BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹????‍♀️⛹????‍♀️????

ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA????????????????????

1~ KUFAN WUTA????
Safiyya Huguma

1~ BAQAR INUWA????
Billyn Abdul

1~ RAYUWAR MACE????
Hafsat Rano

1~ MASARAUTA????
Miss Xoxo

1~ NOOR ALBI❤‍????
Mamuhgee

Guda 1????300
Guda 2????400
Guda 3????500
Guda 4????700
Guda 5????1k

ZAKU BIYA KUDINKU ANAN????????

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya????????

09032345899

KATIN MTN????????

09166221261


JAMA’AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan????????

Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F

ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA????????

+227 95 16 61 77

TEAM ZAFAFABIYAR????????????????


BAƘAR INUWA…????????

Da ɗumi-ɗuminsa????????????????????????????????

Please
Follow me
Share
Comments akan abinda ya shige maka duhu.

     _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar????????????????????????_

YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za’a cike Form ɗin kamar haka: –

Enter your name: (Cikakken sunanki)

Enter your mail: (Email ɗinki)

Enter an username (Sunanki)

Enter your password: ( misali 12341234)

Confirm password: (misali 12341234)

Sai a taɓa Sign Up shikenan an buɗe account a ArewaBooks????????????.

Continue with Google – Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za’a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

Register – Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.

AREWABOOKS LINK kai tsaye

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3

Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com

Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App… Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine.

MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER

+234 903 177 4742

Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan????????????????????????.

ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????
Typing????

Episode 58

……….A hankali ta saki numfashi tare da nannauyar ajiyar zuciya ganin Bilkisu ce ba wanda take fargabar haɗuwar da shi ba ko’a hanya bare a cikin ɗaki da ga ita sai shi. Zama Bilkisu tai kusa da ita tana kai hannu a goshinta. “Aunty Lafiya kuwa kika dawo da w….”
     Maganar tata ta maƙale jin jikin Raudha da zafi. “Ya salam baki da lafiya yauma ko? Dan ALLAH ki yarda muje ko cikin clinic ɗin gidan nanne inma bazamu je wajan Mommyn Jabeer ɗin ba. Aunty wai zaki cigaba da cutar da kankine akan Yaya Ramadhan ne? Kin hana na faɗama kosu Anne halin da kuke ciki, ni kaina ɓoyemin abubuwa da yawa kikeyi wlhy. Harga ALLAH nidai na gaji da shurun nan da kika dabaibayeni da haɗani da ALLAH akan nayi”.
       Murmushi Raudha tayi tana haɗiye hawayen dake son zubo mata. Ta tashi zaune cike da ƙarfin hali ta kamo hanun Bilkisu cikin nata. “Aunty B kiyi haƙuri dan ALLAH, ban hanaki gayama su Anne bane sai dan yanda kike kallon matsalar ba haka take ba. Aiki ne kawai yay masa yawa, sannan ni babu wani abu na rashin daɗi dake tsakanina da shi, kawai dan ba zaman gidan yake kamar da ba saboda ayyuka yasa kike ganin akwai matsalane. Kinga babu dalilin kai ƙara akan laifin da babu shi aunty. Nasan kina ganin kamar auren nan nasane cutarwa a gareni shiyyasa. Dan ALLAH kibar damuwa ALLAH ni banajin komai akan hakan duk da nasan dole ne naji kishi matsayina na matarsa. Amma karki manta Aunty ALLAH ya bashi damar yayi huɗu, a addinance ma da biyu aka fara, sannan uku, sannan huɗu. Sannan a yanayin da Ya Ramadhan ke ciki dama ya kamata ace yanada mace mai ilimi da zata jagoranci wasu abubuwa na mulkinsa bawai irina da iyakata secondary ba kuma mai ƙarancin shekaru. Karki manta aunty yanzufa nake shekara ta shatara kawai a duniya, koba komai kuwa Aynah nada kusan ashirin da tara ko talatin da ɗaya ko fin hakan ma, sannan tayi ilimi mai zurfi daga ƙasar NAYA har wajenta. Tako ina ta cancanci zama matarsa koda nauyin al’umma dake a kansa”.
      “Humm Raudha sam ban gamsu da wannan bayanin naki ba. Babu ruwan hankali da ƙarancin shekaru, hakama babu ruwan sanin yakamata da ilimi. Mutane nawane a zamanin da basuyi ilimin boko ba amma sunada basirar tsara abinda ko professor na yanzu bai iya tsarawa ba. Kai har a wannan zamanin akwai wanda basuyi ilimin boko ba amma wlhy idan sukai miki wani abun sai kinsha mamaki. Hakama shekaru, shekaru baga kowa suke taka rawar hankali ba ga mai su. Zakiga mutum da shekarun manya amma idan yana tafka miki baranɓarama ke kyace ɗan goma sha ne. Kuma kiga karamin yaro na gyara masa. So ni a tawa mahangar banga ta inda Aynah zata taimaki Brother ba wlhy. Ƴar uwatace ita kuma jinina, amma bazan ɓoye miki cewar inaji a raina akwai manufa acinkin wannan al’amarin ba Raudha. kuma insha ALLAH bazan gajiyaba wajen ganin na daƙile hakan sai dai in ƙaddararsa ce zama da ita”.
   Tana gama faɗa ta mike ta fita hawaye na sakko mata a fuska. Da kallo kawai Raudha ta bita sai itama ta fashe da kuka. Sai da tayi mai isarta sannan ta mike ta shiga toilet ta wanko fuskarta….

(ALLAH ka bamu ikon cinye jarabawa a duk yanda tazo mana????????????).

___

          A ɓangaren su Gimbiya Su’adah kuwa shirin biki suke na ƴaƴan gata, dan a wannan gaɓar ko auren Lubnah da Bilkisu bata bama muhimmanci ba kamar na Ramadhan da Ayna’u. Babu abinda zuciyarta ke raya mata sai cewar zata haɗa cikar birinta da maido ɗanta ƙarƙashin umarninta ta kuma rabashi da wadda ta zame mata ƙayar kifi a maƙoshi badan ta taɓa mata wani laifi ba ko kuskure.
      Hatta da Ramadhan yanzu wani gata take masa na fitar hankali ita da su fulani da uwar gayya Addah Asmah. Baya iya jera sati baizo gidan ba a sace. Takai yanzu ko sashen su Anne baya shiga sai dai suji labarin yazo a bakin Basma. Hatta yin waya ya rage dasu, komansa gimbiya Su’adah. Ko abu ya shige masa akan harkar mulki maimakon kiran Bappi da yakeyi ko Anne a da sai ya kira Gimbiya Su’adah yanzun. A mafi yawan lokuta shawarar tata bata haifar da ɗa mai ido a garesa. Dan kuwa dai gadarace kawai da son nuna isa take ɗorasa akai, ALLAH ne kawai ke taimakonsa da in yay maganar da Cos sai yay saurin faɗama Bappi shi kuma ya gyara, wani lokacin idan Bappi ya kirasa yace kar ai kaza ɗin nan kaza ya kamata ayi har haushi yakeji, ya dinga ƙunkuni kenan yana cika yana batsewar fushi. Idan kaga haƙoransa a waje yanzu to tare yake da su gimbiya Su’adah. Aynah kam kamar yanda bokan Adda Asmah ya faɗa mata a ɓoyeta kar Ramadhan ya ganta har sai an kaita gidan gwamnati haka akai, sai suka fake da cewar gyaran jiki ake mata, amma a zahiri umarnin boka suke bi, dan ya tabbatar musu inhar Ramadhan yay ido huɗu da Aynah kafin aure duk wani sihirin jikinsa sai ya warware.
    Game da Raudha kuwa a yanzu basu da lokacinta, dan su tunaninsu sun gama da shafinta lokacin komawarta gidansu kawai suke jira. Shiyyasa ko bibiyar lamarinta basa waniyi gaba ɗayansu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button