi ya san Ramadhan ɗin yakai maƙura gab yake da birkice musu bai sassauta masa ba. Dan a ganinsa gara ayita baki ɗaya ta ƙare kawai. Hakan yasa kai tsaye ya ɗora da faɗin, “Sai kuma batun aure, shima mun riga mun maka mata dan ko munce ka nemo ba kawowa zakai ba. Bakuma zai yuwu ka hau mulki babu mace ba, idan har ALLAH ya ƙaddara zaka hau ɗin. Dan haka mun gama yanke hukunci mu zamu nema maka aur…..”
Kafin ma Bappi ya ƙarasa numfashin Ramadhan ya fara fisga. Ya shiga laluben hanun bappin dake kusa da shi, da ƙyar ya samu ya riƙosa ya damke. Cikin sauri Bappi ya miƙe ya ya rungumesa a jikinsa da kiran sunansa yana girgizashi.
Su dukansu ɗunbin tausayinsa ne a cikin ransu. Wannan yanayi da yake shiga idan ransa ya ɓaci yana tada musu hankali, babu irin likitan da basu gani ba, amma iya bincike akan sanar musu lafiyar ƙwaƙwalwarsa kalau. Sai dai maimakon su maida hankali gana musulinci sai suke sakaci, dan tabbas al’amarin nasa yana kamanceceniya da nai mai iska ko sihiri, ga diabetis kuma da shima ya zame musu na gado. Dan shi kuma Bappin ne ke dashi, shima Alhaji Basheer ɗin nada, hakama Ramadhan ɗin da wasu a cikin yaran gidan ƴammata.
“Ramadhan relax, calm down Please”.
Bappi ya faɗa yana shafa kafaɗarsa da ɗora masa kofin ruwa a baki. Babu musu ya sha kusan rabi, sai kuma ya miƙe ya sake rungume Bappin. Murmushi Bappi yayi da sake rungumesa da ƙyau shima yana shafa bayansa.
“Please Bappi a sassauta mini koda maganar auren a janye”. Ya faɗa lokacin da Bappi ke ɗagosa da ga jikin nashi.
Murmushi Bappi yayi mai ƙayatarwa da shafa sumar Ramadhan ɗin yana girgiza masa kansa. “Babban sassauci kawai bin umarninmu Ramadhan. Idan kayi hakan sai ALLAH ya albarkaceka da nasarori a rayuwarka ok?”.
Maimakon amsa sai ya sake faɗawa jikin Bappin ya ƙanƙamesa har takai mai-martaba da baice komaiba har yanzu sakin murmushi. Shi kansa Pa gefe ya maida kansa yana nasa murmushin dan yasan mai shiga tsakanin Bappi da Ramadhan sai ALLAH. Shi kansa ya buɗe masa wutane dan yasan sa sarai akan kafiya da dagiya kan abinda bayaso. Shiko bazai taɓa yarda mahaifinsa yaji kunya ba tunda har ya riga ya amshi tayin su president ɗin….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button