BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

   Da wannan tunane-tunanen ya yini a office ga mura da ciwon kai ga zazzaɓi ga kuma aiki. Yini gudan nan kuma bai ci komai ba ƙishi ma sai da yaji maƙoshinsa na neman fara yayyankewa sannan yasha ruwa, dan daya tuno jinin daya gano a Kauci sai tsigar jikinsa ta dinga tashi.

     Duk da wannan damuwar hakan bai hana wakilan da yasa minister ya naɗa zaman mitin da masu kwangilar nan ba. Sun kuma gudanar da zaman tamkar yanda ya bada umarni. Yanayin zazzaɓi daya rufesa ya sashi barin office tun 2pm ya shiga gida.

   ★Koda ya shigo gidan ya iske Raudha bata gidan, shi shaf ma ya manta da batun fara zuwanta school yau. Ɗaki ya shige ya kwanta, duk da abinci ya kamata ya fara ci ya sha magani hakan bai faruba, sai dai yaji ciwon kansa na ƙara tsanani ya ɗauka man zafi ya shafa ya sake lulluɓe jikinsa gaba ɗaya cikin duvet.

     Duk da burin da taci akan wannan rana ta fara zuwanta makaranta abinda ya faru jiya sai ya rage masa armashi, Bilkisu ce ma da zuwan Ramadhan ƙauyen ya ɗan ƙarfafa mata gwiwa. Sai dai kuma kafin ta wuce ta ɗauka shawarar zuciyarta, so take tai karatu tankar kowane ɗalibi batare da ansan ita wacece ba. Hakan kuma bazai kasance ba sai idan bata tare da dogarawanta da aka tanada mata. Gudun karta aikata ba daidaiba ta sanarma Bilkisu shawarar data yanke a yau game da karatunta. Ɗari bisa ɗari Bilkisu ta yarda da tunanin Raudha, amma itama sai ta kira Anne ta sanar mata. Hakan ya burge Anne ta kuma bama Raudha goyon baya tare da yabama ƙyaƙyƙyawan tunaninta. Daga ƙarshe Anne tace zata turo mata Adamu driver ya kaita kafin a samu drivern da zai kaita. Idan kuma zata dinga tafiya da su Basma ne sai su na biyowa ɗaukarta inhar tanada lecture tare da su tunda makarantar tasu ɗaya ce.

   Hakan yay mata, takumayi godiya sosai har sai da Anne ta ƙwaɓeta. Babu jimawa kuwa Malam Adamu yazo ɗaukar tata. Kasancewar securitys ɗin sun ganesa saboda yawan kawo family ɗin shugaban ƙasa da yake gidan yasa bai samu wata matsala ta shigaba. A ɓangaren Raudha shigar mutunci tayi dogon hijjab harda niƙaf, tafukan hanunta kawai kake iya gani hakan yasa bayan Mama ladi babu wanda yasan da fitarta. 

     Taji daɗin kasancewar ta a wannan makaranta da ta daɗe da fidda ran ganin kanta a ciki. Babban farin cikinta kuma department ɗinsu ɗaya da Rumaisa da Basma. Fadila ce kawai take daban dan abinda take karanta yanada banbanci da su Basma. Suturta jikinta ya matuƙar ɓoyeta ga kowa sai su Basma da suka sani. A nutse komanta ya gudana a wannan yani cikin kwanciyar hankali da farin ciki. Har a waya ta kira Asabe tai mata addu’ar fatan alkairi. Hakama M. Dauda ta kirashi sai dai Larai ta ɗaga cikin masifa tace baya nan. Ko jira su gaisa bataiba kuma ta kashe wayar. Murmushi kawai Raudha tayi dan halin matar baban nasu ba sabon abu bane a wajenta.

   Ƙarfe huɗu da wasu mintuna su Basma suka kawota gida, sai dai basu shigoba suka juya. Yunwa takeji sosai dan har wani dishi-dishi take gani saboda ta fita ko karyawa batai ba. Kuma har taje ta dawo ruwa kawai tasan tasha. Sam batai tunanin samun Ramadhan a gida ba tunda tasan yana office, dan haka kai tsaye ta wuce ɗakinta. A daddafe ta watsa ruwa ta canja kayanta zuwa doguwar riga mara nauyi, sai hula data saka da Slippers ta fito. Ba komai a dining, ita kuma tacema mama ladi kar ai komai sai dare tunda itama bata gida hakama bilkisu. Taɗan riƙe ƙugu da hanunta dake riƙe da wayarta, ɗayan kuma tana murza goshinta dake mata ciwo ta ciki kaɗan-kaɗan tabbacin yunwa da rashin isashen barci na damunta. 

   Rasa inda zata kama ya sata kiran Mama ladi a waya ta sanar mata ta dawo. Sai kuma ta kai zaune cikin kujera cike da rashin ƙarfin jiki tana shafa ciki da ɓata fuska. dan da gaske yunwa takeji fa irin ta fita hankalin nan. Minti goma ba’a ƙulla ba sai ga mama ladi da basket na kayan abinci, ai tunkan ta ƙaraso inda take ta sauke ajiyar zuciya da faɗin, “Wayyo mama gaskiya kina sona”.

   Ƴar dariya mama ladi tayi tana ƙarasowa gareta. Cike da girmamawa ta ce, “Barka da dawowa ranki ya daɗe ai bansan kin shigoba wlhy”.

   “Bamma jimaba mama, dan ko mintuna talatin bana zaton nayi, dan na fara wanka ne shiyyasa. Kamar kinsan da yunwa na dawo gidan”.

    “Ai nasan za’a rina, tunda naga kun fita baki karyawar kirki ba. shiyyasa na tashi na haɗa miki wannan karki dawo ba’a kammala abincin dare ba”.

   “Nagode sosai mama ALLAH ya saka da alkairi”.

  Cike da jin daɗi mama ladi ta amsa mata. ta tsiyaya mata kunun tsamiya daketa ƙamshi dan ta fahimci Raudha naso sosai, zata zuba mata sauran abinci ta dakatar da ita. “Mama bara nasha wannan tukunna dai to”.

   Cikin ƴar dariya mama ladi tace, “Yunwar dai bata kai ko’inaba ma kenan to”.

   Dariya kawai Raudha tayi itama tana saka sugar. Mama ladi ta miƙe tana faɗin, “Bara na barki kici abinci naje kitchen muga mi za’a girka kar adalin shugabamu ya dawo da wuri. Amma mi za’a girka masa da kema kanki?”.

    A cikin zuciya Raudha tace (shi wannan mina sani zaɓinsa inba nama da fura ba) a fili kam sai tace, ko tuwon alkama za’ai masa ne, sai a haɗa da farfesun kayan ciki asa yaji da ɗan yawa dan yana mura….. Kodaima mama ku jirani naci abincin zanzo kitchen ɗin kawai”.

    “To shikenan a fito lafiya”.

  A nutse Raudha ta cigaba da shan kununta hankalinta nakan wayarta tana karatun wani littafin hausa da Bilkisu ta tura mata. Bayi take ba, amma yanda Bilkisu ke zuga littafin ya sata fara dubawa shekaranjiya. Sai kuma kamar wasa labarin ya tafi da ita ta nutsu a karatunsa. Dan ita bama tasan bayan marubutan dake buga littafi ba akwai na online sai yanzu. Kodan bata da wayar ne shiyyasa. Kuma ko sanda suke hutawa bata damu da waya ba shiyyasa bata taɓa maida hankalinta ga nasu Fatisa ba, amma tasha jin suna sauraren littafi a waya ta zata na masu bugawa ne da ake karantawa a gidan redio.

     Yunwa ce ta hana barcinsa tasiri shima. Duk da dai babu laifi ya ɗanyi tunda gashi har makara sallar la’asar yayi. Da ƙyar ya tashi zuwa toilet ya ɗan watsa ruwa duk da zazzaɓi dake jikinsa ga ciwon kai. A kallo guda zaka fahimci murar ta sake masa rugu-rugu dan saman hancinsa ya ƙara jaa sosai abinka da fari. Hakama idanunsa sun kumburo fiye da jiya fatarsu tai jajur. Ga shi dama baiyi wani barci isashe ba da daddare. Sama-sama ya shafa mai ya saka wando da riga masu ɗan kauri na kamfanin adidas harda hula a jikin rigar, sai dai bai ɗora hular a kansa ba ya saketa saman bayansa. Slippers ya zura cike da dauriya ya fito falon hannayensa duka a aljihun wandon, gara ya samu ko tea ya sha kozai samu nutsuwa ta wani ɓangaren. Tun daga nesa idonsa ke kanta, yayinda sam ita batasan dashi a wajen ba dan gaba ɗaya hankalinta ya tafine akan littafin da take karantawa mai suna SIYASA KO ƘABILANCI? na (marubuciya Bilyn Andull ƴar ƙasar Nigeria). Labarin ya matuƙar ɗaukar hankalinta saboda kamanceceniyarsa da tsarin da mijinta kamar yake kai a yanzun.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button