BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

   Babu abinda ke fita a bakin Raudha sai kalmar innalillahi…. Har ƙarshe, ga hawayenta na zarya a kan ƙirjinsa. Murmushi ya saki da sake yamutsa gashin nata da yakeji kamar su yini yana wasa da shi. Cikin wata irin shaƙaƙƙiyar murya da bata taɓa cin karon ji da ga garesa ba ya fara magana…

     “Ustaza wannan ba mafita bace, idan kika bari naje matakin ƙarshe sam bazan saurarekiba sai na tabbatar da sadakina bisa kanki yanzun nan harda ribar baby insha ALLAH..”

    Baima kai ƙarshe ba tai saurin sakinsa da son tureshi, sai dai hakan bamai yuwuwa ba, dan duk da halin da yake ciki ai goma tafi biyar albarka. Yanda tai ɗin ya bashi dariya, sai dai halin da yake ciki bana dariyar bane, yayi imani kuma da inhar aka cigaba da kasancewa a haka babu makawa a yanzun nan bazai iya ƙyale yarinyarnan ba, duk da ƙoƙarinsa na son yin hakan. Kaɗan ya matsa ta samu hanya, ai da gudunta ta fita har tana bigewa da ƙofa…. Shima zaune ya kai jagwab saman stool ɗin mirror bayan ya ɗauke book ɗinta dake a wajen. Ya dafe kansa zuciyarsa na matuƙar gudu kamar zata fito… (Mike damunka Ramadhan? Mikaje ka takaloma kanka wajen shegen tsokale-tsokalen neman ayi?) a zuciyarsa yake maganar, sai dai sam babu nadamar abinda yay tattare da shi. Sai ma a fili daya furta ‘Oh Ramadhan ka lalace, da sa’ar autarku kake wannan abun ko kunya babu.’

    Sai kuma murmushi ya suɓuce masa, ya kai hannu a wuyansa, “Ni Ramadhana zazzaɓin ma ya dawo” yay maganar a marairaice yana wani langaɓe kai gefe cike da tausayin kansa…. Tuna abinda ya gani ya sashi saurin juyawa ga mirror ɗin, book ɗinta ya ɗauka ya buɗe, sai kuma ya miƙe yana bin rubutun da kallo. “Kai ina..” ya faɗa a fili yana girgiza kansa da miƙewa riƙe da littafin. Bakin gado ya koma, ya ɗauka ɗaya daga cikin wayoyinsa yay snapping rubutun, littafin ya ajiye ya cigaba da danne-dannensa. Tsahon mintuna biyu ya kai wayar kunensa.

     Daga can cikin tsokana Bappi yace, “Ɗan gatan ALLAH ka warke kenan?”.

   Murmushi yay yana sake ƙoƙarin control ɗin halin da yake ciki. “Oh Bappi nida nake kwance cikin ciwo kake kira ɗan gata?”.

     Dariya Bappi ya karayi daga can. “Ɗan gatane mana tunda ciwon naka na ƴan gatane. Bakaji bahaushe yace mura ciwon ɗan gata ba”.

     Dariya sosai shima Ramadhan ya sanya a wannan gaɓar Bappin na tayasa. Sai da suka nutsu Ramadhan ya fara magana serious. “Bappi wani abune ya ɗan rikitani yanzun nan. Amma na turo maka saƙo ta email ka duba yanzu dan mu tabbatar”.

    Bappi ma daya koma serious ɗin yace, “To ALLAH yasa dai lafiya?”.

     “Lafiya lau Bappi duba dai”.

     Bayan kamar mintuna uku sai ga kiran Bappi ya shigo, lokacin yana ƙoƙarin saka kaya a jikinsa. Dakatawa yay ya ɗaga wayar. “Ramadhan ina ka samu wannan hand writing ɗin?”.

    “Iri ɗaya ne ko bappi?”.

Ramadhan ya amsa tambaya da tambaya. Daga can Bappi yace, “Tabbas babu wani babbanci, kenan wanda ya turo takardar nan kamar yanda mukai hasashe yanada kusanci damu?”.

    “Bappi kasan rubutun waye kuwa?”.

   “Shi na ƙagu naji Ramadhan ”.

“Ameenatu!”.

  “Aminatu? Kana nufin Aminatu dai matarka?!”.

    “Ita kuwa Bappi. Yanzu naci karo da shi a book ɗinta na makaranta, shiyyasa gaba ɗaya kaina ya kasa ɗauka nima dan na shiga ruɗani”.

   “Uhhm to kaga wannan maganar bata nan bace ba, idan ka fita office gobe idan ALLAH ya kaimu zanzo kawai”.

    “Bappi na sameka a gida mana anjima”.

  “No Ramadhan akwai haɗari. Satar fitarka tayi yawa, ina tsoron magauta su fara fahimta su cutar da kai ta wannan hanyar. Dolene ka canja takunka”.

  Fuska ya ɓata, dan gaskiya akace bazai dinga zuwa gidansu akai-akaiba an cutar da shi. Wannan takura har ina dan ALLAH.

     ★Hajjaju Raudha kam tunda ta fice tana can ɗaki duƙunƙune a bargo. Ji take kamar ta tona tsakkiyar gidan kawai ta shige ta huta. Bawai bata san minene aure ba, domin tanada zurfi a ilimin addininta, shiko musilinci ya fiddo mana komai dangane da aure cikin hikima da rahamar UBANGIJI. Matsalar kawai shine komai yana zuwa mata baƙo ne. Bata saba ba, bata taɓa gani anayi ba. Bata karatun littafi sai ranar da Bilkisu ta bata, ko karatun tanayine cike da kunyar wasu wajajen idan tazo a lokacin. Gidansu na hutawa ko tv babu, wama yake da lokacin zaman kallo, yo fitinar Abbansu ma tasa idan rashin kuɗi ya ciyosa ya kwashe ya siyar kona wacece a gidan babu ubanda ya isa yace wani abu kuma. Bata da tarkacen ƙawaye, idan ma kika kasance mai rawar kai a aji bata shiga harkarki, sannan bata zaman fira in group daga boko har islamiyya, hasalima faɗa takema su Safara’u idan taga sunayi. Tasan dole ne ta shiga ruɗani da sabon yanayin da Ramadhan ke son jefasu a tsakanin nan. A wani bangaren kuma tanada gaskiyarta akan shiga ruɗani. Tun farko ta sakama ranta Ramadhan yafi ƙarfinta. Shima kansa ya tabbatar mata yafi ƙarfin nata. Mahaifiyarsa da danginsa harma da mutanen duniya sun tabbatar. A baya babu abinda take gani a cikin idanunsa sai saɓanin abinda take gani a yanzun, duk da dai harga ALLAH tasan bai taɓa muzantata da baki ba, bai taɓa hantararta ko wulaƙantata ba, kawai dai baya shiga sabgarta. Dolene canjawarsa a ƙanƙanin lokaci ta zama abu mai rikitarwa a gareta. Amma tayi alƙawarin hakan bazaisa ta taɓa saɓama umarni ko hani daga garesaba, zatai masa biyayya matsayinsa na miji inhar bai hau turbar sabama ALLAH ba. Zata yi biyayya ga umarnin UBANGIJI akan binyayya ga miji da dokokin aure kodan tabbatar da martabar tarbiyyarta data gidansu a idanunsa saɓanin wadda aka sanar masa da wadda duniya take kallon ahalinta dana iyayenta da shi……

   Ƙarar landline ɗin ɗakin ta katse mata tunaninta, gabanta ya faɗi. Sai dai tunanin ko Mama Ladi ne ya sata buɗe kanta a bargon ta ɗaga.

    “Ustazah! Haka aka koya muki kula da mijinne wai a islamiyyar?”.

    Batama san bakinta ya suɓuceba wajen faɗin, “Wlhy Yaya Ramadhan zaka kasheni da raina!”.

    Murmushi yay daga can, “Idan na kasheki Ustazah dawa zanyi angwancin?”.

    “Na shiga uku”.

Dariyar da batasan ya iyaba ya ƙyalƙyale da ita daga can. Tasa hannu ta rufe fuska tamkar tana gabansa. A zuciyarta ɗunbin mamaki da al’ajab ne danƙare. (Dama haka yake kokuwa yanzune ya canja…..?)

   “Ina jiranki kizo ki bani abinci kar yunwa ta hallakani ga ciwo”. Ya faɗa cikin katse mata tunani yana yanke wayar.

     Baki buɗe Ramadhan dake zaune cikin kujera ƙafa ɗaya kan ɗaya lap-top a cinyarsa alamar aiki yake ya saki yana kallon Raudha data shigo bayan tayi knocking ya bata izinin shigowa. (Lallai yarinyar nan kanta da motsi) ya ambata a ransa yana ɗauke idonsa gareta. Sanye yake cikin kaya masu taushi baƙaƙe. Duk da badan kwalliya ya saka ba sun masa ƙyau da sake fiddo hasken fatarsa. Idanunsa dake cike da abubuwa kashi-kashi ya janye yana maidawa ga aikin gabansa. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button