BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

1~ BAQAR INUWA????
Billyn Abdul

1~ RAYUWAR MACE????
Hafsat Rano

1~ MASARAUTA????
Miss Xoxo

1~ NOOR ALBI❤‍????
Mamuhgee

Guda 1????300
Guda 2????400
Guda 3????500
Guda 4????700
Guda 5????1k

ZAKU BIYA KUDINKU ANAN????????

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya????????

09032345899

KATIN MTN????????

09166221261


JAMA’AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan????????

Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F

ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA????????

+227 95 16 61 77

TEAM ZAFAFABIYAR????????????????


BAƘAR INUWA…????????

https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09

Da ɗumi-ɗuminsa????????????????????????????????

Please
Follow me
Share
Comments akan abinda ya shige maka duhu.

     _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar????????????????????????_

YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za’a cike Form ɗin kamar haka: –

Enter your name: (Cikakken sunanki)

Enter your mail: (Email ɗinki)

Enter an username (Sunanki)

Enter your password: ( misali 12341234)

Confirm password: (misali 12341234)

Sai a taɓa Sign Up shikenan an buɗe account a ArewaBooks????????????.

Continue with Google – Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za’a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

Register – Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.

AREWABOOKS LINK kai tsaye

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3

Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com

Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App… Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine.

MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER

+234 903 177 4742

Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan????????????????????????.

ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????

ALLAH ka gafartama iyayenmu???????? ????Typing????

Episode 8

…………“Nikam dai nake ga kamar anzo gaɓar daya kamata ace nasan minene damuwarka?”.
Dattijuwar tsohuwa fara ƙal ta faɗa tana duban dattijon dake kishingiɗe a gefenta yana buɗe kwanikan data ajiye masa masu ɗauke da tuƙaƙƙen tuwo dawa daketa tashin ƙamshin kanwa. Duk da jin daɗi dake tattare da yanayinsu hakan bai hana bayyanar tsufanta ba ƙarara, sai dai jikinta nada ƙwarinsa musamman daya haɗa da cikar kamala da nutsuwar dake tattare da ita. A fuska kawai zaka fahimci ita ɗin bamai yawan wasa bace sam. Sai dai hakan bai hana kwarjininta bayyana akan fuskar ba.
Yanda ta tsatstsare sa da idanunta masu girma da haske duk da tsufan dake tattare da zagayen fatarsune ya saka Alhaji Hameed sakin murmushi yana tashi zaune sosai.
“Nifa kibar hukuntani da idanun nan naki Jannatu, tunda ko kwanikan nan da kika ajiye shaidane banyi wani laifi ba”.
Murmushi ta saki a karon farko tana girgiza kanta mai cike da furfurar gashi dake shan gyara. Ta gyara zamanta tana gyara kwanikan tuwon data zuba masa a gabansa. “Nima ba hukuntaka nakeba Dattijo. Kawai dai idaniyatace ta gaji matuƙa da ganin yanda kullum tunaninka keyin nisa da ni. Tun randa kukai zama da shugaban ƙasa na fahimci ka kasa sukuni. Daka zauna ko wani ya gusa a jikinka zakai nisa da duniyar mutane zuwa wata daban. Idan har ban shiga hurumin daba nawaba mizai hana na sani ko inada abin cewa dazai kawo mafita dattijo”.
Komai baiceba. Sai dai yayi murmushi mai sanyi da cigaba da cin abincinsa da yakeji a duk duniya babu abinda ya kaisa daɗi da nutsuwa a garesa. Itama ɗin bata sake cewa koman ba, dan ta fahimci ma’ana da dalilin shirun nasa. Sai ma ta maida hankalinta ga television ɗin dake manne a ƙayataccen bangon falon nasu kawai.

    “Babu wanda ya shigo cikin yaran nan?”.
    Alhaji Hameed ya faɗa dai-dai yana ture kwanikan abincin nasa alamar ya kammala. Hakan kuma yayi dai-dai da juyowar matar tasa garesa tana gyaɗa masa kanta. “Babu wanda ya shigo, kasan yau jajibirin salla, mafi yawansu suna can wajen gyaran jikin kwalliyar salla. Garama ja'irarnan Bilkisa data shigo ɗazun da hantsi tacemin can zataje sallar juma'a wajen uwarta Asma'u”.
   Kansa kawai ya jinjina mata tare da ɗaukar ruwa yasha. Sai da ya ajiye kofin dayin hamdala ga UBANGIJI kafin ya gyara zamansa sosai da sake nutsuwa fiye da farko.
  “Jannatu tabbas akwai abinda ke damuna, sai dai na barsane a iya ni da tunanin zan samo mafita mai ɓullewa kafin ki sani k da Basheer. Kamar yanda kikayi tunani damuwata nada alaƙa da zuwa ofishin shugaban ƙasa.” yaja numfashi, batare da ya bata damar cewa wani abuba ya cigaba da faɗin, “Ya buƙaci na fito takarar shugabancin ƙasar NAYA saboda rikicin da aketa tafkawa akan wanda zasubama takarar a wannan jam'iyyar. Dan kusan mutane biyar ne suka nuna sha'awar hakan, sannan dukansu sun cancanta a fuskar gudunmawar da suka bama jam'iyya da shi Excellency ɗin. Kai kawon daketa wanzuwa ya sakashi ganin duk su huta shi ya ɗora wanda yaga ya cancanci ɗorawa daga ayyukansa. Shine bai tunkari kowaba sai ni”.
   (Murmushi) ta saki murmushi mai faɗi tana sake fuskantarsa. “UHMM!! That's a salient point Dattijo. Sai dai kai wace amsa ka bashi?”.
   “Ban san dalilinki na jingina tatsuniyar tasa da muhimmiya ba. Sai dai na yarda dake wajen warware matsaloli cikin sauƙi. Amsar dana basa ɗayace wadda nasan kema zakiyi tunanin hakan, shine ba zanyiba, banga dalilin dazai sakani yin mulki a wannan shekarun nawa ba na tsufa. Kai ni bamma taɓa sha'awar hakanba shima ya sani. Siyasar kanta ma sai da kukayi yaƙi sosai kafin na shiga domin bada shawarwari badan tana cikin tsarina ba. Sai dai bijirewata baisa ya ƙyaleniba. Ya kawo dalilai masu yawa da yake ganin Basheer ya cancanta....”
    “Shima bai cancanta ba”.

Ta katsesa tana kallonsa da murmushi yanzu ma.
“Miyasa kikace haka Jannatu?”. Ya tambaya cikin mamaki da taraddadi. “Dalilai masu yawa dattijo. Sai dai ba kowa zai iya kallonsu a dalilan ba, amma nasan kaima zaka fahimci wasu a hakan”.
“A dalilin fahimtar wasunne ma yasa kai tsaye nace shima ɗin bazaiyiba Jannatu. Tayaya ma excellency ke tunanin zanbarma duniya Basheer alhalin shine kawai inuwar hutuna a yanzun. Shine kaɗai ɗan da muka haifa, a kuma wannan gaɓar dukkan wani kaiwa da komowa na abinda ALLAH ya azurtamu da shi a hannunsa yake, hasalima bana tunanin yanada interest akan mulki shima”.
“Wannan gaskiyane dattijo. Naji daɗi da tunaninmu yazo iri ɗaya. Duk da dai ni da kai akwai banbancin hange a tafiyar. Rashin cancantar Babangida ko kai a siyasa bashike nufin zamuƙi amsar wannan damar ba da ALLAH ya matso da ita a tafin hannunmu, domin taimakon talakawa da ƙasarmu ta NAYA.”
“Ban gane mikike nufi ba? Mizai amfanar damu a cikin amsa bayan munsan babu mai riƙewa to?”.
“Akwai!”.
“Akwai?! To wa kenan?”.
RAMADHAN!”
A take dukkan Murmushin da ke shimfiɗe a saman fuskarsa ya ɓace ɓat. Wani abu mai kama da fushi da ɗaci ya bayyana. Kansa ya kauda gefe tamkar bazaice komai ba, dan ita kanta ma harta fidda rai da ga jin wani abun a bakinsa.

★★★__★★★
A lissafi yau kwankinsu biyar kenan cif da shigowa cikin birnin na Bingo, inda a cikin kwanaki biyar ɗin nan Asabe tasha matuƙar fama wajen neman yafiyar mahaifiyarta data turje cewar bazata riƙe su Raudha ɗin ba. A cewarta ita kaɗai ta haifa, ita kaɗaice dolenta da idan Dauda ya koro zata amsa. Amma ƴaƴansa su shirya ta basu kuɗin mota su koma gidan ubansu suma.
Hankalin Asabe yayi matuƙar tashi harma dasu Fatisa, dan haka suka dage wajen roƙo da taya Mommynsu magiyar ganin an barsu sun rayu a kusa da ita. Sai dai ga Raudha sam abin ba haka yakeba. Dan gaba ɗaya zubin kakar tasu da ɗabi’unta basu mataba, domin tun ba’ai nisa ba ta auna ta ɗora abubuwa da yawa na kakar tasu a mizani da ya cire mata sha’awar rayuwa anan ɗin. Duk lalacewa gara gidan mahaifinta, tunda dai acan babu mai takura maka akan tilas sai kabi wata hanya mara tushe.
Abinda ya ƙara tada hankalin Raudha da zama cikin ƴan uwan mahaifiyar tata shine…. Halayensu, dan a kallo ɗaya idan kai musu da wahala ka ɗorasu a mizanin mutanen kirki kai tsaye. Kamar yanda kukaji tun a farkon labarin su Asabe su huɗu ne a wajen hajiyar birni, Asabe kuma itace auta, sannan itace ta fara bijirewa wajen ganin tayi aure. Sai dai bayan auren nata yayarta da suke uba ɗaya wadda itace ta uku a gidan itama ta sake ɓallewa tai aurenta a birnin Bina. Yayinda hajiyar birni ta cigaba da zama da sauran ƴaƴan nata biyu suna neman arziƙi ta kowacce irin hanya.
Sai dai kuma bayan shuɗawar wasu shekaru da adadinsu bai wuce uku zuwa huɗu ba itama babbar yayarsu tai aure anan cikin Loss ɗin. Amma kuma sai aka samu matsala auren bai wani yi ƙarko ba ya mutu sakamakon mijin data aura baisan haihuwa. Ta fito da ciki inda ta haifi ƴan biyu, suka kuma cigaba da zama anan wajenta, dan duk bushewar zuciya irin na hajiyar birni bata amince ƴaƴanta suyi nesa da itaba. Duk inda zaka kaje da rana ka dawo ka kwana a gida. Koda babbar yayar su Asabe ta yaye yaran nata sai ta sake wani auren duk da hajiyar birni bata so. A wannan karon tayi auren ne a jihar Dokato, inda shima auren bai kai ko’ina ba ya ƙare sakamakon jarababbiyar kishiya data samu. Nan ma ta fito da yaro, duk da shi sai da akai kicimilli kafin ubansa yabar mata akan tilas. Bayan fitowar tata kuma ƙanwarta mai bi mata itama ta auri wani ɗan siyasa mai faɗa aji anan Loss (Aunty Hannah), sai dai a nan Bingo suka zauna.
Itakam ta zauna harda yarinyarta guda data haifa da shi, sai dai sheka guda kenan auren ya mutu ta dawo gida da zama itama, ta kuma faɗa harkar siyasa dalilin sanin manyan mutane da tayi tun tana gidan tsohon mijinta ya taimakama nasarorinta ƙwarai da gaske. Dan a yanzu haka tana kusa sosai da matar shugaban kasa harma da shi shugaban kasa ɗin kansa, duk da dai bata fito da hakan a fili ga mutane saboda tsohon mijinta. A taƙaice dai a yanzu haka hajiyar birni duk tana tare ne da yaran nata da jikoki huɗu a wannan gida. Sai kuma ƴarta ta uku dake aure a Bina itama da yaranta uku. Sai Asabe mai yara huɗu, kuma sune za’a kira kamar manya a jikokin na hajiyar birni duk da uwarsuce ƙarama.
Bayan magiya da roƙo da aka dinga mata tare da yayun Asabe biyu da suka kasa zaman aure suma sai ta amince. Sai dai ta amince ne da sharaɗin zasu tashi su nema na kansu dan bazata iya ciyar dasu har su huɗu ba. Kai tsaye Asabe ta amince bisa shawarar yayun nata da suka kwaɗaita mata wani abu daban ba wanda zuciyarta take ƙyamata ba a yanzun.
To ayanzu dai haka gasu a zaune bisa sharaɗin neman nakan nasu, wanda a dalilinsa hajiyar birni tace su Raudha su shirya bayan salla zasu fara mata aiki a restaurant ɗinta. Dan zasu iya samun wasu ayyukan a dalilin zamansu wajen, tunda masu hannu da shuni ne ke dabdala akoda yaushe.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button