BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

    A wannan lokacin tsabar firgici zamu iya cewa Asthma ɗin Raudha ma motsawa ta nemayi. Dan da gaske numfashin ta a take ya fara fita a rarrabe har tana sarƙewa. Bai barta ba sai da ya fahimci yana neman kama wani layin saɓanin wanda yay niyyar bi kawai. 

   Shiru yay bayan barinta yana sauraren yanda hawayenta ke sauka a ƙirjinsa har yana huda riga yana ratsasa. Yay tattausan murmushi hanunsa saman kanta da akai ma kitson da baisan anyi ba. Sai da numfashinsu ya gama dai-daita ya kai bakinsa kan kunenta yana magana cikin muryar da batasan ya mallaka ba. “Cutie! Yaufa babu fashi sai anje duniyar samo ƴan huɗun nan bazan iya ɗaga ƙafa ba”.

   Sake ƙanƙamesa tai jikinta na rawa dan harga ALLAH tsoro ma yake bata. Kalamansa sake firgita rayuwarta takeyi. Shine na farko daya taɓa mata abinda wani namiji a duniya bai taɓa mata ba. Shine na farko daya taɓa ɗora hanunsa akan abinda wani mahaluki bai taɓa taɓawa ba. Shine na farko daya ganta a yanda wani bai taɓa gani ba sai yau, yau ɗin ma yanzun nan duk da bata da tabbacin ya kalleta ɗin…

   Ring ɗin da wayarsa tai a jikinsa ya sashi furzar da numfashi mai ƙarfi. Sosai idanunsa suka canja launi hakama fuskarsa tayi ja abinka da fari. Yasan Maah! ce, ya kuma san abinda take buƙata. Dan ta tabbatar masa tana son ganinsa daya dawo akan zancen aurensa da Aina’u. Da ƙyar ya iya saita kansa yakai wayar kunensa bayan ya ɗaga. Da sauri Raudha dake duƙunƙune a jikinsa tai saurin barin jikjnsa ta dire saman gadon. Bai hanata ba harta sake duƙunƙunewa cikin bargon daya rufa musu. Murmushi yay ganin yanda ta yayesa ita kuma ta nannaɗe a ciki kamar an nannaɗe gawa a likafani. Sosai ya tashi zaune ko zai sake samu muryarsa ta saisaitu.

    “Kiyi haƙuri Maah zanzo ALLAH amma sai gobe idan ALLAH ya kaimu. Inaga ma anan zamu yi hutun nan na kwana huɗu yanzu kaina na ciwo”.

   Abinda ta faɗa ya sashi sake marairaicewa kamar yana gabanta. “Please maah i promise you bazan saɓa alƙawari ba”.

   “Okay thanks you dear Mammah I love you”.

Wannan kalma ta Ramadhan ta bala’in faranta ran Gimbiya Su’adah. Sai taji gaba ɗaya fushin da takeyi da shi ya kwaranye a zuciyarta. Sai dai hakan baisa taji zata janye maganar auren Aina’u ba, tana akan bakanta duk da suna kan rikici da Pa ne akan hakan ma. Dan kuwa su Bappi sunce su babu ruwansu indai Ramadhan ya amince su masu son hakane ai.

    Mikewa yay yana kallon Raudha dake ƙudundune fuskarsa da murmushi. “Irin wannan nannaɗa haka Ustazah kamar wata shawarma?. Indai nine nayi nan ina jiran abinci da yunwa na dawo cikina kamar anmun sata”.

  Ya ƙare maganar da shafa cikin nasa daya ɗan taso. Shi kansa ya fahimci ya ƙara nauyi, kwana biyun nan baya iya fita training, dole ya dawo kar azo yakai matsayin da ƴar rigimarsa zata kasa ɗaukarsa wata ran. Da wannan tunanin ya fice ya barta bayan ya gwada yayeta ta sake saka masa kuka.

     Kallon-kallo Aina’u da Muneera kema juna ganin yanda Yayan nasu ya fito a ɗakin Raudha fuska ɗauke da ƙayataccen murmushi da sai dai su hanga yanama wani shi ko su Bappi. Wani irin zafine ya shiga ratsa zuciyar Aina da jin ƙara tsanar Raudha da duk wandama ke tare da ita. jitake zata iya kashe Raudha saboda Ramadhan a yanzu. Dan tun tana shakkar maganar auren nasu a yanzu abin ji take yana ƙara mata tasiri a rai da ɗokin kasancewarta matarsa kodan suma susha romon mulki, dan tasan dai ta auresa yanzu tabbas itace zata zama first lady bawai waccan kazamar yarinyar da ko tsarkin kashi batajin ta gama ƙwarewar yi. Momynta (Adda Asmah) ta gama tabbatar mata indai Ramadhan ne sai ya sota fiye da uwarsa ma a duniya da su Anne, dan zata mallake mata zuciyarsa yanda bazai sake tunawa da kallon wata mace da daraja a duniya ba sai ita. Tabbas tahau ta zauna. Ta kuma yarda. Dan ita shaidace Abbansu a tafin hanun Mom nasu yake. Sai abinda tace yake yi.

(Hummm????????????. ALLAH yasa sanda za’aima wasu hisabi muna aljannah a fadan MANZON ALLAH (S.A.W).

 ★★★

   Da ƙyar Raudha ta iya daurewa ranta ta tashi. Sai dai gaba ɗaya a tsorace take da komai ma. Yau gaba ɗaya Ramadhan ya rikita mata lissafi. Tama rasa wane kalar tunani zatai. Shiryawa tai cikin doguwar rigar abaya baƙa. Komai bata shafa ba sai khurah da turare. Sai dai ta wanko fuskarta saboda kukan datai. Cikin ɗar-ɗar da zuciyarta keyi ta fito domin sama masa abincin daya buƙata. Cikin sa’a ALLAH ya taimaketa tai kiciɓus da Bilkisu a kitchen ɗin sama. Dan ƙamshin da taji da motsine ma yaja hankalinta tunda tasan bamai shiga inba itaba sai mama ladi dake gyarawa.

   Ido taɗan waro kaɗan na mamaki. “La aunty Bilkisu..”

   Bilkisu dake murmushi tai saurin cewa “Kamar kice komai. Kawai naga Yaya a bazatane shiyyasa na rugo kitchen ɗin tunda ba salla zanyi ba. Mun shagala kwata-kwata bamu buɗe television ba balle muga batun dawowarsa.”

    Ajiyar zuciya Raudha ta sauke. Cikin danne abinda ke taso mata tace, “Wlhy nima nasha mamaki.”

   Ƴar dariya Bilkisu tai. “Uhm ya miki surprise na masoyane kawai”.

   Kunya zancen Bilkisu ya bama Raudah, ta kauda kai kawai tana murmushi. Hannu ta saka suka karasa aikin da aready dama Bilkisun tana gab da kammalawa. Sai da suna haɗa abincin a basket Bilkisu ke faɗin. “Niko idonki kamar wadda tai kuka”.

   Da sauri Raudha tace, “Abune ya faɗamin a ido daƙyar na samu ya fita bayan nata zuba masa ruwa”. 

  Sannu Bilkisun ta mata dan har zuciya ta yarda. Raudha ta ɗauka basket ɗin tana mata godiya da addu’ar ALLAH ya kaisu ran aurenta da yanzu haka ana shirin saka rana kusan su biyar.

     Da ƙyar ta iya kawo kanta ƙofar ɗakin nasa. Ji take kamar bazata iyaba amma ta daure matuƙa. knocking tayi kamar bataso. Tana shirin sake na biyu aka buɗe ƙofar. Bata yarda ta kallesa ba, dan tasan dai shine ɗin. Shiko idonsa a kanta ƙyam yana ƙaremata kallo yanda abayar tai matuƙar mata ƙyau. Matsawa yay ya bata hanya ta shige batare da yace komaiba. Sai da ta gittashi ta shiga ya maida ƙofar ya rufe. Saman kujerar daya tashi ya koma ya zauna tare da ɗaukar Tab.. Da ke a hanunsa kafin shigowarta. Ganin ya basar da ita ya sata daurewa tace, “Ga abincin”.

   “Zuba”

Ya faɗa a taƙaice batare da yabar abinda yakeyi ba. So yake yay dauriyar fasa abinda yay niyyar yi a gareta amma zuciyarsa taƙi amsar lallashin sam. Bai kalleta ba harta zuba masa gasashen naman ragon daketa ƙamshi, yaji haɗi na musamman. Sai kunun madara da Bilkisu tayisa a nutse saboda sanin yanda yake ƙaunarsa. Zata zuba abincin yay saurin dakatar da ita. “No bar nan kawai”.

  Dakatawa tai ta maida kwanon ta rufe da tura table ɗin gabansa yanda zai samu nutsuwar ci. Sai da ya ɓata wasu sakanni ya ajiye tab.. Ɗin, dai-dai da miƙewar Raudha dake fatan samun hanyar guduwa dan yau bazata juri zama da shi a inuwa ɗaya ba. Caraf ya riƙo hanunta ya zaunar a gefensa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button