BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹????‍♀️⛹????‍♀️????

ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA????????????????????

1~ KUFAN WUTA????
Safiyya Huguma

1~ BAQAR INUWA????
Billyn Abdul

1~ RAYUWAR MACE????
Hafsat Rano

1~ MASARAUTA????
Miss Xoxo

1~ NOOR ALBI❤‍????
Mamuhgee

Guda 1????300
Guda 2????400
Guda 3????500
Guda 4????700
Guda 5????1k

ZAKU BIYA KUDINKU ANAN????????

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya????????

09032345899

KATIN MTN????????

09166221261


JAMA’AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan????????

Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F

ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA????????

+227 95 16 61 77

TEAM ZAFAFABIYAR????????????????


BAƘAR INUWA…????????

Da ɗumi-ɗuminsa????????????????????????????????

Please
Follow me
Share
Comments akan abinda ya shige maka duhu.

     _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar????????????????????????_

YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za’a cike Form ɗin kamar haka: –

Enter your name: (Cikakken sunanki)

Enter your mail: (Email ɗinki)

Enter an username (Sunanki)

Enter your password: ( misali 12341234)

Confirm password: (misali 12341234)

Sai a taɓa Sign Up shikenan an buɗe account a ArewaBooks????????????.

Continue with Google – Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za’a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

Register – Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.

AREWABOOKS LINK kai tsaye

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3

Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com

Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App… Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine.

MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER

+234 903 177 4742

Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan????????????????????????.

ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????
Typing????

Episode 54

……….Koda suka kammala falon suka sake dawowa, ya kuma ɗaure fuska yanda bazata roƙesa fitar ba. Dole ta kama kanta dan kuwa koda ya zaunar da itama karshen 3seater sai ya kwanta shi ya ɗaura kansa a cinyarta. Ya kuma kamo hannayenta duk biyu ya ɗora a sumarsa sannan ya canja musu tasha.
     Raudha babu bakin magana, tun tana cuna baki gaba har laushin sumar da takema kallon zatai ƙarfi saboda yanayinta na irin tamu ada ya fisgeta ta tura yatsunta a ciki a hankanli. Lumshe idanu Ramadhan yayi da sauke numfashi a hankali dan hakan abune da yake matuƙar so a rayuwarsa shima.
      A hankali ta cigaba da wasa da yataunta cikin sumar cike da shauƙi harta shagala ta manta dawa take tare. Haka ta cigaba da wasa da sumar kansa cikin shagala tana kallon film, yayinda shi nashi idon ke’a lumshe ya lula duniyar tunani.

      ★Kowa bai damu da rashin ganinsu a gidan ba har yamma, sai gimbiya Su’adah ce data cika tai fam da takaici, dan har Muneera ta aiko tai mata cid ɗinsu ta koma ta sanar mata ai duk yau ma bata tunanin Raudha taga rana. Gara Ramadhan kan fita yayo salla. Dama kuma shi yaje ya gaisheta da safe ma.. Har lunch ta shirya masa da kanta da maganin da Adda Asmah ta kawo waina fidda son Raudha a ransane ya tsaneta. Har sai ya mata korar kare a government house. Sai dai abinda bata sani ba na tsananin jan ra’ayinsa da mallakar zuciyarsane akan Ayna’u, malamin daya bata ya tabbatar mata Ramadhan yaci maganin nan sai ya manta har gimbiya Su’adah ɗin ma da kaf Taura family ya koma ƙarƙashin ikon ƴarta Ayna’u, hatta da mulkin ƙasar NAYA Aynah ce zata koma mai tsarawa da zartar da yanda za’ayi.
      Sai dai kuma Ramadhan ya kwafsa mata baije sashen da rana ba. Washe garima babu wanda ya gansu, sai randa suka cika kwana uku yaje sashen nata shi da Raudha da rana. Hakan baisa ta gaza tanadin na dare ba a cikin gasashshiyar kazar da taji kayan haɗi na ban mamaki aka aika masa har sashen Anne da kunun madara da yasha zuma a ciki a wannan rana. Ita kanta Raudha basu ƙyaleta ba. A baki Bilkisu sukaji abinda tafi so, amma kasancewar guri ya ƙure aka haɗa mata zoɓo mai sauƙi aka barbaɗe da magani sanin Ramadhan baya shan zoɓo shi kuma.
     Tunda Lubnah ta nufi sashen Anne da abinci sai kuma zuciyar gimbiya Su’adah ta shiga ƙunci, rasa mike mata daɗi tayi tanata faman kaikawo a bedroom ɗinta. Gaba ɗaya zuciyarta na nuna mata ƙiyayya da abinda ta aikata akan ɗan data haifa saboda tsanar matarsa. Sai dai kiyayyar da takeji akan Raudha nata ƙoƙarin danne gaskiyar dake son bayyana kanta ga kuskuren da idonta ya rufe ta kasa fahimta…

       Sam Anne bata kawo komai a ranta ba ta haɗa kayan wajen gimbiya Su’adah a cikin dinner ɗin su Ramadhan. Taya ma zatai tunanin za’ai amfani da uwa wajen cutar da ɗanta? Ita bama ta taɓa kawoma ranta wani cikin surukan nata na bin malamai koda akan Pa ba. Tama shedesu akan hakan ɗari bisa ɗari dan bata taɓa ganiba gaskiya. Ita kuma mutumce da bata yanke hukunci akan abinda bata ganiba sam.
          Raudha yarinyace mai tsarta, haka kawai taji gabanta na faɗuwa lokacin da sukai zaman cin abincin. ALLAH ta shiga ambato a zuciyarta, yayinda Ramadhan gashin kaza ya ruɗesa ya ɗan ɗiba da cokali mai yatsu ya kai bakinsa yana ambaton “uhhm”. Kallonsa tai kawai batare data iya cewa komai ba. Sai da zai kai lauma ta biyu ne ALLAH ya bashi ikon ambaton Bismillah. Ƙaramar ajiyar zuciya ta sauke, koda yace suci kazan catai ta ƙoshi, dan itakam idan tace zatai irin cin namansa ai matsala za’a samu. Bai wani ci da yawa ba ya tashi akan zaije wajen meeting idan an tashi yazo yaci. Amma ta tabbatar taci abinci inba hakaba ya dawo ɗura zai mata da kansa.

     Gimbiya Su'adah ce ƙarshen shigowa. Ramadhan ya gaidata cike da kunyar tun safe bai koma sashenta ba. Koda yake Anne ma da suke tare sai ya fito salla take ganinsa. Ya ɗanyi mamakin yanda ta amsa masa a sake, ta kuma gaida su Anne itama. Kowa zaune yake a kujera har su Yafendo, shine kaɗai zaune ƙasan lallausan carpet ɗin falon domin girmamawa ga iyayensa.

     Ba Ramadhan ɗin kaɗai ba, hatta su Pa sakewar gimbiya Su’adah ya basu mamaki, duk da suna danganta hakan da abinda ta kawo take ganin zataci nasara. Su dai babu ruwansu, idan Ramadhan ya amince ya karɓa zasu tayasa so, idan baya so kam bazasu masa dole ba tunda yay musu biyayya akan Raudha kar su cika shiga hakkinsa.
  Bayan an buɗe taro da addu’a Bappi ya bama Gimbiya su’adah damar faɗin abinda tazo musu da shi kafin yau. Tunda ta fara bayani Ramadhan ya ɗago a rikice yana duban mahaifiyar tasa. Fara’ar fuskarsa kuwa tuni ta ɓace sai dai komai baice ba harta kammala. Bappi ya jinjina kansa da maida hankalinsa ga Ramadhan da ya maida kansa ƙasa.
      “Ramadhan kaji abinda mahaifiyarka tace. Tana buƙatar ka auri ɗiyar ƴar uwarta domin likita ya sanar matarka bazata sake haihuwa ba saboda ciki data zubar a kwanaki”.
       Ramadhan daketa jera kalmomin innalillahi a zuciya ya nisa da ƙyar. Abinda Maah bata sani ba ya daɗe da kammala bincike akan yanda Raudha tasha magani, sai dai takamaimai wanda ya bama su Muneera maganin suka zuba mata dama yake nema ruwa a jallo. Sai gashi a cikin sauƙi ta tabbatar masa da itace, domin inba itace ɗinba taya tasan mahaifar Raudha zata lalace harta gagara haihuwa….?
      “Ramadhan!”.
Inna dake gefensa ta kira sunansa. Numfashi ya furzar da ɗago idanunsa da suka kaɗa ya kalleta. Sai kuma ya maida kansa kasa yana ƙoƙarin danne ɓacin ransa.
      “Kiyi haƙuri Maah bazan bijirema umarninki dan baki isaba. Sai dai zanyi hakane tare da tabbatar miki wannan BAƘAR INUWAr da kike hangemin gwara ranar da kike gudanmin da ita. Ban musa miki wasu a dangin Ameenatu nada tabo na ƙaddarar rayuwa ba, amma ina son ki sani wlhy Ameenatu yarinyace kamila mai addini. Sannan ta kawomin mu..tuncin…ta har gida. Idan zan faɗa miki wacece wadda kikema kallon mutuniyar kirkin a yanzu zakisha mamakin hakan. Maah laifin wani baya shafar wani ko’a wajen UBANGIJI. Sannan ALLAH na fidda rayayye a cikin matacce. yana kuma fidda matacce a cikin rayayye. Hauhuwa kuwa ta ALLAH ce, amma insha ALLAH akoda yaushe zaki iya ganin zuri’ata basai na auri wata ba”.
     Dukkanin wata fara’a dake a fuskar gimbiya Su’adah ta ɓace ɓat, baka ganin komai sai ɗunbin ɓacin rai da azabar masifa. Gasu Pa kuwa gaba ɗaya murmushi ne kwance a fuskokinsu, bana bijirema gimbiya Su’adah da Ramadhan yayi bane. Na yabo da tabbatar da ingancin tarbiyyar Raudha da sukajine daga bakinsa. Wanda su sanin kansune Ramadhan baya iya boye abu inhar bai masa daɗi ba zai faɗa, hakama idan yayi masa zai yaba koda da murmushi ne. Koba komai hankalinsu ya sake kwanciya da yarinyar da suka jima suna kyautatama zato.
      Babu wanda ya sake cewa komai har ita. sai Inna ce tai musu nasiha da gaba ɗaya take nufin da gimbiya Su’adah take amma sai ta haɗa kowa da kowa a ciki. Daga haka taron ya tashi babu wani armashi. Dan ko bikin yaran gidan da sukaso tattaunawa a yau ɗin shima bai yuwu ba dole aka barsa sai wani lokacin dan ana jiran sauran gidajen angunan su kawo kuɗi ne. Ƴammata kusan shidda za’a aurar a gidan nasu Ramadhan. Ciki harda Lubnah da Bilkisu kuwa. Sai Sumayya, Rufaidah, Ai’sha da Ummita. Dukansu sunyi karatu wasunsu ma na aiki, Ummita ce kawai take kan karatun saboda manemin nata ya takurane yasa za’a haɗa da ita amma sa’ar Muneera ce ma. Koda yake ita kanta Muneera ɗin ta isa auren ai kawai dai dan akwai yayuntane.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button