BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

   Murmushi kawai Anne keyi jin bayanin surukar tata. Ita bazata hanata zartar da hukuncin aurawa Ramadhan wata matarba, sai dai bazata amince a cutar mata da jika ba dan ita kanta ta jima da fahimtar wacece Adda Asmah.

   “Shike nan kije zan samu Dattijo da batun, zai kuma nema Ramadhan ɗin yaji tabakinsa. Idan ya amince da auren mu masu murna da farin cikine akan hakan. Fatanmu ALLAH ya basu zaman lafiya kawai.”

     Duk da ranta ya ƙara ɓaci sai ta amsa da amin. Ta fice zuciyarta na ayyana mata maganin Ramadhan da zatayi. Dan bazata taɓa yarda ya nunama kakaninsa baya son auren ba. Tasan yana bijirewa shikenan bazasu bata goyon baya ba.

,,,,_,,,,__

     Barci ya sake sha sosai har wajen sha ɗaya. Ring ɗin wayarsace ma ta tilasta masa buɗe idanu da ƙyar. Ido a rufe ya kai hannu a side drawer da nufin kashe wayar sautin ring ɗin ya hanashi hakan dan yasan Maah ce. Komai bai kawo ransa ba sai tunanin taji baida lafiya maybe. Ya buɗe ido da ƙyar yay picking yana kaiwa kunnensa.

    “Barka da asiba Maah!”.

Gaban Gimbiya Su’adah ne ya faɗi, tai saurin cire wayar a kunenta tana kallo…..

   “Maahhh!”.

Daya sake faɗa cike da kasala da barci ya sakata gaskata zarginta. Da sauri ta latse wayar ta kasheta gaba ɗaya kanta na juya mata. (Har ita Ramadhan zai amsawa waya yana tare da mace. Innalillahi….. Shikenan yaronta ya gama watsewa hanun jikar karuwai)…..

   A ɓangaren Ramadhan kuwa tunanin network ne ya sashi sake dialing number ɗin tata da ƙyar yana kaiwa kunne da lumshe idanu. Sai dai switch up ma ake sanar masa. Yanayin rashin ƙarfin jikin har yanzu ya sashi ajiye wayar kawai da tunanin zuwa anjima zai nemeta. Sai dai ya sake jan ƴan mintunan a kwance kafin ya tashi zuwa bayi, sosai yunwa yakeji na ci masa hanji, badan haka ba baya tunanin zai iya tashi yanzun.

     Shigarsa wankan baifi da mintuna biyu ba Raudha ta shigo hanunta ɗauke littafin data rubuta lecture ɗin jiya tana ɗan bitar abubuwan da bata fahimta ba, dama tun ɗazun take zaryar dubashi da ga falo zuwa bedroom ɗin. Jin motsin ruwa a bayi ya sata yanke shawarar gyara ɗakin a gaggauce ta fice kafin ya fito. Littafin ta ajiye a stool ɗin mirror batare data rufe ba. Cikin rashin sa’a tana tsaka da gyara kayan saman mirror ɗinsa dake a wargaje ya fito. Sosai ta diririce, tai azamar juya masa baya zuciyarta na luguden daka….

     Duk abinda tai akan idonsa ne, har yayi kamar zai basar yanda ya saba sai kuma ya canja shawara. Inda take ya cigaba da takawa yana goge sumarsa da ruwa yaɗan taɓa kaɗan zuwa gefen wuyansa da kunne. Cak ya tsaya sakamakon idanunsa da suka sauka akan littafin nata, ya ƙurama hand writing ɗin ido zuciyarsa na wani irin zillo, hatta da numfashinsa sizing yake wajen fita daga ƙirjinsa…..

     Jin kamar tsayuwar mutum a kanta ya sata saurin juyowa saboda tsorata, dan bataji motsin ƙarasowarsa inda take ba. Yunƙurin barin ɗakin tai gaba ɗaya taji ya cafko hanunta tare da fisgota ta dawo baya, gaba ɗayanta ta faɗa masa har ɗayan hannunta na ƙoƙarin sauka akan ƙirjinsa dake nason ruwa. Ido ta rumtse da ƙarfi da son ɗage hannunta ta tokare tsakkiyarsu, sai hakan ya taimaka mata bata faɗa masa jiki gaba ɗaya ba. Sai dai kuma a bazata da tai niyyar jan jikinta baya cikin in..ina tana faɗin, “I’m sorry”.

   Har yanzu idanunsa akan littafin suke, sorry data ambata ne ya dawo da zuciyarsa gareta, dan ya lula duniyar wani tunani daban, kamar yanda ya taɓa mata lokacin da ƴan gidansu sukazo dubasa ya ƙara matso da ita jikinsa dan bai saki hanunba dama. Mannata yay da jikin nasa duk da taƙi janye hanun nata. Kamar zata fasa kuka ta sake buɗe baki zatai magana dan ita hankalinta bai kai akan abinda yakema kallon ƙurulla ba saboda a rikice take…

     ‘Shiyyy!!’ Ya faɗa yana maido idanunsa kanta da manna bayanta da jikin mirror. Kumburarrun idanunsa dake baibaye da mura ya sauke akan face ɗinta, ganin lips nata na rawa alamar sonyin magana ya girgiza mata kansa. Sake rintse idanu tai da ƙarfi. Murmushi ya saki mai ƙayatarwa idanunsa na cigaba da bin fuskarta da kallo, haka kawai yake shiga nishaɗi idan ya ganta a yanayin tsoron nan.

    “Hy! Buɗe idonki”.

  Yay maganar a dake kamar ba shi ya gama murmushi ba. 

  “Dan ALLAH kayi haƙuri..” Raudha ta faɗa cikin tsananin taraddadi kamar zatai kuka.

       Sake matsar da fuskarsa yay gab da tata yana busa mata numfashinsa. Cikin wata iriyar muryar da badan a gabanta yake ba zata rantse bashi bane ya cigaba da magana. 

     “Kinsan ALLAH idan baki buɗe kin kalleni ba zan baki mamaki yau, ba ruwana da Ustazancin ki kaca-kaca zan miki”………..✍

BAKAR INUWA…!!

Chapter 47
47

…………So take tabi umarninsa ta buɗe amma ta tabbatar bazata iya kallonsa ba riga ba. Sai tayi kamar zata buɗe sai ta maida ta rumtse da ƙarfin tsiya. Tayi haka kusan 3times amma ta kasa. Cike da mugunta ya saki murmushi yana saka hanunsa guda ya janye nata data tokaresa da shi. 

   Wani irin ƙuuuu! Cikin Raudha ya bada sautin da har Ramadhan sai da yaji lokacin da taji saukar lips nashi akan nata daketa ƙyallin lipsgloss mai ƙamshin strowbarry. Shi kam da yayi da niyyar tsokana duk yanda yaso janye nasa lips ɗin sai yaji bazai iya ba, cikin rashin ƙarfin jikin da ke tare da shi ya sake manneta da mirror ɗin tare da rumtse ɗayan hanunta dake cikin nasa ya manne jikinsu waje guda yanda har numfashinsu ke fita da ƙyar….

     Ya riga ya mata matsewar da rawar jikin nata ma baya tasiri, sai zuciyarta dake mugun gudu a ƙirjinta har yana iya jiyowa. Randa su Anne sukazo yayi kissing nata sai dai ba irin na yau ba. Na yau babu sassauci, kai tsayene, cike da salon daya sata shagala tuni tsoronta ya gudu saƙonsa ya fara shigarta ɓargo da jini. Itama tanada lafiya, duk da abinda takeji sabo ne gangar jikinta bataƙi amsaba, dan ta kai shekarun da zata iya buƙatarsa. Sai dai rashin sabo ya sake tabbatar da ruɗaninta, dan lokacin daya janye bakinsa kasa tsaiwa tai a kan ƙafafunta. Babu shiri ta sake ƙanƙamesa. Bazata iya ɗagowa ta kallesa ba, sannan ƙafafunta ma bazasu iya tsayawa akaran kansu ba, dan jikinta babu abinda yakeyi sai mazari.

    Duka hannayensa biyu ya dafe kan mirror ɗin da suke jingine, kansa na bisa kafaɗarta, idanunsa duka a rufe suke saboda abinda ke faruwa a cikin nasa jikin. Lallai yasan ya takaloma kansa, ya kira ruwa yau. Yana zaman-zamansa da lallaɓa yanayinsa gashi nan ya takaloma kansa ruwa wajen neman tsokanarta ya tsokanoma kansa abinda ke kwance shekara da shekaru.

    Sunayen ALLAH ya shiga ambata a zuciyarsa da son janye jikinsa da sauri, sai dai Raudha data dabaibayesa sam ta hana yuwuwar hakan garesa. Sai ma ƙara ƙanƙamesa tai dan bata fatan ya ganta a yanayin da take. Sake gwada janyewa yay itama ta sake ƙanƙamesa. Dole ta sashi buɗe ido yana kallon kansa da bayanta ta cikin mirror. Murmushi ne ya suɓuce masa, sake duban idanunsa da suka kaɗa sukai jajur yayi alamar fitinace kwance a cikinsu. Hannunsa ɗaya ya ɗaga da jikin miron ya kaisa kanta ya ture hular data saka, a take gashinta dake ɗaure ya bayyana. Yatsunsa ya tura ciki baki ɗaya ribbon ɗin ta fice duka.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button