BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

        ★Kamar da wasa ƙaramar magana ta zama babba. Dan kuwa dai babu ɓata lokaci Pa ya tunkari Anne da Bappi da maganar. Sunji daɗi sun kumayi farin ciki, dan haka Bappi yace yabar komai a hanunsa.
     A ɓangaren Bappi ma bai tsaya jan al’amarin ba ya tunkari su Hajiyar Birni da shi, sai dai kamar yanda yay hasashe Asabe ta nuna bijirewa su Hajiyar Birni sukai mata can. Murmushi kawai Bappi yayi, tare da basu shawarar su barta tayi tunani, amma ta bama Alhaji Sageer Dogarai ɗin damar zuwa gareta tukunna sai ta yanke hukunci. Ta aminta da hakan, babu kuma ɓata lokaci Alhaji Sageer yazo gareta washe gari.
        Mutum ne kamilalle kuma mai tarin nutsuwa. Ba wani tsufa yayba dan shekarun nasa bazasu gaza dai-dai da Pa ba, ga iya magana dan a ƙankanin lokaci ya siye zuciyar Asabe har taji ta gamsu da shi. Sai dai bata amsa masa ba sai da ta garashi sosai. Shiko bai gajiya da binta ba har sai da ya samu amincewarta. Hajiyar birni kam ai likafa taci gaba burikanta nata tabbata bayan wahalar da taci a rayuwa da garari akansu. Wani lokacin bawa nayin gaggawa ne akan abinda baida masinaiyar UBANGIJI ya tanadesa cikin ƙaddararsa. Sai son zuciya ta sakashi tsayawa wajen nemansa koda ta hanyar data saɓama shari’a ne. Sai kaga yazo ya samu abin kuma daga baya.
      Alhaji Sageer ya matsa shifa ayi aurenau kafin nasu Fatisa. Itako ta dage akan a’a sai anyi nasu Fatisa. Bai haƙura ba ya cigaba da jajircewa har hajiyar birni ta tabbatar masa yanda yakeso haka za’ai. Sam Asabe bataso hakanba. Sai dai bata ƙaunar yima mahaifiyarta jayya ko kaɗan, sannan Aunty Halima na ɗorata akan shawarar ƙwarai na gara tai auren ko bikin ƴaƴan nata ya ƙara mutunci a idon mazajensu da al’ummar da zasu halarci bikin. Tasan gaskiya Aunty Halima ta faɗa mata, dan haka ta tara yaranta ta sanar musu Raudha kuma aka faɗa mata ta waya. Kamar yanda su Fatisa suka nuna kishin Abbansu a fili haka ma Raudha. Dan kuka ta dinga rusawa akan ita bata yarda Mummyn nasu ta sake aure ba.
       Shi dai Ramadhan ma da yaji tushen kuka. tagumi ma kawai yay yana kallonta. Sai da tayi mai isarta sannan yay magana.
       “Oh ni Ramadhana naga takaina. Ni karma a haifamin yara masu kukannan fa? Yanzu ke Partner dan ALLAH ba abin farin ciki bane Mummy tai aure? Kinada ilimin addini fa, kin kuma san babu sauran aure tsakaninta da Abba taya zata cigaba da zama kuma a haka bayan har yanzu shekarunta basuyi nisan da hakan zai kasance ba”.
      Baki ta tura gaba da juya masa baya zata kwanta ribda ciki ya riƙota. “K rufamin asiri, da wannan cikin zakiyi wannan kwanciyar?, ga Abba ya samu mai tayasa kishi ni ki halakamin nawa.”
     Dama ba kwanciyar zatai ba. Dan yay magana tai hakan, ta sake tura baki da buge hanunsa dake riƙe da cikinta daya sake fitowa sosai yanzu kowama zai iya shaida akwaishi.
        “Ni dai yi haƙuri karki cinyeni da baki, yarana suzo suga an gama gwaguyeni”.
      Filo ta ɗauka ta shiga kai masa duka yana karewa da dariya, sai kuma ta mike daga gadon ta sauka tana daddaga kafa. Saurin riƙota yay ya zaunar a cinyarsa. Zata ɓare masa da kuka ya ɗaura lips nashi kan nata daga haka labarin ya canja.
      Bai bartaba sai da ya tabbatar dukkan damuwarta ta gudu sannan suka shiga toilet suka tsarkake kansu tare. Bayan sun fitoma nasiha ya dunga mata har sai da ta fahimcesa ta sakama auren albarka. Suka kuma kira Asabe tare suka gaisheta da nuna mata goyen bayansu dan yanzu dama Ramadhan kanyi waya da Asabe da M. Dauda lokaci-lokaci. Hakanne ya ɗan ƙara sakama Asaben nutsuwar zaman Raudhan tare da shi………….✍

Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹????‍♀️⛹????‍♀️????

ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA????????????????????

1~ KUFAN WUTA????
Safiyya Huguma

1~ BAQAR INUWA????
Billyn Abdul

1~ RAYUWAR MACE????
Hafsat Rano

1~ MASARAUTA????
Miss Xoxo

1~ NOOR ALBI❤‍????
Mamuhgee

Guda 1????300
Guda 2????400
Guda 3????500
Guda 4????700
Guda 5????1k

ZAKU BIYA KUDINKU ANAN??????

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya????????

09032345899

KATIN MTN????????

09166221261


JAMA’AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan????????

Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F

ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA????????

+227 95 16 61 77

TEAM ZAFAFABIYAR????????????????


BAƘAR INUWA…????????

Da ɗumi-ɗuminsa????????????????????????????????

Please
Follow me
Share
Comments akan abinda ya shige maka duhu.

     _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar????????????????????????_

YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za’a cike Form ɗin kamar haka: –

Enter your name: (Cikakken sunanki)

Enter your mail: (Email ɗinki)

Enter an username (Sunanki)

Enter your password: ( misali 12341234)

Confirm password: (misali 12341234)

Sai a taɓa Sign Up shikenan an buɗe account a ArewaBooks????????????.

Continue with Google – Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za’a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

Register – Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.

AREWABOOKS LINK kai tsaye

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3

Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com

Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App… Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine.

MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER

+234 903 177 4742

Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan????????????????????????.

ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????
Typing????

Episode 73

……….A wata juma’a datai dai-dai da saura kwanki huɗu cikar shekarr Ramadhan guda a mulki aka ɗaura auren Alhaji Sageer Dogarai da amaryarsa Asabe. Aure ne daya tara ɗunbin al’umma musamman daya kasance juma’a ne mutane duk sun halarci masallaci. Aure ne daya saka wasu farin ciki wasu saɓaninsa musamman aunty Hannah da tun farkota nuna adawawta akai, sai dai kuma babu abinda ta isa ta hana daga hukuncin ALLAH.
      Ƴar walima kawai akai amarya ta tare ɗakinta cikin aminci da mutuntawa. A kuma daren Ranar M. Dauda da abokinsa suka iso Bingo a haukace a dalilin M. Gambon ya samo labarin a shanun ƴan talla. Inda ALLAH ya taƙaita al’amarin ya kira Bappi ta waya kafin su tunkari ko’ina. Hakan yasa Bappi saurin taka masa birki yasa Malam Adamu zuwa ya ɗakkosu. Babu wanda yasan da zuwansu Taura House sai Anne da Bappi. Aka basu masauki mai ƙyau da abinci kafin safiya. Da farko M. Dauda ya nuna shifa ba wannan ya kawosa ba Bappi dai ya sake lallashinsa.

     Washe gari da suka zauna akan batun fir ya nuna shifa sai Alhaji Sageer Dogarai ya sakar masa matarsa inhar ana buƙatar zaman lafiya a NAYA. Iya nasiha yaƙi har sai da Bappi ya bama Ramadhan Umarnin sakawa a kawo masa Raudha gidan. Tana makaranta M. Adamu yaje ya ɗakkota. Gaba ɗaya hankalinta a tashe yake dan batasan mike faruwa ba. Gashi babu damar kiran Ramadhan ta damesa tasan yana office. Sai da suka iso taci karo da Abbansu ta sauke ajiyar zuciya. Yay sakalo yana kallonta da cikinta daya fito ɗas duk da ma hijjab ne a jikinta har ƙasa. Sai dai a yanda tai zaman sai da cikin ya fito.
       “Oh ALLAH sarki Raudha ashe wannan irin arziki ALLAH yaymin naketa shirme ma? Dama ciki ne da ke?”.
     Ina ƙasa Raudha ta shige dan kunya, Bappi yay murmushi mai faɗi da gyaran murya. “To kaga kariga ka fara zama babban mutum tunda ga jika kana shirin amsa duk da nasan bashi bane na farko. Ya kamata wasu abubuwan a ajiyesu hakanan kodan wasu dalilai Malam Dawood. Shi aure raine da shi, sannan ƙaddarace ta ALLAH. Ya riga ya ƙaddaro zaka zauna da mahaifiyar yaran nan na wani lokaci ku rabu, idan kuma da rabon sake zama sai kaga ta sake baro can ta dawo gareka ai”.
     Hawaye malam Dauda ya share dan harga ALLAH yana son Asabe, so irin wanda bai tabama wata mace ba. Dan ko auren nan daya kara na budurwa dal a leda bai maye masa gurbin rashin Asabe ba a ransa. Nasiha sosai Raudha da Bappi sukai masa, sai dai M. Gambo nata zungurinsa akan karya yarda wai. Tsaf Bappi ya fahimci M. Gambo, ya kuma gane shine matsalar M. Dauda. Dan haka a ranar ya saka aka maidashi Hutawa bayan ya haɗashi da shatara ta arziki.
      Sosai M. Gambo yaji zafin hakan, dan acewarsa ƙiri-ƙiri an nuna banbanci tsakaninsa da M. Dauda. hakan ya sashi ƙudirin abubuwan mugun abu da yawa cikin rai game da M. Dauda. Acewarsa in bai samu Asabe ba ai akwai hanyoyin ramuwa da yawa.
  
      Kwanan malam Dauda biyar a Bingo, dan har gidan gwamnati aka kaisa ya kaso kwarkwatar ido wannan karon. Bappi kuma ya riƙesa akan ya zauna har sai anyi bikin cika shekara guda na Ramadhan a mulki. Hakan ya masa daɗi sosai, ya kuma sakashi farin ciki. Su Fatisa ma har nan Taura house sukazo gaida shi, har kuma zuwa yanzu bayan su Anne babu wanda yasan da zamansa a gidan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button