BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

★★

     Dole akai gaggawar mika Raudha clinic na cikin gidan. Dan duk wanda yaga yanda take zubda jini abun sai yayi matuƙar firgitashi. Doctors ɗin kansu ruɗewa sukai, haka suka rufu a kanta kusan su uku domin ƙoƙarin ganin sun tsaida jinin sun ceto rayuwarta, dan tuni numfashinta ya bar gangar jikinta.
       Mama Ladi da duk ta gama ruɗewa ce ta kira Anne ta labarta mata abinda idonsu ya iya gani. Haka ma Mama Tambaya ta kira Aunty Hannah ta sanar mata. Cikin ƙanƙanin lokaci sai ga aunty Hannah ta iso saboda ta ɗanfi kusa da Anne. Itama Anne ba’a haɗa mintuna talatin ba ta iso harda Yafendo da Inna duk da suna fama da tsufansu.
       Har kusan azhar doctors ɗin gidan na gwamnati basu ce komai ga su Anne ba, dan Dr Hauwa ma da sukazo tare da su Anne itama ta ƙaru cikin doctors ɗin. Kowa yay jigum-jigum cike da fargabar abinda suke tsoron ji. Bama su ba shaƙiƙanta hatta da ma’aikatan gidan duk wanda al’amarin yaje kunnensa a tsorace yake. Gaba ɗaya sai gidan yay tsitt.
      Ramadhan baisan halin da ake ciki ba sai da suka fito salla COS ya samesa a office yake sanar masa kiran da ya samu da ga Chief security na gidan game da Accident ɗin da Raudha ta samu wanda har yanzu ba’a san musabbabin sa ba. Sosai hankalin Ramadhan ya tashi, amma a fuska bazaka taɓa tabbatar da haka ba, sai nanata kalmar cos ɗin yake a cikin ransa tamkar karatu. Gashi yana da shiga meeting a dai-dai lokacin kuma mai matuƙar muhimmanci. Haka dai ya dake cikin dauriya ya shiga meeting ɗin badan ya fahimci komai da aka tattauna a wajen ba. Baima haɗa mintuna talatin ba ya fito ya barsu su ƙarasa.
     Ya sake ganawar sirri da wani babban mutum da ga ƙasar Nigeria akan wani aikin haɗaka da suke sonyi da ƙasar ta Nigeria ɗin. Sai dai zaman nasu bai wani armashi ba saboda hankalin shugaban ƙasa rabi yana cikin gida. Awarsu guda suka kammala ya fita sallar la’asar. Abubuwan da suka rage masa na sauran awoyin ba wasu masu tsawwalawa bane idan ka cire ganawa da vice ɗinsa Alhaji Yaro glass, dan haka yasa cos sokesu sai gobe idan ALLAH ya kaimu shi kuma ya shiga gida.
      Iske su Anne da yay a gidan ya sake tabbatar masa da al’amarin babbane. Gashi sun sanar masa har zuwa lokacin basuji da ga doctors ɗin ba. Zama yay kawai cikin kujera ransa duk a dagule. Gaba ɗaya yama rasa wane kalar tunani zaiyi shi kam, yasan jiya ta shiga wani hali, amma lafiya lau ya fita ya barta yau ai.
        “Anne har yanzu basu ce komai ba? Kuma babu wanda yasan miya faru daga nan ciki?”.
        Cikin jimami da damuwa Anne tace,, “To ALLAH kaɗai dai yasan musabbabin gaskiya. Amma su su Lubnah sunce tana cin abinci ne abin ya faru, suma sai ganin jini sukai malale a ƙasa, shine ma suka shiga ruɗanin da har ya fargar da su Ladidi”.
      Iska ya turo daga ƙirjinsa ya fesar ta baki a hankali tare da kai hannu saman goshinsa yana ɗan murzawa. Cikin jimamami Yafendo ta karɓe zancen da faɗin, “Shi dama cikin fari na mai rabo ne, sai dai fitar nata yazo da haɗari. Dan tsinkewar jini irin wannan kam tashin hankaline babba ga mai ɓari, sai kace wadda aka ba wani abu”.
       Aunty Hannah da tun ɗazun batace komai ba sai satar kallon shugaban ƙasa da takeyi, dan yau ne ta fara ganinsa ido-da-ido itama a cikin gidan tunda take zuwa. “Da alama cikinne ma dai baiyi wani ƙwari ba shiyyasa. Amma al’amarin yayi kama da wadda tasha wani abu kam gaskiya”.
       “Ciki?!”.
Shugaban ƙasa ya firta cikin kasa ɓoye al’ajab nashi. Kallonsa sukai gaba ɗayansu duk da kuwa yayi maganar ne a hankali. Anne tace, “Ikon ALLAH, kai bama kasan da cikin ba kenan? Amma jiya ba Hauwa’u tazo ta dubata ba?”.
        Kansa ya ɗan jinjina mata sai kuma ya haɗiye dukan abinda ke masa kaikawo a cikin rai. “Itama sai yau zata bamu sakamako dama Anne”.
    Yay ƙoƙarin danne gaskiyar zancen saboda wasu abubuwa da ke masa kai kawo a rai da zuciya. Shiru falon ya sake ɗauka na wasu mintuna. Kafin ya miƙe da kansa ya fita da ga falon zuwa Clinic ɗin.
        Koda ya fito securitys sukai masa caa hana kowa binsa yay, sai dai duk da haka odilan ɗinsa bai yarda ya barsaba duk da dai a cikin gida ne. Ba wata tazara bace mai yawa tsakaninsu da clinic ɗin. Zuwansu yayi dai-dai da fitowar doctor Sambo da ga ɗakin ya baro su Dr Hauwa dake ƙarasa gyarata. Cikin ɗan rikicewar ganin oga kwata-kwata da kansa ya fara miƙa gaisuwa. Hannu kawai Ramadhan ya ɗaga masa, sai kuma yay masa nuni da office alamar su koma ciki..

    Suna shiga Aynah na Munirah dake laɓe suka kaima bango duka. Tunda suka kira Gimbiya Su’adah suka sanar mata ta basu umarnin zuwa su sami likitan su masa maganar komi za’ai kar bakinsa ya faɗi cewar da safe tasha maganin nan. Ya nuna tun jiya ta sha shi da yamma kuma ba yau ne na farko data sha ɗin ba. Shine sukazo fa, suna gab da isa ga doctor Sambo da suke zaman jira tun ɗazun sai kuma ga yayansu da kansa. Hakan ya saka su ɓuya dan kar ya gansu..

      “Wane issue kuka samu?”.
Ramadhan ya tambaya kansa tsaye dan shi baya son ɓoye-ɓoye ko jan rai a magana”.
      Cikin in-ina da fargaba Dr Sambo ya fara magana. “Ranka ya daɗe zuwa yanzu dai munyi nasarar ceto rayuwarta, mun kuma tsaida jinin. Sai dai ta zubar da jini sosai a yanzu haka muna ƙoƙarin samun wanda za’a ƙara mata ne. A binciken da mukai kuma mun gano magani ta sha wanda ya wuce ƙa’ida ma shine ya kawo tsinkewar jinin kamar haka. Badan anyi azamar kawota ba ma zata iya rasa ranta saboda maganine mai ƙarfi kuma abinda aka sha dominsa ma babu shi…”
        “Maganin miye?”.
“M…maganin abortion ne?”.
     “Abortion?”.
Ya maimaita maganar ta sigar tambaya.
    “Yes sir, sai dai kuma ma babu cikin, bincike ma ya tabbatar mana mahaifanta bai taɓa ɗaukar ciki ba sam. Hasalima a cikin yanayin perio….”
       “Ya isa haka..”
Ramadhan ya faɗa cikin ɓacin ran bayyanar kishinsa ƙuru-ƙuru daya kasa ɓoyuwa. Da ƙyar ya danne takaicin taɓa masa mata da sukai da sanin sirrin da basu dace da sani ba daga gareta ya fara magana mai kama da gargaɗi.
       “Wannan maganar ta tsaya iya ni da kai. A wajen kowa yazam cikinne ya zube da gaske. Kar a ƙarama matata jinin kowa a ɗiba nawa. Da ga nan zuwa gobe ina son sanin sunan ƙwayar data sha.”
     “Okay ranka ya daɗe insha ALLAH. Sai dai da zai yuwu zanso ganin abinda taci na ƙarshe dan kamar daga nan matsalar take”.
      Ɗan tsura masa ido Ramadhan yayi kamar mai nazari, sai kuma ya kauda idonsa yana miƙewa, “Muje ka ɗiba jinin, sauran aikin kayi magana da Chief security na gidan”.
      “Okay sir ALLAH ya ƙara lafiya da nisan kwana. Ya kareka a duk motsinka da rayuwar iyalinka baki ɗaya”.
     A saman laɓɓa ya amsa yana ficewa daga office ɗin.

      Ba ƙaramin tashin hankali zuciyar Ramadhan ta shiga ba lokacin da yaga Raudha. Cikin ƙanƙanin lokaci ta zube ta sake haske mai ban tsoro alamar dai da gaske babu jinin a jikinta. Cikin cije lip dinsa da masifar ƙarfi ya kai hannu saman kanta ya shafa gashinta lokacin da yake kaiwa zaune a kujerar da Dr Sambo ya ajiye masa. Sai kuma ya sinkuyi kanta ya kai bakinsa saman goshinta ya sumbata. ALLAH sarki Raudha, inama ace idonta biyu taga wannan al’amari. Na tabbata jininta zai iya daskarewa ma baki ɗaya.
     Kamar yanda ya hana a saka mata jinin kowa nasa aka saka mata, dan kuwa dagewa yay sai da aka ɗiba leda biyun da suke buƙata ɗin. Sai bayan an saka mata ne su Anne suka samu damar shigowa suka dubata, zuwa lokacin har Ramadhan ya koma cikin gidan dan shima yana ɗan buƙatar kwanciya ya huta. Ya bama Chief security damar binciko duk abinda suka tattauna da Dr Sambo. Dan haka babu ɓata lokaci Chief security ya fara aikinsa akan sauran abincin breakfast da Raudha ta ci.
         Ba’a samu wani tangarɗa ba wajen gano Raudha tasha maganin zubda ciki ne ta hanyar ruwan shayi da yay saura a flask ɗin. Wanda a zahiri Raudha ta shanye sa tas, sai dai lokacin da Ramadhan ke sanarma Chief security aikin da zaiyine zancen ya shiga kunnen Lubnah. A firgice taje ta matsa ruwan zafi da ga dispencer ta jefa sabuwar ƙwayar magani a ciki jikinta na rawa. Batafi mintuna biyar ba kuma Chief security ya iso falon dan ALLAH yasa ma ba’a kai ga kwashe kwanikan ba saboda halin da Raudha ta shiga ya ruɗa kowa.
        Kuku bai farga da abinda ke faruwa ba sai da Chief security yasa aka kira masa shi. Gaba ɗaya ya rikice ya ruɗe, dan zuwa yanzu labari ya fara karaɗe gidanne first lady ɓarin ciki tayi, ana kuma zargin an saka mata wani abune ta ci a abinci.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button