BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

    To yau dai Raudha taga takanta. Ɗan ƙwalisar nan Ramadhan mai shegen ɗaukar kan nanne haka. Shugaban ƙasar NAYA jinin Taura da ko kallon arziƙi sai ya gadamar wanda zai yimawa. UBANGIJI mai rahama, UBANGIJI mai jinƙai. Maiyin yanda yaso, ga wanda yaso. Cikin ƙanƙanin lokaci in yaso kamaka da ƙanƙanin abu sai ya firgitaka ka mance kai waye? Miye matsayinka?. Taja numfashi a hankali da shaƙar daddaɗan ƙamshin turarensa na REED. Zuwa yanzu ta nutsu a jikin nasa badan taso ba, babu abinda ke ratsata sai zafin jikinsa da sautin bugun zuciyarsa. Sai saukar numfashinsa a wahale. Magana yake a hankali bisa laɓɓa da bataji, sai dai tanajin alamar motsin bakinsa. Ta fahimci sambatune na ciwo kawai ke ɗawainiya da shi. Kusan mintuna talatin suka samu a haka, ganin lokacin salla na sake shigewa ta fara magana a hankali cike da lallashi. 

    “Lokacin salla nata sake nisa, ga abincin na kawo maka kuma da magani kayi haƙuri na tashi na baka kar mu makara salla”.

    Sarai ya jita, dan idonsa biyu. Sai dai bai nuna alamar yajin ba har bayan shuɗewar wasu mintuna.

    Da ƙyar Raudha ta samu ya rabu da ita ta tashi, toilet ta shiga tana sauke tagwayen ajiyar zuciya da taɓa jikinda da yay zafi kamar itama ta kamu da zazzaɓin. Ruwan ɗumi ta daidaitamsa domin yin alwala. Tayo tata sannan ta fito. Har yanzu yana cikin bargon ƙudundune. Cikin lallashi tace, “Ya Ramadhan ka daure kayi sallan sai kaci abincin da magani”. Kamar bazai motsa ba sai kuma taga ya miƙo mata hanunsa da ga cikin bargon, duk da kunya dake ɗawainiya da ita hakan bai hanata kamawa ba danta fahimci abinda yake buƙat kenan ta taimaka masa ya tashi. Da taimakon nata kuwa ya tashi, ganin kamar yana tangaɗi sai taƙi sakinsa sukaje ƙofar toilet, sai da taga ya shiga sannan ta sauke numfashi. Kasancewar akwai hijjab jikinta tasa abin salla tayi anan, tana raka’ar ƙarshe ya fito da alama ba alwalan kawai ya tsaya ba yayi wani uzirin nasa daban. A ɗayan abin sallar data saka masa ya tada sallar shima yana faman riƙe kai, kafin ya idan da sallar aka shiga kiran isha’i, hakan yasa Raudha komawa ta zauna domin gabatarwa.

    Su dukansu sai da sukai salla har isha’i sannan ta haɗa masa abinci. abin mamaki yau yanka uku Ramadhan yaci na nama, sai romon farfesun kawai ya cigaba da sha. Raudha dake gulmarsa a zuciya ta shiga jinjina kai tana mamakin eh lallai magana ta girma kure na gudun nama yau. To ashe akwai ciwon da zai iya hana Ramadhan cin nama a duniyar nan?. Batace komai ba ganin ya ɗan sha ruwan kunun ya kuma sha romon nama. First aid box data gani a ɗakin ta ɗakko ta duba, cikin sa’a ta samu maganin mura data san yanada inganci tunda tasha amfani da shi itama. Da ƙyar ta samu yasha maganin yana yamutse fuska har yaso bata dariya, ta dai daure ta gimtse.

   Koda ya koma saman gado da nufin kwanciya a ɗofane taɗan zauna. gadon da nufin gyara masa bargo kawai sai jitai ya ɗaura kansa a cinyarta, tare da riƙo hanunta yay filo da shi a kuncisa. Idanu Raudha ta ƙwalalo sai kuma ta ƙwaɓe fuska. Oho basai tanayi ba dan harya fara lumshe idanu, dole ta hakura da ƙudirin idan yayi barci ta zame jikinta ta gudu………..✍

End of book
Leave a comment

Post

Comments

104835043420935222197
Fist to read????

8 hours ago

Contact Us
Arewa Books Publishers

WhatsApp: 09031774742

Email: arewabookspublishers@gmail.com

Navigation
Home
About
FAQ’s
Legal
Privacy Policy
Terms of Service
Social
Facebook
Instagram

Copyright 2021, Arewa Books | ALL RIGHTS RESERVED | Powered by thinkcrypt.io
Chapter 46
46

…………Tun Raudha na irga sakanni harta koma mintuna, kamar wasa suka cinye rabin awa. Data yunƙura zata tashi Ramadhan zai sake ƙanƙame mata hannu, ga kansa bisa cinyarta. Fahimtar kamar barcin nasa baiyi nauyi ba yasata haƙuri ta sake bashi lokaci harda jingina da fuskar gadon, cikin rashin sa’a itama barci yay a won gaba da ita a wajen mai nauyi dan a gajiye take yau ga rashin barcin jiya cike da idonta dama.

    A hankali ya fara buɗe idanunsa da sukai masa nauyi irin na mai farkawa a barci da rashin jin daɗin jiki. Alhmdllhi zazzaɓin ya jima da sauka. Hakama ciwon kan kaɗan-kaɗan yake jinsa shima yanada alaƙa da maganin murar da bai gama sakinsa ba dan barcine taf a idanunsa. Sabo da tashi sallar asuba akan lokacinta ya sashi farkawa. Hanunta da ke riƙe a nasa fuskarsa a kai ya ɗan tsurama ido, tun yana kallonsa dishi-dishi cikin ɗan hasken lamp har idonsa ya dai-daita. Zuciyarsa ce ta ɗan motsa na alamar mamaki, yay saurin ɗaga kai ya dubi sama. Itace kuwan da gaske, kuma akan cinyarta kansa yake. Ta ɗan zama kaɗan ta kwanta saɓanin da da take zaune. Sai dai a kallo ɗaya ya fahimci kwanciyar batai mata daɗi dan a matuƙar takure take a wajen. 

    Idanunsa ya dafe tare da cije haƙoransa ya tura yatsun hanunsa cikin sumar kansa. ‘Ya ALLAH’ ya faɗa a hankali cike da jin haushin kansa. Dan ya gama fahimtar lallai anyi abun kunya a daren jiya. Inhar irin sambatun daya san yanama Anne idan yana zazzaɓi yay mata itama to shikan dai yagama ganin takansa, raini kuma tsakaninsa da yarinyarnan ya samu gurbin zama. ‘Ni Ramadhan miya shiga kaina ne wai?’.

   Ya sake faɗa a fili lokacin da yake tashi zaune hanunsa dafe yaɗan karkata yana kallonta. Duk da takaicin kansa da yake ji hakan bai hanashin jin tausayinta ba. Shi kansa ya sani idan shine bazai iya juriyar kwanciya haka ba dan kawai wani yaji daɗi shi. Jin za’a tada salla ya sashi miƙewa ya sakko a gadon da ƙyar, sai da Raudha ta tabbatar ya shiga bayin sannan ta buɗe ido a hankali. Tun motsawarsa itama ta farka, ta ɗaga hanunta da yay matuƙar tsami da ƙyar taɗan yarfar, wani irin azaba ya ratsata. Saurin riƙewa tai da ɗayan tana cije baki. Da ƙyar ta iya tashi dan kafaɗarta zuwa wuya suma duk a riken suke. 

     Cikin dauriya ta fita a ɗakin zuwa nata dan shima taji motsin ruwa alamar wanka yake. Itama da gasa jikinta ta fara, duk da ba saki hanun da wuyan sukai ba haka ta daure bayan idar da salla ta nufi kitchen. Tunda ta fito ma’aikatan gidan daketa fitowa domin tsaftace sashen ke zubewa suna gaisheta. Babu sa’anta a cikinsu, ta tabbatar kuma ko’a ilimi sun fita, dan haka take matuƙar jin nauyin wannan girmamawa da suke mata. Sai dai tana dauriyar dannewa da amsa musu a dake dan wani girman idan ALLAH ya baka dole kai haƙuri ka riƙe.

    A kicin ɗin ma duk zubewa su kuku sukai suna gaisheta, sukam har sun tsaftace ko’ina sunama ƙoƙarin fara ɗora abinci ne. Tambayar mi zasu dafa tayi, suka sanar mata. Babu abinda ya kwanta mata da yanayin mara lafiya, dan haka tace suyi iya wanda za’aci kawai. Ita kuma ta fara ƙoƙarin haɗama Ramadhan da taimakon Agnes da ita kaɗaice kuku mace a cikinsu. Haka kawai nutsuwar Agnes ɗin ke burgeta. Gata dai ba muslma ba amma bata da rawan kai, kuma bazaka taɓa ganinta da shigar banza ba. Haka farce da ƙarin gashi duk bata sakawa.

    Komai suke Agnes a girmame take tayata duk da ta girmeta sosai, amma tsabar girmamawa Mommy take kiran Raudha. Tsaf suka kammala komai, Raudha zata ɗauka basket ɗin Agnes ɗin tai saurin ɗauka cike da girmamawa. “No Mummy zan ɗauka”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button