BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

GOVERNMENT HOUSE

          Sosai aka shirya bikin cika shekara ɗayan nan har abun ya ɗan so bama mutane mamaki, dan lamarin tamkar wani arashi. An shirya ɗakin da taron zai gudana cikin tsarin ado na tutar ƙasar NAYA. Duk da gwamnoni suma zasuyi nasu a jihohinsu hakan bai hanasu halarta ba. Hakama sarakunan gargajiya da abokan kasuwancin Ramadhan.
        Su Alhaji yaro glass da muƙarrabansa harma da god fathers nasu kam sun halarci taron. Sai tarin manyan ƴan jam’iyya na kowace jiha. Kamar ko yaushe First Lady da mijinta shugaban ƙasar NAYA Ramadhan B. Hameed Taura suka iso wajen taron cikin shiga ta kamala ana take musu baya. Sanye take da hijjab har ƙasa fari ƙal mai hannu, sai kaɗan daga ƙasa ake iya ganin ƙasan doguwar rigarta mai kalar tutar ƙasar NAYA. Daɗin daɗawa akwai facemask a fuskarta tare da siririn farin glass iya hannayenta kawai ake iya gani da tsadajjen agogonta. Hakama shugaban ƙasa Ramadhan sanye yake cikin ɗanyar shadda fara ƙal daketa maiƙo da haska idanun mai kallo. Ta gaurayu da ɗinki na musamman daya ƙawatata ya kuma tabbatar fitar tutar ƙasar NAYA. Hakama hularsa zannah tayi matuƙar murzuwa. A kallo guda zaka tabbatar da tarin kwanciyar hankali da farin ciki tattare da shi. Yana riƙe da hanun matarsa har akai masa rakkiya wajen zamansa sannan mutane da suka miƙe dominsa na girmamawa suka koma suka zauna.
      Kamar yarda shari’a ta tanadar malamai sun gudanar da addu’oi kafin a fara gudanar da abinda ya tara mutane a wajen. Inda bayanin shugaban ƙasa yay matuƙar birge mutane da ƙara darajarsa a idanusu. Lokacin da aka buƙaci cewar first lady.
       Wata hamshaƙiyar mace ta miƙewa da takarda a hanunta ta tabbatar musu ga saƙon first lady ita  wakiliyarta zata isar bisa umarnin shugaban ƙasa amma matsayin miji ba shugaba ba basai tace wani abuba.
      Hakan ya bama wasu mamaki, ya birge wasu. Wasu kuwa sun gumtsi gulma da sauya zancen a muhali na daban. Oho hakan bai damu Ramadhan ba, shidai burinsa tsare mutuncin iyalinsa da kuma kishinta da yakeyi. Bayanan da aka gudanar matsayin na first lady ma sun kayatar kuma sun birge mutane daban-daban. Daga haka taro ya cigaba da guna. Anci ansha anyi hani’an first lady da shugaban kasa babu wanda yasha ko ruwa a wajen.
       Sai da ana gab da tashi a taron ne Raudha ta hango Abbanta tare da Alhaji Hameed Taura cikin shiga ta kamala tamkar bashi ba, dan kayan daya saka sun masa ƙyau matuƙa duk da jikin ya nuna ba’a saba sakawa ba. Taji daɗin yanda ya kame kansa a wajen har aka tashi lafiya.
    
     Duk yanda Raudha ke ɓoyen cikinta a hijjab hakan bai hana wasu ganewaba, tuni kuma yan jarida suka hau yaɗa cewar shugaban ƙasa gab yake da zama angon karni kuma Baba dan firt lady na ɗauke da ciki. A fanin ƴan adawa kuma sun gama baza zance first Lady dai turancine bata iyaba shiyyasa Ramadhan ya hanata magana a wajen aka samo kwararriya aka fake da kishi.
     Maganar tayi nisa sosai, sai dai cikin Raudha yaso danneta tare da manyan ayyukan da aka zano shugaban ƙasa Ramadhan ya shinfiɗa a shekara guda kacal.
      A ɓangare. su Alhaji Yaro glass sunyi zaman meeting akan cikin nan, inda kai tsaye suka ƙalubalanci Aunty Hannah data ɓoye musu hakan. Ta nuna batasan Raudha nada ciki ba itama, amma hakan bashike nuna batai murnaba. Dan ita tanada manufa akan cikin koba komai zasu kasance da wani kaso na dukiyar Taura family musamman idan aka dace Raudha ta haifo namiji.
    Wannan magana tata ta banƙanta ran su Alhaji Yaro glass, harya faraji a ransa Aunty Hannah bazatai dogon zangoba zai kawar da ita. Dan ya tabbatar shi ɗinma zata iya yin kalar tunanin da take furtawa akan dukiyar Taura family akansa kenan. Duk da kuwa Samha ce kawai a tsakaninsu har yanzun.
     To komadai miye, mudai ƴan kallone ai.????

Kwanaki biyu da yin wannan biki na cikar masu mulki shekara ɗaya akan madafun iko Malam Dauda ya koma hutawa da shatara ta arziƙi. Dan kuwa kujerar makka har uku, tare da kuɗi masu yawa da galleliyar mota da alƙawarin buɗe masa manyan shaguna a hutawa da kuɗi zasu dinga shigo masa akoda yaushe. Wannan farin ciki ya sashi danne son Asabe daya san har Abada bazai iya dainawaba.
        A randa M. Dauda yabar Bingo a ranar hoton wani video ya karaɗe yanar gizo da duk mai wayar da take iya buɗe data zai gani. Video ne daya kasance na Aynah a cikin club ana aikata masha’a da ita. Sai kuma wani shima a cikin ɗaki kusan su biyar duk mata. Abinda zai baka mamaki na club ɗin babu face mask kamar yanda Ramadhan ya sani.
      Aminu ya saki wannan video ne bayan ya saka dukan abokansa sunyi amfani da Aynah a wannan dare wasuma harta baya (Wa’iyazubillah????) yayi hakane a dalilin kawo mata ƴammatansa da yay gidan ta nuna itafa ta gaji ya sallameta hakanan kokuma ta tona masa asiri ga iyayensa da yake yaudarar nuna musu shi ɗin mutumin kirkine. Shiko ya tabbatar mata kafin tayi hakan shi zai fara tona nata a sirin wa duniya sai yaga nata da nashi wannene zaifi gawurta da kayatarwa. Tayi kuka ta roƙesa iyakar roƙo amma yay kunnen uwar shegu da ita sai da ya saki.
      A lokacin da wannan video ya riski su Addah Asmah data haukata kanta a neman asirin hallaka Ramadhan da wulƙanta rayuwarsa data Gimbiya Su’adah har ƙasar China ta yanke jiki ta faɗi. Kwannta biyu kenan da dawowarta NAYA, wata kawarta ta rakata China wajen wani gagarumin masanin tsafi. Sun dawo zuciyarta cike da jin ɗunbin nasara saboda abinda matsafin ya haɗo musu, ta tabbatar idan har tai amfani da su Gimbiya Su’adah da zuri’arta sun zama labari kenan. Sai gashi a yau da take shirin zuwa Taura house da fuskar yaudarar roƙon gafarar gimbiya Su’adah danta aiwatar da aikinta wannan mummunan labari ya  baje ƙasar NAYA dama duniya tunda abune na media ako ina zaka iya ganinsa.
     A firgice ma’aikatan gidan nasu da kanwar Aynah suka rufu a kanta sai dai babu alamar numfashi tattare da ita. Dole Zulfah tai kiran asibitin da suke ganin likita dan ta nema no na daddyn su ma bata samuba kasancewar shi bayama kasar.
     

          Hatta da gimbiya Su’adah da ayanzu babu wanda ta tsana a duniya sama da ƴar uwar tata abin ya firgitata, balle kuma Fulani da itama ta yanke jiki ta faɗi ƙasa a sume dalilin tanada hawan jini.
     Raudha ma ta gani kafin Ramadhan, amma ta kasa nuna masa sai zama datai taita kuka dan abun ya ɗaga hankalinta. Musulma ɗiyar muslmai gaba da baya itace a wannan halin duniya ke gani babu ko kunyar mahaliccinmu. Kaicon wata wayewar, kaicon wata dukiyar, kaicon wata damar dan da wata BAƘAR INUWA ce da ita gara rana ma.
      Koda Ramadhan ɗin shima ya gani baiji abin saboba tunda a gabansa aka aikata, sai dai abinda ya bashi mamaki fitar videon bayan shekaru. Hakan na nufin dan kinyi barna ko kayi ka binneta da tunanin ta wuce mutane bazasu ganiba watarana UBANGIJI idan yaso sai ya tonota ta hanyar da kai bakai tunani ko tsammani ba. Sannan ya jiraka a madakata kazo ya hukuntaka dai-dai da laifinka dan shi bai kasance azzalumin sarki ba………..✍

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button