BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹????‍♀️⛹????‍♀️????

ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA????????????????????

1~ KUFAN WUTA????
Safiyya Huguma

1~ BAQAR INUWA????
Billyn Abdul

1~ RAYUWAR MACE????
Hafsat Rano

1~ MASARAUTA????
Miss Xoxo

1~ NOOR ALBI❤‍????
Mamuhgee

Guda 1????300
Guda 2????400
Guda 3????500
Guda 4????700
Guda 5????1k

ZAKU BIYA KUDINKU ANAN????????

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya????????

09032345899

KATIN MTN????????

09166221261


JAMA’AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan????????

Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F

ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA????????

+227 95 16 61 77

TEAM ZAFAFABIYAR????????????????


BAƘAR INUWA…????????

Da ɗumi-ɗuminsa????????????????????????????????

Please
Follow me
Share
Comments akan abinda ya shige maka duhu.

     _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar????????????????????????_

YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za’a cike Form ɗin kamar haka: –

Enter your name: (Cikakken sunanki)

Enter your mail: (Email ɗinki)

Enter an username (Sunanki)

Enter your password: ( misali 12341234)

Confirm password: (misali 12341234)

Sai a taɓa Sign Up shikenan an buɗe account a ArewaBooks????????????.

Continue with Google – Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za’a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

Register – Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.

AREWABOOKS LINK kai tsaye

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3

Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com

Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App… Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine.

MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER

+234 903 177 4742

Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan????????????????????????.

ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????
Typing????

Episode 59

………Bayan kwanaki biyar da wannan magana Bappi ya shirya da kansa yaje har masarautar Bina sukai magana da mai-martaba, sai dai bai sanar da shi ainahin dalilinsu game da sihiri dake tare da Ramadhan ba. Ya nuna masa suyi hakanne kodan gudun abinda zaije ya dawo ga mutanen ƙasa akan kallo da fasararar da zasuma al’amarin. Da yake mutum ne mai fahimta kuma yayi matukar yarda da Bappi a take ya amince ya kuma gamsu. Sai dai ya tsuke bakinsa ko fulani bai tunkara da zancen ba.

    Haka shirye-shirye ya cigaba da gudana har biki ya rage baifi saura kwanaki takwas ba. Su gimbiya Su’adah nata shirye-shiryen fara sanarwa a gidajen redio da television Pa ya dakatar. Cikin ɓacin rai ta nema dalili yace idan lokaci yayi zata sani ai. Acan bangaren mai-martaba ma ya dakatar da Fulani da Adda Asmah, dan koda mijinta ya tsawatar shi da yake ya zama mijin tace batajiba, saima tujara data zuba masa gwargwadon iyawa shiko ya sanarma mai-martaba da dama shine ya bashi umarnin shima.
     Wannan abu ya cuɗa musu zuciya. Babu kunya Gimbiya Su’adah harda kai karar Pa gaban su Bappi. Anne zatai magana Bappi ya girgiza mata kai, yace Gimbiya Su’adah taje zaiyo magana da Pa. Sai dai har yau da ya rage saura kwanaki biyar basuji komai daga bakin Bappin da suka san zai iya yiwa har mai-martaba magana ya janye sharaɗin daya sharɗanta akan duk wanda yay wani abu babu umarninsu a bakin auren Fulani ne. Tashin hankali kennan da ba’a saka masa rana. Domin kuwa wannan furuci na mai-martaba ya matuƙar birkita kowa a cikinsu har Ramadhan ɗin kansa da Gimbiya Su’adah ta kira a waya ta sanarma komai lokacin yana office. Da wannan ɓacin ran ya tabbatar mata zai shigo gidan da dare dama Bappi nata damunsa da son ganinsa ya sharesa.
       
     
       GOVERNMENT HOUSE..

Yau kam da wuri ya shigo gida saboda son zuwa Taura house da anyi magrib. Raudha najin shigowar motocinsa kuwa ta mike daga falo inda suke zaune suna tattauna tsare-tsaren bikin Bilkisu da ayanzu ta zame mata ƙawa dan dama bata da su sai school mate kuma ita iyakarta a gaisa babu aminiya. Saurin riƙota Bilkiau tai ta zaunar. “Ni banga amfanin wannan wasan ɓuyan da kike da shi ba, kiyi zamanki dan ALLAH karma ya samu kafar rainaki dan zai ƙara aure ko ya zata wani kishinsa kike ma”.
     Kamar Raudha zatai kuka sai dai komai batace ba ta koma ta zauna ɗin. A haka Ramadhan ya shigo ya samesu.
Akan Raudha ko ya fara sauke idanunsa, itama anyi sa’a kallon nasa take. Lokaci ɗaya zukatansu suka harba cikin bugu mai tsanani. Raudha da taga ya rame mata a ido sosai sai dai ya ƙara haske da ƙyau ta fara janye nata idanun fuskarta na nuna wani yanayi mai wajalar fassara. Shiko ido ya ɗan tsura mata tamkar mai nazari ko kuma yau ya fara ganinta. Sosai ya ga ta ƙara masa girma da cika. Dan duk da ciwo da take fama da shi a watan nan baki ɗaya saita kara buɗewa tai ƙiba da girma. Sannan komai nata ya ƙara girma ga haske tayi sosai mai tafe da wani sirrintaccen ƙyawu da duk hassadar mai hassada bai isa mata kallo guda ya ɗauke ido ba.
       Kansa ne yaji ya sara masa. Yay saurin janye idanun a kasalance, sai kuma yay ƙoƙarin barin wajen kamar da ƴar sassarfa dan ko gaisuwar da Bilkisu ke masa bai amsa ba. Ƙofar ya maida ya rufe tare da jingina a jikinta lokcin da ya iso bedroom ɗin nasa. Ya ja ajiyar zuciya da sauke nanauyan numfashi idanunsa har sun kaɗa sunyi jajur. Ya jima a wajen tsaye kafin yaja kafafunsa da ƙyar zuwa toilet, agogon kawai ya cire ya sakarma kansa shower. Sai da yay sharkaf daga shi har kayan dake jikinsa sannan ya ragesu yay wanka….

      Raudha da dama a cikin yanayi. dauriya take zaune a wajen ta miƙe da gudu tabar wajen hanunta toshe da bakinta. Da sauri Bilkisu ta bita har cikin toilet data shiga. Amai ta shiga kwarawa tamkar zata amayar da hanjin cikinta. Hankalin Bilkisu ya sake ɗagawa matuƙa ta riƙe Raudha. Sai da komai data ɗanci ya fita tas sannan aka samu lafiya. Bilkisu ta tamaka mata ta gyara jikinta da wajen suka fito tana jera mata sannu.
      Cikin sauke numfashi a wahale tana kaiwa kwance ta ce, “Kai aunty B ƙamshin turare nan na Yaya babu daɗi”.
       Sosai Bilkisu ta zaro idanu waje, sai kuma tace, “Kutt Aunty Raudha ƙamshin Boucheron ɗinne baida daɗi? Anya kuwa kin shaka dai-dai?”.
      “Ni wlhy lafiya lau na shaƙa, kuma dai tun yashe muke zaune a falon na ƙamshin komai bai dameni ba sai daya shigo ne ƙamshin turaren nan mai kama da ka…..”
     Da sauri Bilkisu ta ruƙe mata hannu tana dariya, “Uhmm to lallai Taura grandchild bai zo da wasa ba.”
    Sam Raudha ba wani fahimtarta tai ba. Bakuma tabuƙaci ba’asin mganar ba tama lumshe ido dan barci ke ɗan figarta ga kanta daya fara ciwo.

TAURA HOUSE

          Cikin matuƙar bayyanar tashin hankali Ramadhan ya ɗago yana duban Bappi da ya gama masa jawabi. A take idonsa ya rufe yama manta da wanda yake tare.
      “Gaskiya bazai yuwuba Bappi, duk ma wada yake tunanin sharɗanta hakan ya janye dan ba yarda zanyi ba.  Tayama kamar ni za’ace a ɗaura aurena a sirri sai kace wani funafunci? Na muku biyayya na amince da zabinku kukai yanda kuke so nima dole a barni nai yanda nake so akan nawa zaɓin. Sannan maganar events banajin akwai ɗaya da za’a janye a ciki, ba sai kun dinga nuna hassadarku da adawa aka dangin mahaifiyata zan san kun isa da ni b…..”
      Ji kake “tauuuu!!” Wani bazafaren mari ya sauka a saman kuncin Ramadhan har sai da ya kifa kamar zai faɗi. Pa da yake a fusace zai ƙara masa Bappi ya dakatar da shi. “No Basheer barsa barsa. Kai Ramadhan mu kake faɗama muna adawa da hassada da dangin uwarka!!”.
       Har yanzu hanunsa a saman kuncinsa dan da gaske marin yay matuƙar ratashi. Cikin ƙanƙanin lokaci ya sake birkicewa gaba ɗaya, idanunsa suka rufe ruf. “Idan ba hassada ba a gayamin mi kuke musu? Kun rabani da su komai sai ku, tun ina 2years a rabani da uwata tayi kawaici ta bar muku amma hakan baisa kunga haƙurinta da kawaicinta ba. To wlhy daga yau ku sani ta ƙare, idan kuma kunce a’a to muzuba mu gani!!”.
    Ya ƙare maganar cikin ƙaraji da nufar hanyar fita.
          Da sauri Pa ya miƙe cikin wani irin fushi yay kansa shima. Sai da Bappi yay azamar riƙo hanunsa yana girgiza masa kai. Duk yanda Pa yaso yin magana Bappi ya hana shi, ganin yanda jikinsama ke rawa sai kawai ya rungumesa yana shafa bayansa murmushi na subuce masa na tsantsar zafin da yakeji a ransa. Da wahala kaga fushin Bappi. Mutum ne mai yawan fara’a da dattako, akoda yaushe fuskarsa ɗauke take da murmushi. Duk abinda kaga faɗansa akai an ƙuresane.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button