BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

(????????saifa aljanin kam).

★★★★★

      WASHE GARI kamar yanda ya faɗa kusan 8am ya shigo ɗakin nata cikin kwalliyar suit baƙaƙe da suka fiddo masa ainahin tsarin halittarsa da ƙyawun haiba da ƙuruciya. Duk ramar nan ta campaign ta ciko fatarsa ta sake fresh sai ƙyalli yake yi.
        Kamar ko yaushe gaisheshi tayi sai dai taƙi yarda su haɗa ido dan har yanzu kalamansa na jiya basu bar bitar kansu a brain nata ba. Tsaf ya fahimci halin da take ciki amma sai ya basar. ATM card ya ajiye mata da wasu takardu guda biyu batare da ya mata wani bayani ba. Ya ɗan kalla agogon hanunsa yana furzar da iska a hankali….
      “Zaki iya fara fita school idan kinji ƙarfi, idan kikaiwa gargaɗina ɗaukar wasa zaki iya rasa karatun baki ɗaya. Abota da wani namiji ko ɗan uban waye bana buƙata. Tarkacen ƙawaye bana ra’ayi. Kiyi abinda ya kaiki”.
       “Insha ALLAH bazaka sameni da ƙinjin magana ba. Sai dai ina roƙon alfarmar securitys ɗin nan basai na dinga zuwa da su school ba, hakan zai iya nisanta idanu a kaina na zauna lafiya ga kowa dan ALLAH. Sannan ina son…..”
     Sai kuma tai shiru ta kasa ƙarasawa.
      “Bana son kwana-kwana, idan zakiyi magana kiyita kai tsaye”.
    Nanma kanta kawai ta jinjina masa. sai kuma ta ɗan ɗago a marairaice yanda zaifi tausayinta ta ce, “Dama ina son ne naje gyaran kai da kitso na kuma je naga Mummy i miss her”.
       Miƙewa yay yana gyara necktie ɗinsa, a ɗan daƙile yake faɗin, “Well kina da damar hakan, sai dai bako yaushe nake buƙatar ganin kitso a kan matata ba. Idan nai buƙatar hakan zance ayi”.
     Sototo tayi tana kallonsa baki buɗe har yaje ƙofa. (Oh dama yana mata kallon mata ne wai dama? Ba ƙawance yace kawai suy…..) ganin zai fice tai saurin katse tunaninta. “Dan ALLAH zuwa wajen Mummy fa to?”.
          Yanda tai maganar cike da zalama ya sashi ɗan waigowa ya dubeta, sai kuma ya ɗauke kansa “Zamuyi waya”. Ya faɗa yana ficewa gaba ɗaya…………..✍
Typing????

BAƘAR INUWA????????AREWABOOKS????????

https://arewabooks.com/chapter?id=62bc34197660dfc79da0e14b

Episode 41

………..Yau kwanan shugaban ƙasa Ramadhan da wasu mutanensa uku kenan a ƙasar UK. Zuwa yau kuma Alhmdllhi jikin Raudha yayi sauƙi sosai. Abin ƙarin farin cikin kuma a jiya Asabe da hajiyar birni da Hajiya mama suka zo suka dubata, jitai kamar karsu wuce, dan kuka rurus ta dinga ma Asabe da ta shagala a kallon fadar Shugaban ƙasa da ALLAH ya jeho ƴarta ciki. Ko’a mafarki, ko’a hasashe bata taɓa kawo kwatankwacin hakan a ranta ba. Wani iko sai ALLAH, shiyyasa masanin gaibu sai shi. Bawa karka takurama ranka da hassada da ƙyashi dan baka isa canja komai daga rayuwar waninka ko taka ba. Duk abinda ALLAH ya ƙaddara masa sai ya cimmawa a duniya ko kana so ko baka so. Sai dai baƙin ciki ya cigaba da zama abokin taka rayuwar. Dan kuwa ita ƙaddara ta riga fata inji bahaushe.
         Gaba ɗaya sai taji ta sake tsanar kanta da abubuwan da suka faru a Hutawa ita da M. Dauda. Tasan ko bajima ko ba daɗe sai an dingama ƴaƴansu har jikoki gori da waɗan nan halayyar, dan ma Raudha bata sanar mata an daɗe da fara mata gori da su ba.
         Zuwan Bilkisu da take kira da Aunty B yay mata daɗi a yau ɗin, dan tazo ne a gabar da take shirin fita wanke kai tunda ya nuna baya ra’ayin kitson duk da ta kasa gano dalilinsa na waɗan nan sharuɗɗan. Tare da Bilkisun suka fita wajen wani haɗaɗɗen gyaran jiki, kai dama dukkan buƙatun tsafta da ƙwalisa na mata. Wajene mai tsaro da sirri, dan mai wajen aminiyar Bilkisu ce. Tunkan su tafi kuma tai kiranta ta sanar mata cewar gasu nan zuwa da first lady tana buƙatar raguwar mutane a wajen.
        Cikin rawar jiki miss xoxo ta sallami kaso biyu da rabi bisa ukun mutanen wajen saloon ɗin nata da kayan ƙamshi. Vip section ma ko empty ya koma dan first lady ba wasa ba. Ta zaɓo ƙwararrun ma’aikatan ta da tasan aikinsu babu wasa a ciki irin su Hafsat Rano, Mamu gee, Huguma, Bilyn Abdull. Ta sakasu shirya komai.

(To Zafafa’s kuma ba’a samu ministers ba an koma aikin saloon a YERWA INCENSE AND MORE ????????????????)

      Tarba ta girmamawa first lady Raudha Ramadhan Taura ta samu, duk da zuwane na sirri hakan bai hana wasu farga ba suka fara ɗaukar hoto a sace. Sai dai Alhmdllhi kasancewar shigace ta mutunci a jikinta hijjab har ƙasa da niƙaf ya taimaka ƙwarai da gaske wajen bata nutsuwa. Babu zancen zaman ɓata lokaci bayan gaisuwar girmamawa data dinga samu ga ma’aikatan wajen  da har ƴar ƙwalla tayi aka fara mata gyaran jiki tako ina. Dan kuwa Bilkisu ce ta lissafa duk abinda ya dace a matan.
               Hummm lallai mace ƴar ƙwalisa ce kam. Dan kuwa gyaran da Raudha tasha duk da akwai na amarci a jikinta hakan bai hanata sake fitowa ba fes tamkar wata balarabiya, Bilkisu kanta babu abinda take sai yabawa. Batai ƙasa a gwiwa ba ta shiga ɗaukar Raudha hotuna dan wando da riga ta tilasata mata sakawa da zasu fito. acewarta basai tazo wajen saloon ɗin ana faman sakata rage kaya ba. Badan taso ba ta saka baƙin wandon jeans da top white anyi rubutu da Silver and black ƙyalƙyali a gaban rigar. I’m Beauty. Sai hijjab data ɗoro kawai a samansu.
         Yanda hotunan sukai masifar ƙyau yasa Billy turama Yayansu a email ta kuma ɗaura wasu a status ɗinta tare da shafinta na twitter. Duk da babu wanda ya gane Raudha cikin ƙanƙanin lokaci ta fara samun Comments kamar banza da like. Harda masu cewa suna kamu. Dama ga shafin nata na sele… ne cike yake da followers kamar hauka, dan tana harkar business ɗinta da koya girki itama.
     Tana ɗora hoton ta sauka da nufin sai dare zata duba Comments kamar yanda takeyi, suka kuma tattara da ga Saloon ɗin suka fito driver da securitys nata na jiransu. Raudha bata san Bilkisu tayi posting pictures nata ba, kawai dai yanda akai mata gyara na musamman harda jan lallale a yatsu ya sata farin ciki. Sai ɗan baƙi kaɗan da akai mata a bayan hanunta. Ga haɗin turarurruka na YERWA INCENSE AND MORE miss xoxo ta haɗo mata cikin leda babba.
       Suna dawowa gida suka iske su Lubnah zasu fita gidan su Aynah. Batabi takansu ba dan manna musu hauka take yanzu bata shiga sabgarsu. Dan haka a matuƙar ƙulle suke da ita musamman ma Aina’u da takejin duk duniya a yanzu bata da maƙiyya sama da Raudha.
       Salla suka farayi, barcin da take ɗan jine ya sata kwanciya tabar bilkisu na kallon wani series.

ENGLAND (LONDON)

          Tashin su kenan a meeting ɗin da shine na uku akan abinda ya kawosu ƙasar a kwanakin nan uku da sukayi. Tafe yake gwamnonin da sukai masa rakkiya su biyar biye da shi sai ministers uku da odilan nashi, babu abinda kake gani sai hasken camaras alamar hotuna yake sha da ga ƴan jarida da dama tun ɗazun suke tattauwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa. Hakama wasu a cikin gwamnonin da ministoci duk an ɗanyi hira da su.
      A gajiye yake, yana shiga masaukinsa abinda ya farayi wanka, ya ɗan sha shayi sannan ya ɗan zauna domin duba abinda ya shafi family nashi da Business da rashin lokaci ya hanashi nutsuwar yi a kwanaki ukun nan. Cak ya tsaya da kofin shayi a baki zafin shayin dana kofin na ƙona masa laɓɓa. Ya dire kofin tare da fitowa a twitter ɗin da ya shiga cikin zafin rai. Haka yakeyi lokaci-lokaci yakan bibiyi shafin kaf ƙanensa na yanar gizo domin tabbatar da abinda kikeyi. Koda bai shigaba ma kika ɗora abu yakan gani. Idan kuma yaci karo da abinda bai masa ba zaka gane kuranka a hannunsa. Babu wani ɓata lokaci yay dialing number Bilkisu da yaga hotunan a shafinta, sai dai iya ƙoƙarin ya kasa samunta. Canja akalar kiran nashi yay zuwa ga number da tunda ya ajiyeta a wayar bai taɓa kira ba. Cikin sa’a kuwa ta shiga……..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button