BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ku kasance da ZAFAFA BIYAR domin karanta daɗaɗan labaransu guda biyar dake tafe da salo na musamman masu ƙayatarwa.

https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09

Da ɗumi-ɗuminsa????????????????????????????????

Please
Follow me
Share
Comments akan abinda ya shige maka duhu.

ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA????????????????????

1~ KUFAN WUTA????
Safiyya Huguma

1~ BAQAR INUWA????
Billyn Abdul

1~ RAYUWAR MACE????
Hafsat Rano

1~ MASARAUTA????
Miss Xoxo

1~ NOOR ALBI❤‍????
Mamuhgee

Guda 1????300
Guda 2????400
Guda 3????500
Guda 4????700
Guda 5????1k

ZAKU BIYA KUDINKU ANAN????????

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya????????

09032345899

KATIN MTN????????

09166221261


JAMA’AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan????????

Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F

ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA????????

+227 95 16 61 77

TEAM ZAFAFABIYAR????????????????


BAƘAR INUWA…????????

https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09
     _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar????????????????????????_

YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za’a cike Form ɗin kamar haka: –

Enter your name: (Cikakken sunanki)

Enter your mail: (Email ɗinki)

Enter an username (Sunanki)

Enter your password: ( misali 12341234)

Confirm password: (misali 12341234)

Sai a taɓa Sign Up shikenan an buɗe account a ArewaBooks????????????.

Continue with Google – Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za’a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

Register – Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.

AREWABOOKS LINK kai tsaye

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3

Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com

Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App… Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine.

MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER

+234 903 177 4742

Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan????????????????????????.

ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????
Typing????

________

ZAFAFA 5 NA MIKA GAISUWAR TA’AZIYYA ZUWA GA MARUBUCIYA UMMY AISHA, TA KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION, BISA GA RASHI NA MAHAIFIYAR TA DA TAYI. MUNA FATAN ALLAH YA JIKANTA DA RAHAMA, YA GAFARTA MATA, YA K’ARA MANA HAKURIN WANNAN BABBAN RASHI DA MA NA IYAYENMU BAKI ƊAYA (AMIN????????????).

_________

Huuuuuum! Idan kaji hanci a sama yayin gittawar mata ƴan ƙwalisa ko shiga gidajensu kasan maganar ta ƙamshi ce

Ina magana ne aka kayan ƙamshi ƴan gaske ba saka iska ta hure maka ba

Ina mata ƴan ƙwalisa ma’abota so da ƙaunar ingantattun haɗin turaruka ƴan gaske? To kuzo maza ga dama a tafin hanunku cikin sauƙi da sauƙaƙawa.

Ana siyarda Turarukan Wuta na yan Maiduguri Set na amare. Ana bada sari kuma.

Sannan akwai kayan gyaran jiki. Akwai zumar qiba result cikin 1 week. Turaren daki, jiki, kaya, tsuguno, humra, colacca, turaren wanka, mopping scents, air freshener.

Address Kano, Mariri Maiduguri Road. WhatsApp number 07068145252.

Sai kunzo????????

____________
Episode 6

………..Da ga Asabe har ƴaƴanta hankalinsu a matuƙar tashe yake. Hakama Baba Nafi, duk da Asabe kishiyace a gareta aurota da akai a gidan ba ƙaramin alkairi ya zame musu ba ta wani ɓangaren. Dan koba komai Asabe kansaka Malam ɗan-azumi ya sauke haƙƙoƙin su dake kansa koda baiyi niyyar hakan ba. Dan kafin ya aurota sai ya gadama yakeyi, ya gwammaci yaje yay caca ko neman mata. Sannan duk jarabarnan tata da wahala kaga tana faɗa da kishiya, wani lokacin Larai kanso suyi, amma Asabe sai taƙi kulata. Mal. Dan-azumin ne dai ita da shi kamar suna kallon hanjin juna. Hatta da sauran yaran gidan duk sun zama sukuku, musamman ma da Inna mahaifiyar malam Dauda ɗin tazo ta sake zazzaga tata masifar ga Asabe saboda Larai taje ta sanar mata ƙarya da gaskiya, duk da kuwa ba ƙaunar laran take ba. Babu wanda ya tanka mata sai larain, dan harda kawoma Innar ruwa saboda tsugudidi. Saida ta gama zazzage masifarta tsaf da gorin Asabe tabar mata gidan ɗanta sannan tabar gidan, Asabe dai na ɗaki ita da yaranta duka cikin matsananciyar damuwa. Dan har Inna tayi ta gama babu wanda ya leƙo.
Gaba ɗaya wannan yini dai anyisa a gidan cikin rashin daɗin rai ga azumi. Idan ka cire Larai dakejin tamkar ta ciji sama dan farin ciki. Malam Dauda bai sake dawowa gidan ba sai dare bayan sallar isha’i. Tsabar jinsa yau a sama da sigari ya shigo gidan yana busawa, wayarsa mai shegen ƙara tana raira waƙar (marigayi Ali makaho)
Galala Baba Nafi tai tana kallonsa, dan duk iskancinsa bai taɓa shigowa gidansa yana shan sigari ba tunma yanaji da ƙuruciya a iskancin. Amma abin mamaki sai gashi a yau cikin watan azumin ramadana, a kwanakin goman ƙarshe da kowa ke dagewa da ibadar ALLAH, ya shigo gidansa dake cike da ƴaƴa a wannan yanayi.
Tsakar gida ya zauna akan rijiyarsu yana kaɗa ƙafa da kai yana zuƙar sigari da ƙwala kiran sunan Asabe tamkar zai tsaga bangon gidan. Ko tari bataiba ballantana ƴaƴanta, jin taƙi tankawar ya sakashi fara zazzaga ruwan masifa da jaddada mata ta bar masa gidansa safiyar gobe idan ALLAH ya kaimu baisan sake ganinta. Kuma ko Yasmin bai yarda ta ɗauka ba idan zata wuce, ta bar masa abarsa.
Nan ma ko tari babu wanda yayi sai Larai data fito daga ɗakinta ɗauke da tire ta jero kwanika. Dan duk da bai bada kuɗin cefane ba, ba kuma aikinta ba yau kuɗinta ta saka tai girki iya ita da ƴaƴanta da shi. Wani irin washe baki yayi yana gyara zama a lokacin data kai tsugunne gabansa tana dire tray ɗin.
“A’a! Larai na mina samu haka ne?”.
Cikin jin daɗin sunan daya kirata da shi ta buɗe tsohuwar kular dake sama, wadda ke cike da taliya da miyar kifi, sai kunun tsamiya a kofi da ƙosai data sayo masa a ƙaramin kwano. Albarka ya shiga kwarara mata da gyara zama ko kunya babu da tunanin bashi yay cefanen ba. Baba Nafi kuwa dake kallonsu tuni zuciyarta ta harba. Dan zuwa yanzu ta fara zargin Larai akan wannan fitinar dake faruwa tsakanin mijin nasu da Asabe. Dan lallai akwai wani abu a ƙasa gaskiya.
Cikin farin ciki Malam Dauda ya kwashi girki yana kwararama Larai kirari tamkar wani jikan maroƙa. Itako sai wangale baki take.

★★★

 Washe gari sabuwar fitina ta sake tashi tsakanin Asabe da malam ɗan-azumi. Dan ya tabbatar mata sai ta bar masa gida a yau. Kuma bazata tafi masa da yaransa ko'ina ba. Ta bashi haƙuri sosai tana kuka amma yaƙi saurarenta, saima yi yake tamkar tana zugashi. Dan gaba ɗaya ya sake birkicewa, har mamakinsa mutane keyi musamman yanda aka san yana bala'in son Asabe, ba kuma yaune karon farko da suke irin wannan fitinarba a cikin anguwar, harma wadda tafi haka sunayi kuma su shirya. Ana tsaka da hakan kuma sai ga Inna yau ma. Komai sake rincaɓewa yayi har maƙwafta da suka taru domin bashi haƙuri akan ya maida Asabe kodan ƴaƴansa sai da ta shafesu. Dan Inna tas ta zagesu ta sake saka malam ɗan-azumi ƙarama Asaben saki ɗaya daya saura a tsakaninsu wanda ya mantama yayisa tun shekarun baya.
  Wannan abu yayima su Fatisa zafi matuƙa. Dan haka suka shiga haɗa kayansu masu muhimmanci dana mahaifiyarsu. Cikin ɓacin rai Fatima taje ta jawo hannun Raudha da Asabe dake gurfane suna basa haƙuri, dan itama Asaben ta zama tamkar ba itaba yau duk masifarnan babu ita. 
  “Mommy dan girman ALLAH in har ba Abbanmu ne autan maza ba a duniya ki barsa kizo mu wuce tunda kema kina da dangi ba'a bola ya tsintoki ba, dan ALLAH idan ya tashi ya auri Innar dake zugashi ɗin...”
  “K! fitsararriya!!”.

Inna ta faɗa a tsawace. Ko kallonta Fatima batayiba taja hannun Raudha da Asabe suka nufi ɗaki.

  Abinda Fatiman tayi ya sake hargitse gidan, Malam Dan-azumi da kansa ya shiga har cikin ɗaki ya fisgo Asabe ya kaita har ƙofar gida yana faɗin tabar masa gidansa, baya son ganinta ya tsaneta. Cikar da ƙofar gidan ta sakeyi ne yasa harsu Raudha suka fito da kaya malam Dan-azumi da Inna basu lura ba. Hakama Baba Nafi. Larai kuwa sarai ta gansu dan tana gefe tanata kwasar dariyarta.
  Mota ƙarama suka fara samu da zata kaisu har jihar Bina shata, kafin wata makwafciyarsu da suke ƙawance da Asaben taje ta kamo hannunta ta kawota har wajen motar, dan itace ta hana su Fatisa komawa wajen gudun kar Malam Dan-azumi ya gansu ya hanasu bin Asaben. Itako bata fatan Asabe ta tafi tabar ƴaƴanta, gara duk rintsi ta tafi da abinta kafin abun yay sauƙi, dan da gani kasan malam dauda baya cikin hankalinsa sam. Tafiyar Asabe yasa akaɗan samu sauƙin hayaniyar. Sai mutane daketa yima Malam Dan-azumi ɗin ALLAH wadai da koran Asaben da yayi batare da wani ƙwaƙwƙwaran laifi ba, dan koda aka tambayesa ya rasa mi zaice tayi masa sai babbotan borin kunya yakeyi shida Inna da dama kowa yasan batan ƙaunar Asabe dama duk surukan nata sai baba nafi kawai, ita kanta wani lokacin baba Nafin baji da dadi take hannun innar ba. Na Larai da Asabe yafi zafi ne kawai dai dan ta kasa tanƙwara Malam Dauda ɗinne ya sakesu dole ta haƙura. Yanzu ko data samu dama shiyyasa tai tsayuwar daka wajen ganin ƙarshen Asaben da take kallo matsayin wani miki ga ɗan nata....


   ★A Bina su Asabe suka yada zango gidan yayarta Halima da take aure anan. Sai dai kuma sunyi rashin sa'a bata nan wai tana jihar Loss kusan wata guda kenan ita da ƴaƴanta duka da mijinta. Sam Asabe bataso haka ba. Dan bata buƙatar zuwa babban birinin ƙasar Bingo dasu Fatisa wajen Gwaggo (Mahaifiyarsu hajiyar birni). Saboda ta tabbata idon hajiyar birni idon su Raudha to akwai matsala.
  Cikin damuwa da sanyin murya Raudha ta kalli Asabe da sauran ƴan uwanta da duk suka jigata saboda azumi, ita kanta daba azumin takeba a jigace take dan babu abinda taci tun jiya da rana sai ruwa. Hawayen dake a idanunta ta share da faɗin, “Mommy nikam a ganina mizai hana mu wuce Bingo wajen su Gwaggo direct mana. Babu amfanin wani raɓe-raɓe a gareki damu a yanzu. Na tabbata Gwaggo ta canja zuwa yanzu, sannan zata amsheki hannu biyu tunda daman zamanki da Abbanmu ne bata so.”
   Shiru asabe batace komaiba. Tasan maganar Raudha gaskiyane, sai dai tana fargabar zuwa dasu Bingo su lalace kuma. Su Fatisa basa jin magana tabbas, amma rashin jinsu bai kai inda masu karatu ke hasashe ba, sai dai ta tabbatar kusantasu da hajiyar birni a yanzu komai zai iya faruwa, saboda masifar son kuɗinta. Suma ƴaƴanta ta ɗorasu a hanyar banza dan kawai ta samu kuɗi, balle su kuma jikoki gasu kuma yaranta dukansu masha ALLAH, ba duk namiji zai kalla ya iya kauda kai ba......
  “Mommy gaskiyafa Raudha ta faɗa wlhy, gara kawai mu tafi Bingo ɗin”.
Fatima ta faɗa cikin katse tunanin Asabe. 
  Numfashi asaben taja mai nauyi, “Banƙi ta taku ba, sai dai nima akwai abinda nake lissafawa. Amma kuma banida wata mafita saita tafiya Bingo ɗin a yanzu. Matsalar kawai dai itace bamu da isassun kuɗin motar da zasu kaimu ne mu duka”.
    “Akwai kuɗi Mommy”.

A tare duk suka dubi Raudha datai maganar cikin mamaki. Cikin rashin damuwa da kallon da suke matan ta zaro kuɗi a cikin zani sabbi ƙal ƴan ɗari biyu ta miƙama Asabe. “Mommy jiya mutumin nan da yazo dubani a asibiti ya bani su. Nayi niyyar bakine dama idan munzo gida danki fara sana’a. Amma yanzu na tabbatar insha ALLAH zasu kaimu duk inda zamuje ko?”.
Hawaye ne suka ciko idon asabe. Dan bata taɓa tunanin Raudha haka ba. Ganin yanda take musu nuni dasu gyara yasa take tunanin sam Raudha bata ƙaunarta matsayin mahaifiya. Ashe ba haka bane ba. “ALLAH yayi muku albarka, ya kare min ku”.
Ta faɗa gawaye na silalo mata na nadamar sakaci da tasoyi akan tarbiyyar ƴaƴanta saboda ruɗin shaiɗan da son zuciya. Hannu Yasmin dake jikinta tasa ta share mata hawayen. “Mommy ki daina kuka, banason naga kina kuka kamar irin na Aunty R”.
Asabe ta rungume Yasmin tana murmushi da share sauran hawayen. “Na bari auta, itama bazata sake yin kukaba insha ALLAHU. Da ga yau zan tsaya akanku da inganta tarbiyyarku da muku addu’ar miji nagari ba irin mahaifinku ba da ni.”
Ba Raudha da ɗabi’ar iyayensu ke damunta a rai ba, hatta su Fatisa yau duk sai jikinsu yay sanyi ƙalau. Bayan asabe ta kira ƙawarta dake hutuwa sukai magana sai suka ɗunguma tasha duk da yamma tayi liƙis. Basu damuba dan tafiyar daren ma sai tafi musu kwanciyar hankali. Anan tasha sukasha ruwa dayin sallar magriba. Kafin motarsu ta tashi zuwa birnin Bingo. (Babban birnin ƙasar NAYA kenan. Dan yanzu hajiyar birni tana nan da zama ta baro jihar loss).

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button