BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

   “Kiramin Anne”.

Badan taso ba tabi umarninsa tai kira number Anne ɗin. Sau biyu tai wringing aka ɗaga, a hanunsa ta ɗora wayar dan ita kam bata san mizatace da Anne ɗin ba. Shima komai baice mata ba ya tashi da ga kafaɗarta ya kwantar da bayansa a kujerar yana kai wayar kunnensa. Dai-dai Anne na ambaton sunan Raudha cike da kulawa….

    “Anneee!”.

Ya kira sunanta cikin katseta. Ɗan jimm tayi kafin tace, “Ramadhan!”.

   “Uhhyim”

Ya amsa yana sakin atishawa cikin rashin ƙarfin jiki. A take Anne ta rikice, dama tun jiya ta tsargu a muryarsa da suna waya. Amma koda ta tambayesa sai ya nuna mata lafiyarsa ƙalau. 

    “Baka da lafiya ko! Haba Ramadhan abin nan kasa a ranka harya kwantar da kai haka?”.

   “Anne cool down mura ne tun a uk nataho da shi”. 

  Sanin wahalar da shi da mura keyi ya saka Anne sake shiga damuwa. Cikin ƴar rikicewa tace “Haɗani da Aminatu”.

    Maimakon bama Raudha da akace sai cayay “Anne ni dai kizo dan ALLAH, ko kuma na taho nan”.

   Murmushi tayi mai sauti, ita kanta tasan badan raino irin na uwa taima Ramadhan ba tabbas a taɓare zai tashi. Sai dai batai sakancin masa rainon kaka ba ta tsaya kansa da tarbiyyarsa tamkar uwa, kai ko uwarsa batajin idan da a hanunta yake zai samu tarbiyya makamanciyar wadda yake a yanzu. “To naji bani Aminatu nace”.

   Fuska ya tsuƙe yana ɗorama Raudha wayar a kunne sai kuma ya tashi zaune ya ɗauka kunun ya cigaba da sha badan yana masa daɗi a baki ba, saboda gaba daya baida appetite. Gashi kuma yaji tasa sugar sai dai baiyi ƙarfi ba shiyyasa bai damu ba tunda yana ɗan sha wani lokacin duk da yana wahalar da shi idan akai rashin sa’a…

     Cikin damuwa Anne take amsa gaisuwar Raudha. Kafin ta ɗora da roƙo akan Ramadhan ɗin. “Ameenatu kiyi haƙuri nasan bazaki barsa cikin ciwo ba amma dan ALLAH ki kula dashi sosai kinji. Ramadhan nada matuƙar rauni akan ciwo bai da juriya, ga rakin tsiya. Dan gaba ɗaya shafkewa yake tamkar yaron goye musamman mura da bata masa kamun wasa. Wajigasa take matuƙa ga wannan ma naji kamar ta masa ƙarfi sosai halan baisha ko magani ba tun jiyan?…”

   Cikin ɗan in ina da kunya Raudha tace, “Eh Anne gaskiya inaga bai sha ba, dan yau tunda safe ya fita a gida”.

    “Amma garin yaya haka ta kasance Aminatu?”.

  “Uhm..uh…m Anne jiyanne ransa ɓace ya kwana saboda abinda ya faru a ƙauyan can, daga baya ma kulle kansa yay a ɗaki”. 

   Sosai Anne ta sauke numfashi mai nauyi tunda tasan halin kayanta idan ransa ya aɓaci. Alhmdllhi ma an samu canji bai sauke damuwar kan ƴar mutane ba, koda yake bawai komaine ke ɓata ran nasa ya aikata ba. Cikin katse tunanunta tace, “Ai mijin nan naki kam sai addu’a Aminatu, wani lokacin idan ya birkice tamkar mai iskoki a ka haka yake. Sai kinta haƙuri kinji. yanzu dai asamu kayan ƙamshi ai masa shayi da su citta ya fito sosai a ciki harda tafarnuwa. A abincin da yace yana so ma asaka yaji ya ɗan fito. Nasan sa da son wanka da ruwan sanyi ki hanashi, hakama ruwa mai sanyi karki bari yasha koda fura ne ko madara. Ruwan shansa ya zama da ɗan ɗumi haka, ƙafarsa ta kasance cikin safa. Yasha magani idan yaci abinci insha ALLAH zai taimaka masa hakan dan haka nake masa idan yana mura. Zuwa anjima zan kira, idan zazzaɓin bai sauka ba sai a turo Dr Shamsu.”

     Raudha dake jin lisaafin kamar na ɗan goye ta jinjina kanta kamar tana a gaban Anne. “To Anne insha ALLAH yanzu duk za’ayi. ALLAH ya ƙara lafiya da nisan kwana.”

   “Amin Aminatu ALLAH ya saka miki da alkairi yay miki albarka.”

  Cike dajin daɗi Raudha ta amsa mata kafin suyi sallama……..

      Wayar ta sauke da ga kunnenta tana sauke numfashi. Sai kuma taɗan kallesa ta maida kanta ƙasa da sauri ganin ita tsurama idanunsa kumburarru. “Mizaka ci to sai a girka kafin magrib insha ALLAH an kammala?”.

    A hankali ya janye idanunsa a kanta batare da yasan ya shagala a kallonta ba tun tana waya da Anne. Shi kansa zuwa yanzu ya tabbatar yarinyar ƙyaƙyƙyawa ce, sai kuma baijin zai….. Kasa ƙarasa abinda zuciyarsa ke son faɗa yayi badan yasan dalili ba. Cikin dasashshiyar muryarsa ya sake dubanta yana magana a hankali tamkar mai raɗa. “Koma miye ki dafa zanci”.

   Kanta ta jinjina masa tana miƙewa. Ya bita da kallo harta nufi stairs. Sai da ta ɓacema idanunsa ya sauke numfashi da ƙyar yana ɗaukar remote ya canja television zuwa inda zaiga labaran shida na yamma.

   Sanin maitarsa da nama ya saka Raudha haɗa masa farfesun da taimakon mama ladi. sai kunun gyaɗa, madarar shanu dake gidan ta tafasa itama ta juye masa a flask sai shayi. Aikin bai wani jasu da nisa ba tunda kaɗan iya cikinsa ne. Kuku kuma sukai sauran iya dai su dake sashen.

    Da taimakon mama ladi ta hauro da kayan anata kiraye-kirayen sallar magriba. Ya tashi a falon, dan haka Raudha ta amshi sauran kayan hanun mama ladi tana mata godiya. Ɗakinsa ta nufa, tai knocking har uku bataji motsi ba, sai kawai ta tura ƙofar ta shiga da tunanin ko yana alwala. Ɗakin na nan tsaf yanda ta gyarashi da safe, sai dai duk ya watsar da kayan daya dawo office akan gado da ɗan stool ɗin jikin gadon zuwa ƙasan carpet. Kayan hanunta ta ajiye tana kwashe kayan, sai lokacin idonta ya sauka kansa a gado nannaɗe cikin bargo. Tausayi ya sake bata, ta ƙarasa ta gefesa, ɗan ranƙwafowa tai a ɗarare takai hannu taja bargon daya rufa har saman kansa, rawar sanyi ma taga kamar yanayi, yana ƙoƙarin ture hanunta da son hanata janye bargon sai hanun ya shiga cikin nashi, damƙewa yay da iya ɗan ƙarfinsa ya fisgota. Abinka da ba ƙarfi ɗaya ba sai gata gaba ɗayanta a kansa.

    “Wayyo ALLAH na”. Ta faɗa cikin matse fuska saboda ƙirjinta daya bugi jikinsa, sauƙinma laushin bargon ya bata kariya sosai. Ƙoƙarin tashi take kamar zata fasa kuka, hakan ya bashi damar ɗaga bargon ya turata ciki. Rawa jikinta ya farayi, dan al’amarin yazo mata a bazata, ta shiga son fita da janye jikinta daya tura a nasa ya matse, duk da a halin ciwo da yake ciki hakan bai hanashi sauke ajiyar zuciya ba. Cikin rawar muryar da ke tabbatar da baida lafiya yake magana a kunenta cikin raɗa da sambatu na ciwo (Dan idan yana ciwo tofa akwai sambatu kamar su oh eh????. bazan faɗi suna ba dai???? lol.)

     “Anne sanyi nakeji ki ƙara min bargo, Anne kaina ciwo kamar zai fashe, wayyo Anne kaina jikina zafi Anne ko’ina ciwo”.

    Dariya, tausayi, tsoro, mamaki, duk suka dira a zuciyar Raudha lokaci guda. Gata matse a jikinsa tamkar zai ɓalla mata ƙasusuwa ga zafin jikinsa na matuƙar ratsa nata jikin. Sosai ƙirjinta ke bada sautin fatt! Fat!! Da ƙarfi, da ace lafiya yake babu abinda zai hanashi da kiranta matsoraciya. Cikin rawar murya tace, “To ka bari na tashi na baka magani gashi magrib ma tayi”.

    Jin muryarta saɓanin ta Anne da yake tsammanin ji ya ɗan buɗe ido, ba ganin fuskarta yake ba dan ya rufe musu har kai a bargon, “Kinada tausayi kuwa?”. Ya faɗa yana sake ƙanƙameta har saida tai ƴar ƙara saboda ƙirjinta. gaba ɗaya a birkice yake, “I’m sorry”. Ya sake faɗa a hankali cikin kunenta yana sassauta mata riƙon, sai kuma ya sake faɗin, “Kiyi shiru bana son magana kaina na ciwo”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button