BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA????????????????????

1~ KUFAN WUTA????
Safiyya Huguma

1~ BAQAR INUWA????
Billyn Abdul

1~ RAYUWAR MACE????
Hafsat Rano

1~ MASARAUTA????
Miss Xoxo

1~ NOOR ALBI❤‍????
Mamuhgee

Guda 1????300
Guda 2????400
Guda 3????500
Guda 4????700
Guda 5????1k

ZAKU BIYA KUDINKU ANAN????????

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya????????

09032345899

KATIN MTN????????

09166221261


JAMA’AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan????????

Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F

ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA????????

+227 95 16 61 77

TEAM ZAFAFABIYAR????????????????


BAƘAR INUWA…????????

Da ɗumi-ɗuminsa????????????????????????????????

Please
Follow me
Share
Comments akan abinda ya shige maka duhu.

     _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar????????????????????????_

YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za’a cike Form ɗin kamar haka: –

Enter your name: (Cikakken sunanki)

Enter your mail: (Email ɗinki)

Enter an username (Sunanki)

Enter your password: ( misali 12341234)

Confirm password: (misali 12341234)

Sai a taɓa Sign Up shikenan an buɗe account a ArewaBooks????????????.

Continue with Google – Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za’a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

Register – Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.

AREWABOOKS LINK kai tsaye

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3

Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com

Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App… Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine.

MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER

+234 903 177 4742

Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan????????????????????????.

ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????

Typing????

Episode 26

…………A ɓangaren shugaban ƙasa kuwa yana cikin gidan lokacin da aka kawo Raudha, sai dai yana tare da wasu manyan mutanen ƙasar NAYA da sukazo masa gaisuwar barka da shigowa gidan gwamnati. Daga haka suka cigaba da tattauna wasu abubuwa da suka shafi ƙasar tare da shi. Zaman saurarensu kawai yayi da tankaɗa da rai-rayar dukan kalamansu. Alhmdllhi zaman kuwa ya masa daɗi duk da yana buƙatar son kwanciya ya huta, dan ya fahimci abubuwa da dama wanda ada bai kawosu cikin ransa ba.
      Bai samu shigowa ba sai kusan ƙarfe ɗaya da rabi na dare, a galabaice yake da son kwanciya da kuma jin yunwa, dan haka ido rufe yashigo ciki batare da tunawa da wanzuwar Raudha matsayin mata kuma amarya a gidan ba.

★★

       Hasken ranar daya leƙo ta cikin labulen window ya haske fuskar Raudha ya sata fara motsa idanun da gyar, dan kanta har yanzu ciwo yake mata har a cikin barci. Idanun ta buɗe da ƙyar kuma a hankali, sai dai hasken ya sakata sake maidasu ta rufe sannan ta kare fuskar da hanunta. Sake buɗewar tai duk da nauyin da yay mata. Da ƙyar ta yunƙura ta tashi, tare da bin jikinta da kalllo zuwa ɗakin, ganin time ya sata tashi a zabure ta diro ƙafafunta bisa tattausan lafiyayyen carpet dake gaban gadon. Bata da nutsuwar cigaba da kallo da mamakin ɗakin, ta nufi ƙofar da zuciyarta ke tabbatar mata toilet ne. Ilai kuwa tayi sa’a dan ta dace da hasashenta. Nan ma bata damu da zaman yima komai kallon ƙurilla ba, duk da akwai abubuwan kallon kuwa bila adadin, tai alwala ta fito.

       Wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke lokacin data idar da salla. Tsami da ciwon zazzaɓi dake cin ƙashinta ya sata yanke shawarar sake komawa cikin toilet ɗin tayo wanka da ruwa mai ɗumi. Sosai taji daɗin jikinta, sai da ta fito kuma idonta ya raina fata, dan babu kaya ko ɗaya a ɗakin sai na jikinta. Jiri da takeji da rashin mafitar inda zata nema kayan sakawa ya sata faɗawa gadon ta sake kwanciya tare da jan bargo ta ƙudundune. Rawar sanyi ta fara a hankali kafin wani zazzafan zazzaɓi da yafi na daren jiya yay mata rijib.

★★

         Tun kammala tsaftar lungu da saƙo na gidan da farar safiya da ma’aikatan gidan sukai shugaban ma’aikata ya tattaro kowa sukai zaman dakon fitowar first lady dinsu domin gabatar mata da kawunansu. Sai dai kuma har kusan goma na safe babu ita babu alamarta. Shugaban ƙasa ko tun bakwai na safe yabi ta sirintacciyar ƙofar da bai zama lallai kowa na gidan ya gansa ba inba wanda suke a harabar gidan ko aiki ta sashen ba ya fita zuwa office.
    Basu gaji ba suka cigaba da zama har kusan sha ɗaya, wasu a cikinsu dai sai ƙunkuni suke a zuciya da sukar wulaƙancin first lady, waɗan da suke a gidan tun zamanin tsohon shugaban ƙasa na ayyana (ita kuma da salon wulaƙancin da tazo kenan). Wasu ko masu ɗan hankalin ciki na ayyana maybe ango ya angwance ne har first lady ɗin kuma amarya ta gagara fitowa. Haka dai sukaita tunani barkatai kowa da irin nasa hasashen har su aunty Mariya da sukazo kawo akwatinan lefen Raudha suka iso gidan.

         Kusan a tare suka iso da su aunty Hannah da sukazo domin amsa. Sai dai halin da suka iske Raudha a ciki ya sakasu mantawa da wani karɓar lefe ko badawa. Aunty Mariya da tunaninta ya tsaya akan shugaban ƙasa Ramadhan yayi angwancine amma ya tsallake Raudha ya fita sai faɗa takeyi. Dan duk wanda ya dubi yanyin Raudha ɗin, da idanunta da suka koɗe saboda kuka dole kai tsaye ransa ya basa abinda aunty Mariyan ke zargi.
         Duk falo suka koma bayan sun mata sannu, aka bar aunty Hannah kawai tare da ita, acewarta zata taimakawa Raudhan ta gyara jikinta. Dan tasan yaran yanzu da son jiki yanzu haka bata shiga ruwan zafi ba.
      Kalaman aunty Hannah ba ƙaramin ƙona ran Safina ƙanwar shugaban ƙasa dake bi masa a haihuwa da Aina’u da tazo kallon ƙwaf suke ba. Dan koda akace bara a kimtsa Raudhan Safina ta dubata tunda likita ce, ca tai bata iya duba patient na gida.
        Tsaf aunty Mariya ta fahimceta, dan kaf ƴaƴan gimbiy Su’adah idan ka cire Bilkisu da Basma babu mai ƙaunar auren Raudha, saboda gimbiya Su’adah ta gama fallashe musu sirrin asalin Raudha ɗin kaf da cusa musu ƙinta. Su Basma ne kawai basu ɗauki abin da muhimmanci ba. Acewarsu ma ai ba Raudha ɗince ta aikata karuwancin ba. Talauci kuma ba’a goshi yake ba balle a gane wanda ya fito a cikinsa, su dai sun son Raudha kodan taimakon kakansu da tayi wanda da yanzu labarin wani ake bashi ba.
        Aunty Mariya tasan yanzu Ramadhan zai musu matuƙar wahalar gani musamman a wannan ranar daya fara shiga office, dan haka tai kiran Anne ta sanar mata suna buƙatar doctor yazo ya duba Raudha ɗin. Anne da zuciyarta ke mata hashe irin na Aunty Mariya cikin damuwa tace, “Ya cutar musu da yarinya ko Mariya?!”.
     Cikin jin nauyin Annen Aunty Mariya tace, “Anne sai dai haƙuri, ƴaƴan nan namu na yanzu sam basu da tausayi. Komai yinsa suke da ƙarfin tuwo da tunanin abari ya huce…..”
        Ƙwafa Anne tayi cikin takaici ta ballama Shugaban ƙasa Ramadhan da ake kan gaɓar nunawa a television zaune a office suna gaisawa da vice ɗinsa Alhaji Yaro glass harara. “Kai gaka anan hankali kwance kabar ƴar mutane a wahale ja’irin kaya”.
    Oho baima san tanaiba, hasalima shi har yanzu bai tuna da wata Raudha ba a ransa. Musamman da tunda yazo office ɗin suna tare ne da vice ɗin nasa, bayan yayi zaman mintuna talatin da wasu manyan mutane. Yayi ƙyau matuƙa cikin shadda kalar ruwan ƙasa mai ɗan duhu kaɗan sai maiƙo take da ɗaukar idanu. Ɗinkin babbar rigane daya kara masa kwarjini da girman shekaru ga mai kallonsa. Fuskarsa tayi fayau saboda ramar da yayi, sai dai wasu kai tsaye suke fassara yanayin cikar haiba da kamalar fuskar tasa da ya sha angwanci ne kawai. Ga hularsa tangaran dake ta ɗaukar idanu na sake fiddo ainahin ƙyawunsa kai tsaye.
     Anne ta ɗauke kanta daga kallonsa dai-dai sanda aka sake nuno yana musabaha da Alhaji yaro glass, tsintsiyar hannunsa dake sanye da baƙin agogo da baƙin link mai brown stone suka bayyana. sai zabba na azurfa biyu dake a yataunsa wanda duk itace ta saya masa su a saudia.
        “Lafiya wai kiketa sababi ke kaɗai Janna?”.
    Dattijo Alhaji Hameed Taura ya faɗa lokacin da yake fitowa daga toilet ɗin bedroom ɗin nasa da Anne ke zaune. Cikin sake ɓata fuska tace, “Da jikanka nake mana”.
     “Oh-oh mi yayi ɗan bawan ALLAH ”.
     “Kaface haka mana. Yanzu Mariya ta kirani wai a tura musu likita. Yaje ya farma ƴar mutane babu tausayi balle duban ƙarancin shekarunta. Bai kuma tsaya neman mai taimakonta ba ya tsallake ya fita sabgar gabansa shi a dole ga shugaban ƙasa”.
     Murmushi mai faɗi Alhaji Hameed yayi yana kaiwa zaune kusa da matar tasa ƴar daru. Ya kamo hanunta cikin nasa idanunsa na yawo a fuskarta. “To amana afuwa dan ALLAH. Insha ALLAH bazamu sake ba”.
     “Ko jikina kunne ne ba yarda zan bazaku sake ba. Amma ina gargaɗinku da ku kiyayeni”.
     Tai maganar tana tashi da cire hanunta cikin nashi dan ta ɗakko ɗayar wayarta a ɗaki ta kira Doctor. Binta yay da kallo yana dariya ƙasa-ƙasa. Banda dai daru irin nata mutum da matarsa sai a hanashi yin yanda yaso. Shekarar Ramadhan nawa babu aure, kuma shi shaidane Ramadhan baya neman mata tun yana saurayi balle yanzun. Dole kuwa ya damƙi mace a samu matsala.
      Bata daɗe da fitaba ta dawo tana sabuwar mitar ƙin samun Doctor Hauwa’u, dan haka ta sake kiran Aunty Mariya taji yaya.
     Koda aunty Mariya ta ɗaga saita ce tama kwantar da hankalinta an samu doctor da tazo zata dubata. dan aunty Hannah ta kira wata ƙawarta dake nan kusa da fadar shugaban ƙasar.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button