BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

    Tafiya yake a hankali kamar baya so, saboda rashin ƙwarin jiki harya iso inda take, ya kai zaune a kujerar 3seater ɗin da take zaune sam bata fargaba. Sai da ya kai kwance ya ɗaura kansa bisa cinyarta tai saurin ɗagowa a zabure dan tsabar firgitar ganin kan mutum bisa cinyarta a baza .

    “Shut up!”.

Ya faɗa da yanayin tsawatarwa ganin zatai ihu sai dai muryar a ɗashe take fita da sanyi-sanyin dushewarta a dalilin mura da damuwa. Hannu Raudha tai saurin ɗaurawa a bakinta, sai kuma ta lumshe idanunta zuciyarta sai lugude take a ƙirjinta kamar zata faɗo. 

    “Sai shegen tsoro”.

Ya sake faɗa a hankali yana lumshe idanunsa da harɗe hannayensa a ƙirji ya miƙar da ƙafafunsa har bisa hannun kujerar da ƙyau. Raudha da sanin shi ɗinne baisa ta dai-daita ɗari bisa ɗari ba ta buɗe idanunta a hankali ta sauke bisa sumar kansa da ko ba’a faɗa ba kasan tana cin kuɗi kodan ƙyallin da takeyi duk da kasancewarta irin sumar baƙaƙen fata mai tauri da cika.

   Cinyarta ta ɗan motsa cikin ɓata fuska, a ganinta adalilin miye wannan taɓara da zaizo ya kwanta mata cinya babu gaira babu dalili. Motsa ƙafafun nata ya sashi buɗe idanunsa sai suka shige cikin nata da take hararar masa kai. Da sauri ta kauda kanta gefe da gyara yanayin fuskarta tace, “Ina yini”.

   Kamar koyaushe yanzun ma bai amsa ba, sai dai ya zare hanunsa guda daga saman ƙirji ya kamo haɓarta ya dawo da fuskarta yanda take. Cikin sake tsuke fuska ya ce, “Hararata kikeyi?”.

   Idanu Raudha ta ɗan zaro. “Ka rufamin asiri, ni yazanyi na hahareka?”.

   Kamar zaiyi magana sai kuma ya saki fuskar da maida hannayensa a ƙirji yana faɗin, “Inma kin hararenin ne iyakarki hararar, kuma duk matar dake harar mijinta dai kinsan aljanna sai dai ta gani dajin ƙamshi a maƙota”………✍

????????????????????Da alama dai shugaban ƙasa Ramadhan ya koma wa’azi????????????

End of book
Leave a comment

Post

Comments

nabsypurple90
Wannan shugaban kasa namu akwai rigima

21 minutes ago

5163177247118880
Nyc

2 hours ago

aeesha
Masha Allah muna godiya

2 hours ago

Contact Us
Arewa Books Publishers

WhatsApp: 09031774742

Email: arewabookspublishers@gmail.com

Navigation
Home
About
FAQ’s
Legal
Privacy Policy
Terms of Service
Social
Facebook
Instagram

Copyright 2021, Arewa Books | ALL RIGHTS RESERVED | Powered by thinkcrypt.io

Menu
Dashboard
My Library
Create Story
Home
About us
FAQ’s
Privacy Policy
Terms of service
Logout

BAKAR INUWA…!!
Chapter: 45

Share:

Report

BAKAR INUWA…!!
View: 115

Words: 2.5K

Chapter 45
45

………Yanda yay maganar kamar bashiba yasa Raudha ɗan taɓe baki da marairaice fuska. “Ni dai tunda banyi ba ai Alhmdllhi”.

   Bai tanka mata ba, sai dai ya sake buɗe idanu yana kallonta. Sosai zuciyarta ke gudu a ƙirjinta dan ta fahimci abinda yake kallon. (Oh ita Raudha taga takanta, mima ya kaita fitowa ba hijjab ko mayafi?) ta ayyana a zuciyarta a fili kamar zatai kuka.

    “35, 32, 38… Uhhm da alama zaki iya….” 

    Saurin buɗe ido tayi jin ta ɗan zama kanta na son ganin kuma mi yake ma lissafin numbers haka? Da cewa zata iya. Saurin son zame masa kai tayi a ƙafarta sai ya ɗan mintsini cinyarta. “Hi kokin manta sadaki na biya malama. Stay quite ko kiji a jikinki”.

     Daina motsa ƙafafun tayi, sai dai tasa hannu ta kare ƙirjinta tana tura baki dan ta fahimci lissafin seize ɗinta na ƙirji, ciki, hips yake yi. Ji take inama ƙasa ta tsage ta shige kawai ta huta dan kunya. Ita kam al’amarinsa yanzu ya daina bata mamaki sai dai tsoro. 

    Ganin yanda ta kare ƙirjin nata ya sashi ɗan yamutsa fuska da taɓe baki. “Yarinyar nan anya kuwa bazaki lalatani ba. To banda son lalatani inda na dosa daban inda kika dosa daban tabbacin abinda ke ranki kenan”.

       Ji Raudha tai mizai hana kawai ta saki kuka ta huta, kafin ta lalubo abinyi ya tashi zaune cike da ƙarfin hali yana gyara zamansa sosai a gefenta dab. Fuska a yamutse idonsa ƙyam a kanta yace, “Da alama yarinyar nan zaki tsufa da wuri, dan ƙiba zakiyi bata wasa ba mtsoww nidai an cucan..” ya ƙare maganar da ɗaukar kofin kunun da take sha. Zamansa ya gyara tamkar bashi ya gama zuba zancen ba ya kai kofin bakinsa bayan ya ƙarema abinda ke cikin kofin kallo ya fahimci kunun tsamiya ne da Anne nayi, kuma Alhmdllhi yana matuƙar son sa.

     Yunƙurawa Raudha tai zata tashi dan ya gama dabaibaiyeta a cikin cakwakiyar kunya ya dakatar da ita. “Amma gaskiya baki da tausayi Ameenatu! Haka akace ki kula da miji idan baida lafiya!?…”

   Yanda ya ƙarasa maganar da saki wata wahalalliyar atishawa da jin sunanta a bakinsa ya sakata dakatawa. Zuciyarta da ɗan fargaba ta dubesa dan tun dama yazo wajen ya fara magana da ɗumin dataji kamar a kansa daya ɗaura jikinta take tunanin yana lafiya kuwa? Sai dai tsokanar magana daya ɓige da mata yasata ture tunanin. Dubansa tai cikin ƙarfin hali, ganin yanda fuskarsa tai jaa musamman saman hancinsa, sai kuma idanunsa da ya buɗe suka haɗa ido suma sun sake koɗewa fiye da jiya alamar babu lafiya. Saurin kauda nata tayi tausayinsa na ɗarsuwa mata a rai, dan tun fil azal haka take da saurin jin tausayin mutum koda mugune (akwai lokacin da aka taɓa kama ɓarawo a makwaftansu, gashi dai itama haushinsa takeji saboda ya taɓa haurawa gidansu yay sata. Amma yanda aka dinga jibgarsa sai itama taita kuka tana roƙon a barsa ya tafi).

   A bazata taji ya damƙi hanunta ya kai saman goshinsa da ya ɗauka zafi sosai har tanajin harbawar jijiyoyin wajen. Cikin tsoro da tausayinsa da ya bayya a cikin idanunta ta buɗe baki zatai magana sai dai ya rigata. Cikin taushi da sanyin murya da batasan yanada su ba. “Ki bani abinci naci kiban magani”.

    Tausayinsa sosai ya sake kamata. Cikin damuwa da sake sanyaya muryarta itama mai sauƙin faɗi tace, “Murance har yanzun?”.

    Idanunsa daya ɗan maida ya lumshe ya sake buɗewa. Sai kuma ya kwanto kansa kan kafaɗarta yana faɗin, “Kin damu da nine balle ki sani? An baki amanata kin kasa riƙewa”. Nanma zafi taji jikinsa. Tai saurin rumtse idanu kunya na sake dabaibayeta da dariyar maganarsa (wai an bata amanarsa. Bama itace aka bashi amanarta ba) Tasan ya kamata tun a jiya data fahimci ya dawo da mura tabi shawarar Bilkisu na kai masa magani. Amma ganin kamar Bilkisu ta manta sai itama ta share batun dalilin abinda ya sake harmutsasu na faɗan ƙauyen Kauci. Dai-dai tana janye hanunta a goshinsa yace, “Kiramin Anne”.

      A sanyaye tace, “Amma za’a tayar mata da hankali ai”. 

   Komai bai ceba ya ɗaura hanunsa saman cinyarta idanunsa a lumshe ya hau laluben wayarta. Saurin riƙe masa hannu tai a ɗan firgice jin yanda yake lalubeta kamar da gayya. 

    “Ki daina fassarani da abinda bashi nake nufi ba, ni waya nake nema”.

    Duk da idonsa a rufe yay maganar hakan bai hana Raudha ƙyaɓe fuska ba da tsuke ta. Sai dai batace komai ba ta tura masa wayar ta dunguri hanunsa datai saurin saki a nata. Shima komai bai sake cewa ba ya ɗauka wayar ya ɗaura bisa hanunta. Murya babu wasa yace, 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button