BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

1~ MASARAUTA????
Miss Xoxo

1~ NOOR ALBI❤‍????
Mamuhgee

Guda 1????300
Guda 2????400
Guda 3????500
Guda 4????700
Guda 5????1k

ZAKU BIYA KUDINKU ANAN????????

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya????????

09032345899

KATIN MTN????????

09166221261


JAMA’AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan????????

Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F

ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA????????

+227 95 16 61 77

TEAM ZAFAFABIYAR????????????????


BAƘAR INUWA…????????

https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09

Da ɗumi-ɗuminsa????????????????????????????????

Please
Follow me
Share
Comments akan abinda ya shige maka duhu.

     _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar????????????????????????_

YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za’a cike Form ɗin kamar haka: –

Enter your name: (Cikakken sunanki)

Enter your mail: (Email ɗinki)

Enter an username (Sunanki)

Enter your password: ( misali 12341234)

Confirm password: (misali 12341234)

Sai a taɓa Sign Up shikenan an buɗe account a ArewaBooks????????????.

Continue with Google – Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za’a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

Register – Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.

AREWABOOKS LINK kai tsaye

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3

Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com

Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App… Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine.

MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER

+234 903 177 4742

Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan????????????????????????.

ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????
Typing????

Episode 13

………..A hankali Ramadhan dake a bakin ƙofar ya cigaba da tako tsaftataccen marble’s ɗin falon, dan ya cire takalmansa tun a corridor ɗin daya raba falon farko da wannan falon, sai safa baka kawai. idanunsa akan kakannin nasa. Tafiya yake dai-dai da hurowar iskar hadarin dake kaɗa labulolin falon tare da walƙiya tamkar yana taku a saman kaɗawar tata ne. Harya ƙaraso gaban Baffi basu iya sun motsa ba, ya durƙushe gaban bisa gwuyawunsa tare da sauke jikkar kafaɗarsa. Hannu ya kai bisa kansa a hankali yay baya da hular nutsatstsiyar fuskarsa mai cike da kwarjini da cikar haiba ta bayyana.
A hakan ma bai iya dubansu ba, dan har yanzu idanunsa sakaye suke da gilashinsa mai nuna blue. Maimakon ya zaresa sai matsawa yay ya ɗora kansa bisa cinyar Bappin yana sakin wasu tagwayen ajiyar zuciya da lumshe idanunsa masu nauyi da fargaba.

A ɓangaren Pa ma yau tare yake da gimbiya Su’adah dan girkintane. Tsananin gajiyar dake tare da shi ta kaiwa da komowar da yayi yau kashi-kashi ya saka shi yin wanka da ruwa mai ɗumi da taimakon gimbiya Su’adah. Fitowarsu kenan a toilet ɗin tana tsane masa jiki da towel ƙarami. Ya kai dubansa ga labulen windows da aka ƙawata adon bedroom ɗin nasa da su. Yanda iska ke kaɗasu abin sha’awa ga mai kallo. Ajiyar zuciya ya ɗan sauke batare daya ɗauke kansa a jikin labulen ba ya fara magana a hankali.
“Da ace Bappi zai yadda da ya bar maganar nan ta takara. Saboda na tabbatar abinda yaso faruwa a yau yanada alaƙa da wannan siyasar da bana hango wani amfaninta a garemu ko kaɗan….”
Wani irin bugawa ƙirjin gimbiya Su’adah yayi. Domin ba ƙaramin ƙwallafa rai da ƙara jin alfahari takeba akan batun fitowa takarar tilon ɗanta namiji da Bappi ya kwaɗaita musu tun daren jiya. Zata iya cewa dukkan farin cikinta na yau da murmushinta yana da alaƙa ne da hakan kai tsaye. Idan ko mijin nata ya cigaba da nuna adawarsa akan hakan ko kokwanto lallai tana cikin ɗunbin rashin nasara kenan. Dan kuwa Bappi zai iya saurarensa akan hujjojinsa inhar ya samesa da batun……..
“Su’adah kinyi shiru”.
Pa ya faɗa cikin katse mata dogon tunanin data faɗa. Numfashi taja mai ƙarfi a ɓoye da ƙaƙaro murmushi tana kaiwa zaune a gefensa. Maɓallan rigar barcinsa dake ajiye gefe take ɓallewa bayan ta ɗakkota a hannunta.
“Ba shiru naiba Daddyn Ramadhan, nima wani tunani nakeyi game da maganarka. Tabbas zancenka nakan gaskiya, dan ni kaina harna fara jin tsoro. Idan har za’a iya harar mana Bappi irin haka akan wannan batun shi kuma Ramadhan dazai tsaya takarar yaya zata kasance kenan?”.
“Abinda nake hangowa kenan Su’adah. An illata mana yaro a baya batare da mulki ba, har takai ga ya nisancemu a yanzu saboda tabon da aka bar mana a zukata ya kasa barin ruhinsa. Inaga yanzun da ake son ɗora masa nauyin abinda ya girma shekarunsa. Suma da suke manya masu shekaru basu tsira ba balle shi da dudu shekarunsa talatin da biyar. Ko’a tarihi babu wani shugaban ƙasa a wannan ƙasar ta NAYA da akayi mai ƙarancin shekarunsa fa….”
“Ƙarancin shekarunsa basu bane damuwar Dadyn Ramadhan. Dan kuwa koba komai anzo da wani sauyine da al’ummar ƙasar NAYA zasuyi farin ciki da shi. Mun cancanci mu damu da gudun abinda zaije ya dawo, sannan kuma ta wani ɓangaren yanada ƙyau muyi dubi da talakawa masu buƙatar irin Ramadhan ɗin a yanzun, domin da gaske ƙasar NAYA irin Ramadhan take buƙata da shekarunsa. Badan shugabannin baya sun gaza ba, a’a suma sun taka irin rawarsu kuma munji daɗin ƙoƙarinsu da yaba musu, dan mulki ba abune na wasa ba. Wanda ke gefe bai isa sanin wahalarsa ba sam. Dan shi daɗin kawai yake hangen maiyinsa na ciki yake, sai dai abunda bamu saniba wahalarsa itace kaso 99. Kaso ɗaya kacal ɗin nan shine kawai jin daɗin ga ma’abota mulki. ALLAH ya sakama shugabanninmu da alkairi, ya yafe musu kurakuransu yay riƙo da hannayensu. ALLAH kuma ya basu ikon sauke nauyin al’umma dake kansu”.
Numfashi ya sake saukewa da faɗin, “To amin ya rabbi. Amma duk da haka ina jin tsoro Su’adah”.
“Karkaji tsoro Dadyn Ramadhan. Addu’a kawai zamu duƙufa yi, tare da tunanin ta hanyar da zamu maido Ramadhan gida a yanzu batare da mun sake ɗorama Bappi wani nauyin ba”.
“Eh kema kinyi batu na hankali. Inko hakane barama na leƙa bappin dan na manta ma ban sanar masa batun kammala fidda komai na zakkar ba yau, duk mun wuni cikin rashin kwanciyar hankali ba’a fitarba kamar yanda aka saba”.
Miƙewa tai tsaye tana taimaka masa ya saka jallabiya fara bayan ta ajiye rigar barcin gefe, dan tasan bazaije sashen su Anne da kayan barci ba. Hakan al’adarsace da girmamawa ga mahaifan nasa batun yanzu ba. Turare taɗan fesa masa sannan ya fice.

     Gimbiya Su'adah ta sauke nannauyan numfashi a ƙasan ranta tana godema ALLAH daya kasance yau girkintane har taji batun nan taima tufƙar hanci da wuri. Taya zata amince maganar nan ta koma ciki bayan ta fito. Da farko bataƙibama ace shi Alhaji Basheer ɗinne zai hau shugaban ƙasar ba. Dan koba komai darajarta zata ƙaru, ta fito daga gidan mulki mafi daraja da kima, gata tana aure a gidan dukiya sahun farko a ƙasar NAYA dama yankin Africa baki ɗaya. A ƙarshe a kirata first lady. Lallai data amsa sunanta *_SARAUNIYA SU'ADAH_* ba gimbiya Su'adah ba. Amma ko'a hakan ma ba komai baneba, dan samuwar mulkin ga gudan jininta wani abune mai girma da za'ayi ƙarnuka da zamanai da bazai mantu ba. Sannan dole ne a kirata uwar shugaban ƙasar NAYA. Dan haka itace da kanta zata zaɓa masa matar aure dai-dai da ra'ayinta. A wannan karon bazata sake sakaci irin na farko ba akan matar da Ramadhan zai aura.

(“Mulki! Mulki!! Mulki!!????????????” ).

    Turus Pa yay tare da ƙoƙarin haɗiye sauran sallamarsa a maƙoshi duk da ta kusan gama fita a harshensa. Ba komai ya jawo hakan ba sai tozali da yay da gudan jininsa zaune gaban Bappi da Anne. Gaba ɗaya fuskar tsoffin nasa babu alamun fara'a, yayinda Ramadhan ɗin yay ƙasa da kansa yana magana a kausashe mai cike da ɗaukar alwashi.
   Kai tsaye ya fahimci kausasa harshen nasa nada alaƙa da abinda yaso samun bappin a yau. Sarai ya sani basai an faɗaba, ɗansa Ramadhan mutum ne mai zafin zuciya ainun, abu kaɗan ke fusatashi ya hargitse tamkar baisan wani abuba wai shi sauƙin kai. Amma idan ka kallesa a fuska bazaka taɓa ɗauka ma yana magana mai alaƙa da masifa ba saboda fuskar mutane masu haƙuri da rashin son hayaniya garesa. Sometimes idan yay abu mutanen da basu san ainahinsa ba sukance bashi bane ba, dan a zatonsu ko yatsa ka sakama Ramadhan bazai taunaba saboda haƙurinsa da rashin son magana. Girman kai ne dai kam kowa na masa kallon mai shi kai tsaye, koda sau ɗaya ka fara ganinsa.
  Sai dai su duk sun san ba hakan baneba, Ramadhan bauɗaɗɗen mutum ne mai zafi da tsananin ɗaukar kai (girman kai inji bahaushe????). Tabbas baida yawan magana badan yana miskiliba, tsabar jin kai ne kawai ke hanashi magana a lokuta da dama koda ace ya dace yayi ɗin. Tabbas anan ɓangaren ya biyo mahaifiyarsa ƙwarai da gaske, dan saima ace ya ɗarata izza dajin mulkin a cikin jininsa fiye da ita da aka haifa a gidan mulkin. Sai dai kuma ta wani ɓangaren yanada wasu halaye kishiyar waɗan can da zama dashi ne kawai zai iya fiddoma wanda ya sanshi da waɗan can ɗin su.....
    “Ramadhan!”.

Pa ya faɗa cikin wata irin murya mai kaushi-kaushi da ɗaci. Dan haka kawai daya tuna yanda suka dinga bin Ramadhan akan yay haƙuri ya manta komai ya dawo ƙasar NAYA amma ya nuna musu bazaibi maganarsuba ya shiga dawo masa a rai.
Da ga Ramadhan har su Anne juyowa sukai suna kallon Pa ɗin, dan sam basuji shigowarsaba balle sallamarsa saboda tasowar iskar hadari dake ƙaruwa.
“Pa!”.
Ramadhan ya faɗa da sauri yana miƙewa idonsa akan mahaifin nasa.
“Miya kawoka gidan nan!!”.
Pa ya faɗa yana ƙoƙarin dakatar da Ramadhan daya miƙe da alamar ɗokin ganin mahaifin nasa da zumuɗin isowa garesa, dan jikinsa har tsuma yake.
“Pa!……”
Ya sake buɗe baki zaiyi magana Pa ya dakatar da shi.
“Karkace komai a gareni!!, zo ka fita a gidan nan yanzun nan!!”.
Yanda yay maganar babu wasa ya saka Ramadhan duban su bappi, kafin ya sake kallon Alhaji Basheer Taura.
“Pa…….!”.
“Ramadhan!! Nace ka fita a gidan nan yanzun nan!. Bana son sake ganin wannan fuskar taka!!”.
Alhaji Basheer Taura ya faɗa a tsawace yana nunama Ramadhan hanyar falon.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button