BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

    Gabansa Raudha ta ƙaraso bayan ta ɗakko basket abincin data shirya masa tun ɗazun, komai a cooler yake dan haka bata tunanin sun huce. Table ɗin ta kalla inda ƙafarsace fara tas a miƙe, ganinta da abincin kuma baisa ya sauke ba. Kallonsa taɗan sata a ranta tana gulmarsa ganin yanda ya tsuke fuska tamkar bashi ya gama mata abun kunya ɗazun ba (Humm da gaske mutumin nan dai yanada aljanu). A fili kam sai cewa tai “Ga abincin”. 

   Banza yay mata kamar baiji ba. Ta sake maimaitawa cikin marairaice fuskarta dake cikin niƙab data sako. Ganin yaƙi nuna yasan da zamanta a wajen sai takai durƙushe a gabansa tana dire basket ɗin a ƙasa. “Dan ALLAH kayi haƙuri, wlhy tsoro naji ɗazu ɗin”.

   Nanma banza yay mata yana cigaba da sarrafa keyboard ɗin lap-top ɗinsa hankali kwance. Sai dai ya fahimci maganar tata nada alaƙa da tunanin gudun datai ɗazun ne.

    “Dan ALLAH!”.

Ta sake faɗa a hankali. Idanunsa da har yanzu jan yaƙi kwaranyewa a cikinsu ya ɗan rumtse, ga mura ga fitina da yaketa ƙoƙarin haɗiyewa taƙi hadiyuwa. Iska ya ɗan furzar dakai hanunsa saman goshi ya shafa, tunda tace ALLAH kuma ta gama da shi. Amma hakan bai hanashi yin magana a daƙile ba.

    “Dan kin rainani ni zakizoma da wannan abun a fuska?!”.

  (Oh ALLAH, dama akan niƙaff ne?) ta faɗa a zuciyarta tana lumshe ido. A fili kam hannayenta ta matse waje guda. Cikin sanyin muryarta dake tsumashi batun yau ba tace, “Dan ALLAH kayi haƙuri ALLAH kunyarka nakeji”.

     (Kunya) ya maimaita kalmar a ransa yana ɗan bubbuga yatsansa bisa lips ɗinsa idonsa a kanta. “Okay! Naji ciresa to, inba hakaba kuma ni bashi zan cire ba, wancan zan cire”.

    Kukane kawai ya ragema Raudha ta fashe da shi. Mutumin nan so yake kawai ya zautar da ita a gidan nan, dan sarai ta fahimci abinda yake nufin zai cire. Babu yanda ta iya dole takai hannu tana kwance niƙaff ɗin sai dai ta rumtse idanunta… Hararta yay ya ɗauke idanunsa dan ya tsani ganin hawayen nan.

    Jin bai tanka ba yasata satar kallonsa sai taga hankalinsa baya gareta. Saurin saka nikab ɗin tai ta goge hawayen. Kafin ta ɗaura basket ɗin saman table ɗin ganin ya sauke ƙafafun nasa. Abincin ta haɗa masa ranta cike da fatan ALLAH yasa ya barta ta koma ɗakinta. Sai dai addu’ar tata bata amsu ba. Dan bayan ya gama shan ƙamshinsa lap-top ɗin ya ajiye gefe tare da nuna mata gefensa fuska a tsuke.

    (Nidai tawa ta ƙare) ta ambata a ranta tana miƙewa tabi umarninsa dan har tafara jin nutsuwa ganin ɗan sake mata da yakeyi kwana biyun nan, sam bazataso su koma ƴar gidan jiya ba. Duk da 2seater ce sai da taɗan takura sakamakon yanayin nasa zaman. Lap-top ɗinsa ya ɗauka ya maida a cinya yana faɗin “Ohya bani, dan hukun cinki kenan yau a gidan nan ciyar dani abinci daga nan har dare”. Ya matso da fuskarsa gab da tata. Cikin raɗa ya ƙarasa faɗin, “Inba hakaba kuma na rantse ni zan c….”

   A zabure ta ɗaura hanunta saman bakinsa ta toshe, tsabar rikicewa harda tallafo ƙeyarsa da ɗayan hanunta”.

    “Ni dai gaskiya-gaskiya to nama fasa abotar a kwance wlhy”.

   Kaɗan ya rage dariya ta kufce masa. amma yay dauriyar dakewa yana bin fuskarta da idanun ke rumtse da bakinta dake maganar da kallo. Ga jikinta sai tsuma yake. Sosai yake jin nishaɗi idan ya ganta a yanayi na tsorata ko kunyarsa. Hanunsa yasa ya janye nata hanun daga bakinsa harda ɗan bugesa.

    “Ustazah yaushe kika koma hakane wai? To ai mai raba wannan abotar sai mutuwa mun ƙulla kenan”.

   “To an taɓa dole ne?”.

Ta faɗa cikin waro idanu tana sake ƙwaɓe fuska. Hancinta ya lakata kaɗan da ɗage gira sama ya kashe mata ido ɗaya. “Abota dani dolene yarinya. Dama kika samu na zaɓeki zakimin iyayi”. Yaƙare maganar da wani salon taɓe baki kamar wani mace. Hakan sai yay bala’in saka Raudha dariyar da batai niyya ba. Sosai murmushin fuskarsa ya ƙara faɗi shima. Sai dai tana gama dariyar ta ɗago da faɗin, “ALLAH yanda kayi sai kace mace. Baba Laran gidanmu haka take idan tana faɗa”.

   Fuska ya tsuke da kwaɓeta yana hararta. “Waye macen?”.

      Dariyar dake yalwace da fuskarta ta sake ƙyalƙyalewa da ita tana kai hannu ta danne bakin. Yayinda shi kuma ya kai hannu ya mangare mata kai ransa cikeda nishaɗi. Ganin taƙi daina dariyar ya sake bata ranƙwashi….

    “Wayyo Mommyna zai ɓararmin da karatu na”.

  (Kan uban nan) ya faɗa a ransa dariya na kufce masa shima. cak ta tsaya da tata dariyar ta zuba masa ido batare data sani ba. Dan wani irin ƙyau dariyar tai masa. haƙoransa duka sun bayyana ba kuma yana yinta a haukace bane…

   “Sharri kika koma kuma Ustazah?”. Ya faɗa da sake kai mata ranƙwashi yana dariyar har sannan sai ta duƙe kan nata ya sauka bisa cinyarsa hularta na zamewa ta faɗi ƙasa. Ƙoƙarin ɗagota ya shigayi amma taƙi yarda. cakulkulo ya fara mata a wuya, cusa kanta take sakeyi tana dariya da ƙoƙarin ture hanunsa. 

   Jinsa yake a wani irin nishaɗi daya jima baiyiba a rayuwarsa. Zai iya rantsuwa tun bayan rasuwar Haseenahr sa da Amnah bai sake farin ciki makamancin hakan ba da yake a kwanakin nan musamman yanzu. Yanda gashinta data ɗaure ke reto ya sashi kama ribbon ɗin ya zare gashin ya tarwatse. Da sauri Raudha ta ɗago dan batama san hulan ya zame kansa ba. Sai kuma kunya ta kamata jin ya tura yatsunsa a ciki. Tai ƙoƙarin matsawa ya riƙeta. Shiru tai tsigar jikinta na tashi, kamar yanda shima yakejin jininsa na haurawa da gudu a kowanne jijiyar jikinsa….

    “Ina son gashin nan sosai”.

Yay maganar yana matso da kansa a kafaɗarta da kamo gashin ya kai hancinsa yana shaƙar ƙamshin haɗaɗɗen turaren YERWA INCENSE AND MORE… da yakeyi. Sai kuma ya saka maida yatsun nasa cikin gashin ya tallafo kanta ya ɗaura goshinsa akan nata suna musayar shaƙa da fesawa juna numfashi… Murya a matuƙar shaƙe duk da akwai mura dama tattare da shi ya ce, “Ƙawata!”.

    A yanda ya ambaci kalmar ba ƙaramin tada tsigar jikin Raudha yay ba. Da ƙyar ta iya faɗin. “Uhhyim”.

   “ALLAH yay miki albarka”.

Sosai taji daɗin wannan addu’a tashi da batasan dalilin yinta ba. Muryarta a raunane tace “Amin nagode”.

   Kansa ya ɗan jinjina mata da cigaba da motsa yatsun hanunsa cikin gashin nata. “Ni kuma fa?”.

    “Kaima ALLAH yay maka rahama da rahamarsa. Ya kareka da kariyarsa. Ya baka ikon sauke hakkin ƴan ƙasa dake bisa wuyanka, ya baka nutsuwar ayyuka da har abada da baza’a manta da kai ba. Ya hanaka cin hakkin kowa koda bai kai girman ƙwayar gero ba”.

    (Ya ALLAH yarinyar nan zata hakalani) ya faɗa a ransa yana mai rungumeta tsam a jikinsa. Wannan shine karo na uku da hakan ta faru tsakaninsu. Amma yau an samu cigaba dan itama tayi luf duk da jikin nata naɗan tsuma kaɗan-kaɗan.

   “Insha ALLAH ke ƴar aljanna ce AMEENATU!”. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button