BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

      A hargitse ya ajiye wayar bayan sun kammala yana faɗin, “To tunda ya fasa binciken kiran ubanmi yasa Minister ɗin yake musu?”.

     “To wa ya sani”.

Cewar Alhaji Yaro glass.

  A harzuƙe Forma President ya ce, “Amma ya kamata ace irin waɗan nan abubuwan kana ƙoƙari saninsu Alhaji Yaro. Kasan kuwa wanene Ramadhan da Alhaji Hameed Taura?!!…”

    “Haba Alhaji Usama ya zakaga laifina? Bayan kaima kasan yaron nan komai yinsa yake a ƙudundune, daga shi sai matsiyacin cos ɗin nan da nafi tsana fiye da komai yanzu a duniya. Sai ko shegen kakansa ɗin nan da ubansa da nasan sune masu bashi shawara sama da mashawartansa na mulki…..”

      Mr MM zaiyo magana Oga kwata-kwata ya dakatar da shi ta hanyar ɗaga masu hannu. “Inaga wannan cece kucen ba shine mafita ba. Amma tabbas Alhaji Yaro akwai sakacinka anan. Sai dai muma munada laifi da bamu ɗoraka bisa hanyar data dace ka dinga sanin komai da komai ba. Amma ka sani matarka tana ɗaya daga ciki, dolene ta cigaba da kawo mana mike gudana a cikin gidan gwamnati ta hanyar matarsa tunda ƴa take a wajenta. Sauran magana kuma zamuyi daga baya idan na kammala nazari, amma a dakatar da kashe Alhaji Hameed Taura ba yanzu ba”.

   Cikin gamsuwa duk suka ɗaga masa kawuna, duk da a ransu suna son sanin dalilin dakatar da kashe Bappin, sai dai babu damar yin jayayya……..

__________________

     A matuƙar ruɗe Raudha ta kai hannu tana riƙo na Ramadhan jikinta na rawa. “Dan ALLAH kayi haƙuri, nasan wanda suka rasa ransu bazasu taɓa dawowa ba. Sai dai akwai mafita da zata taimaka a taimaki wanda sukaji raunika da tsananta tsaro ga wanda ba’a cutarba”.

      Duk da bai ɗago ya kalleta ba yanda ya dakata da yamutsa kan ya tabbatar mata yana saurarenta. Sai kuma ya ɗago ɗin ya zuba mata idanunsa. Hawayenta tai saurin sharewa tana miƙo masa wayarsa data ɗakko. Sai kuma takai ɗayan hanunta ta share masa nasa hawayen shima da har yanzu suke sakkowa.

     “Kasan yanayin ƙasarmu da ƙarancin kulawar da talaka yake samu akan harkar lafiya da tsaro. Lokuta da dama wasu a cikin jami’ai najin abu na faruwa sai dai tsoro da rashin kayan aiki na daƙilesu akai taimako, wasu kuma son zuciya ke hanasu yin kowane irin yunƙuri. To kamar hakane ga jami’an lafiya suma. Shiyyasa idan sakacin shugabanni ya haɗu da masu raunin taimako a jami’an lafiya ma yana ɗaiɗaita rayuwar talaka. Mafita itace yanzu ba wakili zaka saka ya bincika ba ko ya bama C.P na jihar umarni, kai da kanka ne ya kamata kai magana da I.G da C.P ɗin zasufi jin tsoron tashi suyi abinda ya kamata suma bawai su tura yara ba. Hakama asibitin da kanka ka kira Commissioner lafiya na jihar kai magana da shi dan ALLAH Ya Ramadhan……”

    Ɗari bisa ɗari ya gamsu da maganarta, dan haka ya ɗago da sauri, wayar da take miƙa masa ya amsa yay dailing number cos. Kai tsaye yace, “Ka sameni”.

   “Ranka ya daɗe yanzu haka ina cikin gidan nan ai”.

  Cos ya faɗa da sauri gudun kar shugaban ƙasa Ramadhan ya yanke wayar. Duk da cos baya shigowa har nan yau dai ya bashi umarnin ya samesa. Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa sai ga cos ɗin. Saurin janye jiki Raudha tai daga rungumar da Ramadhan ya sake mata bayan yayi magana da cos. Sai dai hanunta ya riƙo cikin nasa dole ta zauna a hanun kujerar da yake a zaune hanun nata rumtse a nasa.

     COS ya rissina yana gaishe da Raudha data amsa a kunyace, dan yanda ya gansu da yanda yake bata girma har mamaki takeyi.

   Cikin bada umarni Ramadhan yace, “Ina bukatar magana da I.G & commissioner of police na jihar, tare da commissioner lafiya”.

    Kai Cos ya jinjina yana mai fara danna wayarsa. A taƙaice Cos yayma I.G bayani ya mikama Shugaban ƙasa Ramadhan wayar. Koda ya amsa bai wani tsaya sauraren gaisuwar ɗin ba da jikinsa keta ɓari da ga can shi zaiyi waya da shugaban ƙasa. Kamar yanda Raudha ta bashi shawara haka yayi, yana gama kora masa bayani cike da ƙasaita kamar bashi ya nema birkicewa ba yanzu ya miƙama COS wayar. Amsa yay da girmamawa ya sake kira masa C.P na jihar Kuddo da Commissioner ɗin lafiya. Daga ƙarshe yasa aka kira Gwamna ɗin jihar shima inda Shugaban ƙasa Ramadhan ya balbalesa da masifa jin tamkar ma shi babu wata damuwa tattare da shi.

    ★Tabbas umarnin shugaban ƙasa Ramadhan yayi matuƙar tasiri, dan cikin ƙanƙanin lokaci dukkan abinda ya lissafa aka ninkashi ga jama’ar wannan ƙauye. Kafin wayewar gari tako ina garin jami’an tsaro ne har cikin dazukan yankin da sauran ƙauyikan, ga helicopters na sojoji sai yawo suke ta sama. Na asibitima suna samun ƙyaƙyƙyawar kulawa. Waɗan da sukai musabbabin fara haɗa rikicin da CP ya bada umarnin dankosu sai ga gawarwakinsu a cikin waɗanda suka mutu. (Dama haka fitina take, a mafi yawan lokaci wanda ya takalota shi take fara zubarwa a ƙasa. ALLAH ka zaunar da ƙasashenmu lafiya. ya gafarta mana kurakuranmu ka wadatamu da tsarkakakkiyar zuciya????).

★★★

     Da ga Raudha har Ramadhan idan sunyi barcin kirki a wannan dare sai dai ɓarawo. Ga mura ta mugun addabarsa da zazzaɓi mai zafi ma ya kwana. Yayi waya da Bappi yayi da Pa duk akan lamarin. Anne ma ta kwantar masa da hankali ta hanyar nasiha sosai da muhimmincin tashi tsaye akan addu’a .

   Basu kaɗai ba hatta Bilkisu da damuwar ta kwana. Duk da dai nata tsananin tashin hankalin nada nasaba da halin da taga Yayansu da Raudha a ciki. Adalilin hakan ma yau a ɗakin Raudha ta kwana. Ita kuma Raudha a ɗakin Ramadhan suka kwana tare.

     Da sassafe shugaban ƙasa Ramadhan yabar gidan batare da sanin su Raudha ba, dan ɗakinta ta tafi yin sallar asuba bayan ya fita massalaci shima. Sai da suka fito sukaci karo da shi a tv ana nunasa a cikin ƙauyen Kauci, abinda zai birgeka har da shi cikin tawagar masu zana’ida duk da karancin lokacin dake garesa. Ana kammalawa suka baro garin sai dai yabar jama’arsa suna sake zagaya ciki da bai ɗin ƙauyen. Tare suke da gwamnan jihar Kuddo ɗin. Daga ƙauyen asibiti suka wuce nanma shugaban ƙasa Ramadhan ya duba wanda suka sami raunika. Da ga haka bai ƙara ko minti biyarba a jihar Kuddo suka nufo Bingo dan da ƙyar yay squeezing time ɗinsa dama. Sai dai abinda yayi ɗin ya kara masa kima da daraja a idanun talakawan ƙasar NAYA. Gaba ɗaya a yinin nan babu abinda kakeji sai ruwan albarka da ake jera masa tako’ina. 

   Yayinda a ɓangaren su Alhaji Yaro glass kuma sukai yinin baƙin ciki da ƙunci dan basuyi zaton shugaban ƙasa Ramadhan zaije har ƙauyen ba domin nuna kulawa. Ba ƙaramin shiri ya wargaza musu ba akan hakan.

    A ɓangaren mai gayya mai aiki kam Ramadhan yau ya yini ne cikin damuwa da ɗunbin fargabar wannan mulki mai cike da ƙalubale kala-kala. Tun ba’aje ko inaba fa kenan, inaga nan gaba kuma da shekaru huɗu da watanni kusan bakwai ke jiransa. Kai anya kuwa zaya iya?. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button