BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

      Luf take shiru a jikinsa tana sauraren yanda yake sauke numfashi a hankali da sanya mata albarka. Yayinda hanunsa ke cikin sumar kanta yana faman wasa da ita duk ya birkita mata ita. Murya can kasa a ɗashe tace, “Ya Ramadhan sallar isha’i fa akeyi”.
      “Uhhm naji ai”.
Ya faɗa a shaƙe idanunsa rufe. Shiru tai bata sake cewa komai ba har kusan mintuna biyar sannan ya miƙe. Kai tsaye toilet ya shiga, hakan yasa Raudha lumshe idanu da sauke ajiyar zuciya takai hanunta saman cikinta tana shafawa. Bata san yaya zaijiba idan yasan tanada ciki, ita kanta a duk sanda ta tuna akwai ɗa mai alaka da shi tanajin tsantsar farin ciki. Badan shi shugaban kasa bane, badan shi jinin Taura family bane. Sai dai ɗunbin soyayyarta da take hangowa a cikin idanunsa. Motsin fitowarsa a bayin ya sata dawowa hayyacinta daga dogon tunanin data lula.
          Yanda ya fito yana goge sumarsa da jiki ya tabbatar mata wanka yayo, saurin ɗauke kanta tai ta maida gefe. Yay ɗan murmushi da ƙarasawa jikin Wadrobe ɗinsa domin duba kaya. “Madam tashi kiyi wanka muyi salla”.
       “Ni alwala kawai zanyi”.
Ta faɗa a shagwaɓe tana mikewa a gadon itama. Murmushi kawai yayi amma komai baiceba harta shige toilet. Sai dai kuma ashe cika bakinne kawai, dan itama dai hummm kawai…………✍

Alhmdllhi barka da salla, ALLAH ya maimaita mana ya amshi ibadunmu baki ɗaya. ALLAH ya dawo mana da mahajjatanmu gida lfy, ya jiƙan iyayenmu, ya ƙara mana lafiya da zama lafiya. Inama kowa barka da salla ina kuma jiran naman salla dan nagafa sai nayi tuni za’a kawon kenan????????????‍????.

Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹????‍♀️⛹????‍♀️????

ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA????????????????????

1~ KUFAN WUTA????
Safiyya Huguma

1~ BAQAR INUWA????
Billyn Abdul

1~ RAYUWAR MACE????
Hafsat Rano

1~ MASARAUTA????
Miss Xoxo

1~ NOOR ALBI❤‍????
Mamuhgee

Guda 1????300
Guda 2????400
Guda 3????500
Guda 4????700
Guda 5????1k

ZAKU BIYA KUDINKU ANAN????????

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya????????

09032345899

KATIN MTN????????

09166221261


JAMA’AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan????????

Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F

ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA????????

+227 95 16 61 77

TEAM ZAFAFABIYAR????????????????


BAƘAR INUWA…????????

Da ɗumi-ɗuminsa????????????????????????????????

Please
Follow me
Share
Comments akan abinda ya shige maka duhu.

     _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar????????????????????????_

YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za’a cike Form ɗin kamar haka: –

Enter your name: (Cikakken sunanki)

Enter your mail: (Email ɗinki)

Enter an username (Sunanki)

Enter your password: ( misali 12341234)

Confirm password: (misali 12341234)

Sai a taɓa Sign Up shikenan an buɗe account a ArewaBooks????????????.

Continue with Google – Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za’a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

Register – Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.

AREWABOOKS LINK kai tsaye

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3

Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com

Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App… Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine.

MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER

+234 903 177 4742

Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan????????????????????????.

ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????
Typing????

Episode 65-66

………..Fitowarta dai-dai da ƙoƙarinsa na kammala busar da sumarsa. Ya kalleta kawai ya ɗauke kansa baice komaiba. Dan rigartace dai a jikinta data shiga da ita ala dole babu abinda tayo. Sai da ya shimfiɗa abin salla ya miƙa mata wandonsa mai taushi na adidas da farar t-shirt. “Saka muyi salla lokaci na shigewa”.
    Kanta a kasa batare data kallesa ba tace, “Bafa abinda ya sameta”.
      “Humm Ameenatu kenan, karki manta na rigaki zuwa duniya. Bayan rigaki shekaru kusan goma sha takwas na baki, kinga a lissafi kuwa lokacin da nake a mizanin shiga shekarun girma na ɗa namiji aka haifeki”.
      Kunya kamar ta nutse. Dan sam batai tunanin ya ganeba. Dama sotai ta masa dabara sai sun tada sallar ta gudu ɗakin Anne ta canja kayan tai salla.
        “Hallo! Ko sai na nuna miki shaida ne dan rigar kanta ta tona miki asiri tare da wannan”. Ya tura hanunsa cikin hular kanta ya jawo silin jiƙaƙƙen gashinta a ciki. Da sauri ta kwashi kayan zata koma toilet”.
       “Hii aini ba surukinki bane canjasu anan konazo na canja miki kina ƙara makarar damu”.
     Babu yanda ta iya dole tabi umarninsa, bayan ta saka kayan suka gabatar da sallar. Suna idarwa wayarsa ta hau ruri, yasan Anne ce dan haka ya miƙe zuwa bedside drawer ya zauna a bakin gadon yana daukar wayar….
        “Kai ka fita idona kawomin yarinya taci abinci tana fama da kanta”.
      (Mutum da matarsa ƙarfin hali kenan) ya faɗa a zuciya yana sakin murmushi. A fili kam yace, “Okay Gimbiyar Bappi yanzu kuwa maida wukar”.
     
          ★Gaba ɗaya Raudha jitake kamar ta nutse dan kunya. Kanta a kasa ta risina ta gaida Anne da Bappi. Zata zauna kusa da Bilkisu dake tare da su yaja mata kujerar kusa da shi tare da kamo hanunta yanda su Bappi bazasu gani ba. Sai dai ya makaro sun gani ɗin. A kuma kallo ɗaya Anne ta fahimci wayo yaje yayma Raudha, sai dai addu’arta ALLAH yasa bai aikata abinda zai cutar da itaba tunda ɗinkin jikinta bai gama warkewaba. Tunda tazo ɗaki taga babu su tai niyyar kiransa a waya Bappi ya hanata. Acewarsa yasan Ramadhan na cikin hankalinsa bazai sake yarda ya aikata abinda zai cutar da Raudha ba. Gara su barsu su sasanta kansu da wuri kodan su Gimbiya Su’adah ma.
        Bilkisu ce ta zuba musu abincin, dan Raudha dai ta kasa motsin kirki. Gani take kamar su Anne sun fahimci abinda duk ya faru tunda har abu yakai ga canja kaya. Kowa nacin abincinsa hankali kwance amma banda ita. Tsakura kawai take kaɗan-kaɗan.
      “ALLAH in bakici abincin nan ba zan tonaki yanzu su Anne susan mikika aikato a ciki da hujja”.
     Wani irin ƙululu cikinta ya bada. Harta kasa daurewa saida ta ɗan dubesa. Gira ɗaya ya ɗage mata da sakin wani munafukin murmushi daya tilastata maida kanta ƙasa da hanzari. Duk abinda suke su Anne na lure da su, sai dai kowa ya ɗauke kansa kamar bai san anaiba.
         Farfesun kan rago Ramadhan yace Bilkisu ta zuba masa. Kamar jira tana buɗe bowl ɗin Raudha tai saurin toshe hanci da rike numfashinta. Babu wanda ya lura da hakan Bilkisu ta fara zubawa, kasancewar kusa da shi take tuni ƙamshin ya ƙara karfi a kusa da ita. Har takai amai na yunƙuro mata. Ta mike zaram zata bar wajen ya rikota.
      “Lafiya kuwa?”.
Kanta ta shiga girgiza masa da nuna masa ya saketa amma yaƙi. Anne ce ta fahimci abinda ya ɗaga hankalin Raudhan da sauri tace, “Ramadhan saketa”. Tai maganar tana mikewa.
       Sam ya kasa fahimta, a zatonsa wani abune daban, ina kafin ya samu damar cewa wani abu ta kasa daurewa ta fisgi hanunta da ƙarfi. Sai dai kafin takai toilet na bayin ta saki aman a waje. Gaba ɗayansu sukayi kanta har Bappi, dama Ramadhan tunda ta fisge ya bita. Amai sosai takeyi a wahale. Shiko gaba ɗaya ya cimimiyota jikinsa duk a ruɗe. Sai tambayarta yake mike damunta?.
          “Ramadhan ka barta taji da abinda ya dameta mana Please”.
Anne ta faɗa cike da tausayin Raudha. Sai da ya tabbatar ta gama ya ɗagata cak ya nufi sashensa da ita. Anne zata bisu Bappi ya riƙo hanunta yana girgiza mata kai da murmushi a fuskarsa. “Barshi shi daya jawo yay aikin”.
     Murmushi kawai tai da girgiza kai tana mintsininsa da nuna masa Bilkiau da ido. Yay karamar dariya da ita kawai tajisa. Mai aikin Anne ce tazo ta gyara wajen. Su kuma suka koma kan table suna karasa cin abincinsu kowa da tausayin Raudha a ransa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button