BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

★★★

 A can gidan su Raudha ma taƙe yake da mutane har wani baya iya jin zancen wani. Amarya na maƙure jikin Asabe dan zazzaɓi ne mai zafi a jikinta har amai tayi ɗazun saboda takura mata taci abinci da Hajiyar birni tayi. Kwalliya kam sai da hajiyar birnin da Aunty Hannun sukai tamkar zasu halakata dan bala'i sannan ta amince akai mata.
 Cikin ƙanƙanin lokaci ta fito tamkar tauraruwa cikin taurari. Tayi ƙyau harta gaji, musamman da sarƙan gold ɗin wuyanta tai mata wani irin masifar ƙyau da haska fatarta. Duk yanda akaso ta fita tsakar gida ƙi tayi, dan har aka fara guɗe-guɗe a cikin gidan na jin an ɗaura auren bata leƙo ba, sai ma fashewa da tai da kuka mai ban tausayi, dan tasan tata ta kare. Wannan auren tamkar mabuɗin buɗe hanyartane na zuwa lahira ita da wanda ta aura ɗin.
 Tana daga kwance tanajin labarin taron mutanen da aka tara wajen ɗaurin auren nata. Sai taji komai ya kuma kwance mata a ƙwaƙwalwa.

★★★

   An kammala ɗaura aure mutane suka fara kama gabansu. Wasu garuruwansu suke komawa, wasu Bingo. Kafin la'asar sai yazam tsirarun mutane suka rage sai tulin jami'an tsaro. Shi kansa angon ana idar da sallar la'asar jirgin helicopter yazo ya ɗaukesa. dan tawagar da yazo da ita ta abokansa da abokan kasuwanci tuni sun kama hanyar Bingo. Ibrahim babban abokinsa tun na ƙuruciya ne kaɗai anan tare da shi. Duk yanda Ibrahim ɗin yaso yaje yaga amarya tare da sauran abokai ayi hotuna Ramadhan bai bada fuska ba. Dole suka haƙura tunda sun san gobe idan ALLAH ya kaimu dole ne su ganta a wajen dinner da kuma rantsarwa ranar lahadi.

  Ɗagawar jirgin ango babu jimawa jerrrun motoci  talatin cif suka sake shigowa garin Hutawa. Sai na jami'an tsaro dake biye da su kai kace shugaba ƙasar akazo ɗauka, sai dai kuma ko basuzo ɗaukar shugaban ƙasa ba sunzo ɗaukar mata kuma amaryar shugaban ƙasa. (???????? wayaga Mino first lady. Lol)
    A yanzun kam ma kukan Raudha ta kasa, dan anan ɗin ma babu wanda ya zaunar da ita yay mata faɗa balle nasihar aure ko lallashinta. Damuwarsu kawai karsu rasa motar zuwa kai amarya. Andai kira Mal. Dauda sunyi sallama. koda yazo shima ɗin sai ya ɓige da matsar ƙwalla yana jaddada mata inhar bata zauna lafiya gidan mijinta ba harya sakota tai masa baƙin cikin wannan NI'IMTACCIYAR INUWAR da ALLAH ya tsundumasa sai ya taine mata. Kuma babu shi babu ita. Ko kasheta kullum Ramadhan zai dingayi ana sake busa mata sabon numfashi baice ta nuna masa damuwarta koda a fuska ba.
 Jikin Asabe ya ƙara sanyi da kalaman tsohon mijin nata da ayanzu takema kallon wanda baisan ciwon kansa ba. Yayinda tausayin ɗiyarta ya ƙara mamayeta. Sai dai babu yanda zatayi dan su Hajiyar birni sun hanata kowane irin ƙarfin iko na uwa, komai sun mamaye. 

   Zuwa ƙarfe biyar da wasu mintuna kowacce mota ta ɗauki iya adadin mutanen da zata iya. Yayinda suka fita cikin garin Hutawa a jere motar amarya a tsakkiya. Gaba da baya jami'an tsaro ne. 
  Wani irin sarƙewa numfashin Raudha ya shigayi alamar Asthma ɗinta zai tashi, dan kuka. ALLAH yasa Hajiya mama dake a motar tai saurin fahimta taja hand bag ɗin Raudha da sauri tana laluben inhaler ta. Da ƙyar ta samota aka shaƙama Raudhan. Sai da numfashinta ya dai-daita suka shiga sauke ajiyar zuciya ita da Hajiya Zuhrah dake tamkar ƙanwa ga Pa. uwa ga su Ramadhan. Dan kuwa Yafendo ce ta haifeta. Itace babbar ɗiyarta, sai dai tana Australia tare da mijinta dake matsayin ambasada a can. A yanzu ma biki ne da bikin rantsar da Ramadhan ya kawosu ƙasar. Komi na kammala kuma zasu juya.
    Tuni tausayin Raudha ya sake mamayeta, dan tunda ta ganta ƴar ƙarama take mamakin yanda iyayenta suka amince suka mata aure (kusan su irin manyan nan wayayyu ƴaƴan sai sunci boko sun ƙoshi, wani lokacin ma ba bokon ke hanasu yin auren ba, ra'ayine kawai da tunanin za'a yanke musu jin daɗin rayuwar ƴammatanci ko samartaka. Shiyyasa suke ganin masu aurar da yara 17years zuwa 20 tamkar ganganci sukai????).

___________

   *_BINGO CITY_*

Kamar yanda aka nuna ɗaurin auren shugaban ƙasa Ramadhan live a gidajen tv haka aka nuna tahowar amarya da isowarta bingo ma. Inda duk da ɗunbin mutanen nan dake cike da Taura house da wanda sukayo ma amarya rakiya hakan bai hana Anne da ke fama da tsufanta ba fitowa tarbar amarya ita da su yafendo. Fulani na zaune tare da su suka fito amma batako motsa ba. Dan tona irin baƙin cikin da suke ciki game da auren nan ita da Asmah da gimbiya Su’adah ɓata lokacine. Abinda kawai suka sani shine sun tanadama Raudha bama-baman bala’in da sai ta gudu gidansu da ƙafafunta. Dan shi kansa Ramadhan ɗin jiya ya sha masifarsu saboda yace suyi haƙuri shi bazai iya bijirema Pa da Bappi akan maganar auren nan ba.
Aiko sukai masa ca gimbiya Su’adah harda kuka wai Anne ta asirce mata shi bayajin maganarta baijin ta mahaifiyarta da ƴan uwanta. Shi dai bai sake ce musu komai ba, da ga ƙarshe ma kiran wayarsa da akaine tai bailing sa ya samu ya gudu musu. Har zuwa yanzu kuma basu sake ganinsa ba, dan koda ya baro Hutawa kai tsaye wajen meeting ɗin da zasuyi da shugabannin jam’iyya na jihohi ya wuce.

   Sosai ahalin Raudha sunji daɗin tarbar da akai musu. Tun daga kan shimfiɗar fuska har zuwa ta wajen zama da abinci dana sha koma Alhmdllhi. Mafi yawancinsu kuma ba ƙaramin rikicewa sukai da ƙaton mansion ɗin na Taura ba. Har takai wasunsu ma sun gagara bakin magana.
   Babu wani event a yau, dan Bappi ba mai son yawan bidi'oi bane, shiyyasa da wahala kaga anyi taron biki a gidan ana wannan events ɗin na almubazaranci da dukiya, komai yana tafiyane gwargwado, sai abinda ya zama wajibi kamar abinci wannan kam har sai kaci nama ka gaji duk haɗamarka da zura...????

WASHE GARI ma babu wanda yaga idon ango har kusan azhur, dan jiya bai dawo gidan ba sai kusan 3am. Hakan ya sakashi maƙalewa a part ɗinsa yaki fitowa. Ko sallar asuba a gida yayi saboda makara da yay. Masu kiɗan ƙwarya sunyi wasa daga safe zuwa azhar ɗin anan cikin gida. Abin kuma ya ƙayatar da mutane dan kowa yayi farin ciki. Inda amarya tasha ƙyau harta gaji. Dan nasiha da lallashin da Anne tai mata a daren jiya yasaka mata nutsuwa ta daure tabar kuka kasancewar a ɗakin Anne ta kwana tare da ita. Takoji daɗin kasancewa da tsohuwar, tare da ƙarajin ƙaunarta a zuciya da ɓargo.
Ansha ɗinkuna an kuma sha liƙi, abun mamaki harda gimbiya Su’adah da Adda Asmah a masu liƙi, dan Fulani ce ta basu shawarar suma suje suyi tunda su Hajiya Mufida sunyi. Karta yarda kishiyoyi su fita nuna iyayi ga auren ɗanta. Irin wannan sakacin tayi tun farko har Anne ta mallake mata shi a matsayinta na kaka.
Adda Asmah ta rungume Raudha da kanta ke a ƙasa bayan ta gama mata ruwan ƴan dubu-dubu. “Kinci nasarar shigowa cikin zuri’ar Taura ƴar KARUWAI”.
A bala’in firgice da rawar jiki Raudha taso janye jikinta. Sai dai Adda Asma ta sake matse a cikin nata jikin kasancewarta mace mai ƙiba. A kausashe ta cigaba da faɗin, “Sai dai hakan ba shike nuna Ni’imtacciyar inuwar da kike kwaɗayi keda Karuwan danginki bace kika shigo…..”
Ta saketa tana miƙewa tsaye da ƙyau, ƙasa Raudha tai da kanta jikinta na wani irin rawar tashin hankali. Adda Asmah ta saka hannunta dake cike da zabban gold da bangles ta ɗago haɓar Raudha. Idanunta ta tura cikin na Raudha da ƙarfin tsiya tana murmushi, wanda ya gansu daga nesa sai ya ɗauka wani maganar alkairi da yaba Raudha take. A kausashe da salon murmushin makircin tace, “BAƘAR INUWA ce da gwara ranar da kika baro da ita yarinya”.
Ta ƙare maganar da sakin fuskar Raudhan ta sake rungumeta sannan ta saketa. Ko tari gimbiya Su’adah batai ba. Sai dai fuskarta da ɗan murmushin ƙasaita. Kowa yasan halinta na girman kai shiyyasa babu wanda ya damu da yanayin nata, dan likin ma data fito taima amarya ya bama wasu mamaki. A haka dai taron ya tashi ƙwaƙwalwar Raudha a harmutse a kuma cushe. Dan tun kalaman Adda Asmah sai kawai ta koma ambaton sunayen ALLAH dan shine kawai zai iya zame mata mafita a zuciyarta yanzun.
Tana ɗakin Anne bayan ta idar da salla Fatisa da Fatima zaune kusa da ita suna magana take jiyo ƴar hayaniya ambaton sunan shugaban ƙasa dake amsa sunan mijinta a yanzun. Idanunta ta ɗan rumtse a hankali tana jan numfashinta zuwa tsakkiyar ƙirji. Buɗe ƙofar ɗakin na Anne da shigowar mayen ƙamshin turarensa cikin hancinta ya sata saurin buɗe ido. Ƙirjinta ya ɗan harba saboda haɗa ido da sukai, dan tuni su Fatisa sun miƙe daga kusa da ita suna gaishe shi. A taƙaice ya amsa musu yana janye idonsa akan wadda har yanzu bama gama tantance kamanin nata yay ba. Indama ace su Fatima kama suke da ita to da wahala ya iya ganeta a yanda ya shigo ya samesu.
Tuni Raudha ta janye idanunta tai ƙasa da kai, sai dai jin fitar su Fatisa a ɗakin yasa taji kamar ta miƙe ta zura da gudu ta bisu su fita tare.
“I..ina y..yini”.
Ta faɗa cikin rawar harshe da in’inar da batasan daga ina ta samota ba lokacin da take jin tamkar takunsa na kusantota, duk da kuwa akwai lallausan Turkey carpet da ƙamshin daya yake fitarwa ma na musamman ne tamkar ba ɗakin tsohuwa ba.
“Assalamu alaikum”.
Muryar Anne da buɗe ƙofar suka katse sauraren Raudha da ga jiran amsa gaisuwarta gareshi. A hankali ta saki numfashin data riƙe a tsakkiyar ƙirjinta tamkar mai jiran ace ar ta haɗiye abinta cikin ciki.
Shugaban ƙasa Ramadhan dake ƙoƙarin ƙarasawa saman ɗaya daga kujera biyun dake a bedroom ɗin na Anne ya kai zaune yana amsa mata sallamarta. Yayi matuƙar ƙyau cikin shadda ash color data wadatu da jiƙaƙen ɗinki da ƙyawun surar da ALLAH yay masa. Da gani basai an faɗaba maiƙonta kawai ya isa amsa ga mai hasashen kuɗinta.
“Wai sai yanzu ake ganinka a gidan nan Ramadhan?”.
Anne ta faɗa tana kaiwa zaune bakin gado gab da Raudha dake a ƙasan carpet. Dan ko Anne tace ta hau gadon bata iyawa saboda kunya.
Ɗan murmushin daya tsaya masa iya kumatu yayi yana duban tsadadden agogonsa Breitling dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa Silver. “Anne barci ne naji zai halakani shiyyasa na kulle kaina kawai”. Ya faɗa cikin muryarsa mai faɗi da kauri. Sai dai a hankali yake maganar tamkar baya so.
“To ALLAH dai ya rabamu dayin ragon shugaban ƙasa anan, Aminatu sai kin dage da addu’a kam”.
Yanzun ma gajeren murmushi kawai yayi, sai dai ambaton sunan Raudha da tayi ya sakashi ɗan dubanta ya ɗauke ido. A ransa ko rayawa yake (a haka dai tamkar mutuniyar kirki, sanin gaskiyar al’amarinta sai ALLAH). Dan shi tozali kawai da yay da Mal. Dauda jiya ya sake gaskata maganar su Maa.
“Abinci fa?”.
Anne ta katse masa tunani. Agogon nasa ya sake kallo yana ɗan furzar da iska. “Idan da fura kawai a bani ya isa Anne”.
“Fura kam tayi kaɗan ga wanda baiko karya ba. Banajin ma kaci wani abu daren jiya”.
“To Anne ya zanyi”.
Ya faɗa a yanayin nuna rauni kamar na shagwaɓa. Kasa daurewa Raudha tayi sai da ta saci kallonsa. A ranta tana faɗin (humm). Oho baima san tanayi ba. Dan telephone dake kan table Anne tai amfani da ita wajen sakawa a kawo masa abinci. Babu jimawa kuwa ɗaya daga cikin amintacciyar ma’aikaciyar gidan ta kawo masu damammiyar fura datasha haɗi da gasashen naman rago mai romo, sai shawarma.
Babu ko jin nauyin Raudha dake zaune ya zare agogo ya gyara zama. Anne ta duba Raudha da keta wasa da zoben hanunta cikin kulawa. “Aminatu kema ai ba abincin kikaci ba, tashi kije kuci ko ƙyaji ƙarfi”.
Da sauri Raudha ta girgiza kanta. A ranta tana faɗin (tab ɗi ni zanci abinci da shi?) a fili kam sai tai saurin faɗin, “Anne na ƙoshi wlhy”.
Lallaɓata da lallashinta Anne ta shigayi amma ta dage ta ƙoshi, harda ƴar ƙwallarta da taso bama Anne dariya ma.
Duk da a kunnensa suke duk zantukan nasu ko nuna alamar yama san sunayi baiyi ba. Furarsa da nama yaketa ci a nutse hankali kwance. Hakan yasa Anne taɓe baki tana dubansa, cikin ɗan tsokana tace, “Da yake mai abincin ma marowacine Aminatu ai kinga yayi shiru dan kar aci”.
Yasan da shi take, dan haka ya ɗago idanu yakalli Annen. Cikin yamutsa fuska yace, “Kai Anne, kunzo kunce zakuci ne na hana?”.
“Ko bakace ba ai baka nuna alamar kana so aci ba”.
Murmushi kawai ya ɗanyi ya cigaba da cin abincinsa batare daya ƙara magana ba. Yan kammalawa kuma bai ƙara ko mintuna uku ba ya miƙe wai zaije su Ibrahim na jiransa a masaukinsu. Dan in baije yanzu ɗin ba da wahala ya sake samun dama. Bai kamata kuma ace sunzo dan shi ba amma yay musu wahalar gani duk da sun san yanzu da da akwai banbanci tunda shiɗin sunan shugaban ƙasa yake amsawa.
Addu’ar dawowa lafiya Anne tai masa, hakan yasa itama Raudha a hankali ta furta ALLAH ya tsare batare da tayi tunanin shi da Annen zasu jita ba. Sai dai kuma amsawar da Anne tai da “Amin ya rabbi Aminatu” ya sata fahimtar tajita. Shiko bata tunanin ya amsa harya fice abinsa………✍

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button