BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

     Kamar koda yaushe tunda suka zo garin yau ma ta buga uban tagumi bayan kammala aikin gidan da a yanzu ya zame musu tamkar wajibi ita da sauran ƴan uwanta. Sai dai halinsu na rashin son moriya kesa duka aikin ya dawo kanta sai abinda Yasmin taɗan iya tsakura a ciki ta rage mata. Duk da azumi ne haka take dagewa ta gyara komai tsaf, hakan ya saka gidan canjawa cikin ƙanƙanin lokaci, da'alama dama rashin zama a gyarashine ya sashi canja kamanni......
  “Raudha!”.

Asabe ta kirayi sunanta da ɗan ƙarfi a karo na biyu. Firgigit ta juyo ta kalleta dan sam bataji na farko ba.
Hannu Asabe ta shiga tafawa na taraddadi tana salati. “Oh ni Asabe Raudha wai mi kike son maida kanki ne? Duka shekarunki nawa da zaki jefa kanki cikin masifar tunane-tunane mike damunki?”.
“Mommy babu komai fa, kawai na zaunane naɗan huta Yasmin ta fito wanka nima na shiga”.
“Ƙarya kike Raudha, ki faɗamin gaskiyar abinda ke damunki tun kafin mu saɓa.”
Ajiyar zuciya Raudha taja da ɗan ƙarfi tana haɗiye ƙwallar data cika mata ido. Cikin yunƙurowar dukan damuwar dake akan ƙirjinta ta fara magana. “Mommy so nake na koma islamiyya, kinga dai rayuwa bazata tafi da ƙyau ba babu neman ilimi, tunda babu tabbacin samun cikar burin yin makarantar gaba da sakandire (secondary) inaga ya dace ace mun maida hankali akan na addinin matuƙa, a ƙalla dai mun mori wani yanki na arziƙin duniya dazai amfanar damu har a lahira. Amma idan na ɓata miki rai a zancena kiyi haƙuri”.
Sosai zuciyar Asabe ta karye da tausayin ɗiyar tata. Ta sani duk cikin ƴaƴanta babu mai nutsuwar Raudha. Yarinyace mai hankali da sanin yakamata. Ya rinyace abar alfaharin kowaɗanne irin iyaye. Sai dai yarinyace mai murɗaɗɗen hali da wuyar sha’ani. Ba komai take kallo dai-dai da ra’ayin mutane ba, ta rasa inda ta kwaso wannan bauɗaɗɗen halin nata da taurin zuciya. A ido zakai mata kallon mai sauƙin kai, amma sam ba haka baneba, wanda ya nutsu ga fahimtar halin Raudha ɗinne kawai zai gane ra’ayinta yasha banban dana mutane…….
“Mommy kiyi haƙuri..”
Sassanyar muryarta ta katse tunanin Asabe. Guntun murmushi ta saki tana kaiwa zaune kusa da ita, tare da kai hannu ta kamo nata. “Karki damu indai islamiyya ce zan sakaku Raudha, sai dai ki sani bazai zama dai-dai da yanda kike zuwa ta gida ba har sau sama da uku. Saboda kinga nan zaku ringa zuwa wajen aiki, kinga dai yanda sauran ƴan uwana ke tsaye bisa ƙafafunsu, babu wanda ke zaune yana dogaro da Gwaggo. Kowa neman na kansa yake yi ta yanda nima bazai yuwu na zauna na zuba ido Gwaggo ta cigaba da ɗawainiya damu ba”.
“Hakane Mommy, sai dai ina roƙon dan ALLAH komi zamuyi ya kasance bisa ƙyaƙyƙyawar hanyar da bazamuyi dana sani ba watarana mu da ke. Bazan ɓoye mikiba Mommy wlhy sam rayuwar gidan nan batamin daɗi, nafison hutawa….”
Harara Asabe ta dalla mata da ture hannayenta a cikin nata, rai ɓace tace, “Uban hutawa kikafi so mara mutunci, Raudha bar ganin ina lallashinki wlhy zan ɓata miki rai. Duk da buhun wulaƙanci da tozarci da ubanku yay min har kike iya kallon cikin idona kina faɗamin baƙya son nan kin fison Hutawa. To dan ALLAH ga hanya nan koma Hutawar mtsoww mara mutunci kawai”.
Hayaniyar Asabe ce ta fito da Hajiya Mama babbar yayar su Asaben da yau bata fita ko’ina ba tana gidan tana barci.
“Asabe lafiya? Wa kikema ihu haka?”.
“Wannan mara mutuncin yarinyar Raudha mana.”
Ta faɗa a hasale tana harar Raudhan datai ƙasa da kanta hawaye na gangaro mata bisa kumatu. Cikin ɓacin rai Asabe taima yayar tata bayani kamar ta rufe Raudha da duka dan taji zafin maganar datai sosai a ranta. Itama Hajiya Maman faɗa tahau Raudhan da shi sosai har tana mata gorin ubansu bai iya komaiba sai bin mata kamar tsohon bunsuru da busa sigari. Ba Raudha kaɗai ba, hatta su Fatisa wannan furuci na Hajiya Mama ya zafesu a rai matuƙa. Ana tsaka da wannan kicimilli ɗayar yayar Asaben da suke kira Aunty Hannah ta shigo gidan. Da alama fita tayi, dan sanye take da kaya na alfarma sai bula ƙamshi take. Babu yanda za’ai mai kallo yace daga wannan gidan ta fito duk da shima gidan nada ƙyau gwargwadon iko. Sai dai shigar tata tafi kama data hamshaƙan mata da duniya ke kan ganiyar ƙaunarsu da rungumarsu a jikinta. Ta ajiye key ɗin motar ta bisa centre table ɗin falon tana kaiwa zaune.
“Nikam lafiya kuka rufe yarinya ƙarama da ihu tamkar wasu kishiyoyinta?”.
Sanin halinta na rashin son ganin ana takurama yara Hajiya mama tai saurin faɗin, “Hannah bar wannan ba abar goyon baya baceba….” nan itama ta shiga zayyana mata abinda ya faru da Raudha ta faɗa harya fusatasu.
Saɓanin su ita murmushi tayi tana gyara zama saboda wani abu daya cuɗanya tunaninta da zancen Raudha ɗin cikin ƙanƙanin lokaci, har takai ƙwaƙwalwarta ta haska mata wani nasara a ƙananun daƙiƙu, dan yanzu haka daga government house take.
“Raudha badai islamiyya kike so ba? To zakije islamiyya”.
Ta faɗa murmushinta na sake faɗaɗa tare da shafa kan Raudha a hankali. Su Asabe na buɗe baki da nufin yin magana ta girgiza musu kanta tana miƙewa. Dukansu binta sukai da kallon mamaki harta shige cikin ɗakin barcinta. Bawai amsa buƙatar Raudha ɗin bane abin mamaki a wajensu, dan sun san itaɗin mace ce mai son yara sosai, sannan ma tun zuwan su Asabe gidan kowa ya fahimci irin son da take nunama Raudha, dan ko abu zata saka ai mata kafin ta saka su Fatisa ta saka Raudha, sannan har zama take suyi hira da Raudha ɗin. Abinda ya basu mamaki ta shigo a yanayin damuwa sosai, amma dagajin abinda suke ɗauka laifi ga Raudhan sai saɓanin hakan ya bayyana a fuskarta, dan a zahiri tamkar abinda Raudhan tayi ne ya warware dukan damuwar data shigo da shi cikin gidan………✍

Tofa minene a ran aunty Hannah da har yay dai-dai da burin Raudha kuma?????


ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA????????????????????

1~ KUFAN WUTA????
Safiyya Huguma

1~ BAQAR INUWA????
Billyn Abdul

1~ RAYUWAR MACE????
Hafsat Rano

1~ MASARAUTA????
Miss Xoxo

1~ NOOR ALBI❤‍????
Mamuhgee

Guda 1????300
Guda 2??400
Guda 3????500
Guda 4????700
Guda 5????1k

ZAKU BIYA KUDINKU ANAN????????

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya????????

09032345899

KATIN MTN????????

09166221261


JAMA’AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan????????

Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F

ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA????????

+227 95 16 61 77

TEAM ZAFAFABIYAR????????????????


BAƘAR INUWA…????????

https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09

Da ɗumi-ɗuminsa????????????????????????????????

Please
Follow me
Share
Comments akan abinda ya shige maka duhu.

     _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar????????????????????????_

YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za’a cike Form ɗin kamar haka: –

Enter your name: (Cikakken sunanki)

Enter your mail: (Email ɗinki)

Enter an username (Sunanki)

Enter your password: ( misali 12341234)

Confirm password: (misali 12341234)

Sai a taɓa Sign Up shikenan an buɗe account a ArewaBooks????????????.

Continue with Google – Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za’a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

Register – Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.

AREWABOOKS LINK kai tsaye

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3

Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com

Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App… Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine.

MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER

+234 903 177 4742

Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan????????????????????????.

ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????
Typing????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button