BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

    Matashiyar budurwa da zata iya kaiwa shekaru goma sha shida zuwa sha bakwai a duniya ta fito da ga ɗakin da Asabe ta fito ɗazun. Sanye take da dogon jijjab har ƙasa alamar salla tayi. Tana tsananin kamanni da Asabe tamkar tayi kaki ta ajiye. Cikin ladabi da nutsuwa takai duƙe tana faɗin “Abbanmu barka da dawowa? Ansha ruwa lafiya?”.
    “A gidan ubanwa nasha ruwan? ke kuma zaki sake ɓatan rai!”.
  Ƙasa tai da kanta ƙwalla na ciko mata ido, dan tanada zuciya matuƙa, sai dai tana da ƙoƙarin dannewa musamman akan mahaifanta guda biyu da halinsu baida maraba da girman haihuwar ƙasan gada.
  “Kayi haƙuri Abbanmu, dama zance maka nice na amso lemon a wajen jabiru”.
  “Buhun bu*a'uban nan kayyasa (????????????‍♀️????????). E lallai na zama ɗan iska haihuwar ƙasan gada kuwa da gaske. To ubanwaye ya aike ki!!?”.
    Yanda yay maganar a tsawace ya sata runtse idanunta da ƙarfi tana haɗe kukan dake neman taso mata. “Kayi haƙuri Abbanmu, babu wanda ya aike ni. Babu abinda zamuyi buɗa baki ne da shi shiyyasa na amso mana, nace masa kaine ka aikoni dan inba hakaba bazai bani ba”.
    Sake maƙurewa yay jikin bango tamkar tsohon ƙadangaren da ciwon sanyi ya buge yake shaƙo ƙamshin mutuwa.
    “Ni DAUDA naga haihuwar jaraba jinin ladin ƙasan gada. Niko wai yaushe lalacewata takai har hakane a gidan nan ne wai? K dan uban uwarki har ni zaki laƙawa sheri ina fama da ƙishirwar azumi na? To wlhy ki rubuta ki ajiye sai kinyi nadamar hakan daga ke har uwar taki, dan nasan itace ta aike kin ta noƙe......”
   “Kai Dauda sauraramin. To kodai dama dani ɗin kake bada itan ba da ka haifa? To wlhy ahir ɗinka wahainiyarka ta kiyayi ramata, inba hakaba kaima kasan na fika tsiya da tujara. Ka buga ƙafa kamar na karen mafarauta ka barmu cikin yunwa ga ruwa za'a sha saboda kafi kowa iya babbaku da tujara dan kawai an anso abin nera dubu guda injika shine zakazo tsakar gida gaban magauta da ƴan bani na iya kana zazzage min. To wlhy ina dai-dai da kai”.
  “Tsssss!!!!” 

Kakeji wani irin gigitaccen mari mai ƙara da alamar zaiyi ɗan karen zafi ya sauka bisa kumatun budurwar nan dake tsugunne ranta a matuƙar jagule, ta amshi laifin ne dama dan gudun karsu raba halin da suka saba a gaban kishiyoyin mahaifiyar tasu. Amma sai gashi dabarar tata batai ba.
Ta dafe kuncin jikinta na rawa. “Wannan marin na hanani zaman buɗa baki wajen Jabirunne da kikayi ke kuma. Saura na ƙaryar da kikaimun itama. Ke kuma Asabe yanzu banda lokacin mai lokacinki, amma ina nan tafe kanki..” ya ƙare maganar yana nuna Asaben.
Caraf Asabe tasha gabansa tana mazurai. “Wlhy ka sake taɓamin yarinya sai na rama mata. Kai barfa ganin uwa ban son ta, son kayana nake ras, idan kuma kaji ƙarya sake taɓata dai-dai nake da kai, danni a yanzu nake da naka lokacin. Banda kai dai kana cikin mazan da sai an tsoma kansu a wuta an ɗauraye musu zunibi ka fita baka ko bamu geron kunu ba dan mun samawa kammu mafita kazo har kana tara jijiyar wuya. To bara kaji ni ba matanka bane daka maida sakarkaru, idan kaji ƙarya kuma sake gwada bugunta ka gani, kaima kasan wacece Asabe autar hajiyar birni shalelen bahago dan mai…….”
Sai kuma taƙi ƙarasawa ta balla masa harara, ganin ya juya fuuuu zai sake ficewa. Taja tsaki da faɗin, “Da ka tsaya mana kaji ko zaka iya latsawa ka kwana lafiya ɗan gidan abun kwari mai yawo da tsinuwar uwa bisa kai”.
Wani irin kuka budurwar nan da har yau ke duƙe ta fashe da shi. Cikin masifa Asabe ta juyo kanta takai mata shiru dan tasan minene dalilin kuka. “Dan ubanki tashi anan kona huce kaf haushinsa a kanki mara mutunci. Ko dan dai nice jinin asara sai na zauna yana cin zarafina gaban kishiyoyi na masa shiru saboda ga jikar ta-salla wadda ta haɗiyi ƙur’ani dan haƙuri. K nifa bar ganina haka zan iya kakkaɓar daku nai gaba dama tausayinku ne yasa nake zaune a wannan gidan da tsiya taima katutu abincima sai anyi kwarakarsa a maƙwafta dan lalacewa”…………✍️

Tofa jama’a bana ina mukazo haka? Ina alƙalamin namu ya kwasomu ya kawo?????????.

A cikakken Littafin BAƘAR INUWA kawai zamu samu wannan amsoshin. Naira ɗari uku me kacal, tare da duk zafafa biyar naira dubu ɗaya ne kacal. Karku bari ayi babu ku. Dan bakuga komai ba. Yanzu aka fara sharar filin wasan. Cakwakiyar sai wasan ya kankama????. Dan duk wanda akayi babu shi ALLAH yayi missing????.

Taku
Bilyn Abdull ce????????*


1~ KUFAN WUTA????
Safiyya Huguma

1~ BAQAR INUWA????
Billyn Abdul

1~ RAYUWAR MACE????
Hafsat Rano

1~ MASARAUTA????
Miss Xoxo

1~ NOOR ALBI❤‍????
Mamuhgee

Guda 1????300
Guda 2????400
Guda 3????500
Guda 4????700
Guda 5????1k

ZAKU BIYA KUDINKU ANAN????????

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya????????

09032345899

KATIN MTN????????

09166221261

TEAM ZAFAFABIYAR


BAƘAR INUWA…

https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09
     _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar????????????????????????_

YADDA AKE BUDE ACCOUNT A AREWABOOKS

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za’a cike Form din kamar haka: –

Enter your name: (Cikakken sunanki)

Enter your mail: (Email ɗinki)

Enter an username (Sunanki)

Enter your password: ( misali 12341234)

Confirm password: (misali 12341234)

Sai a taɓa Sign Up shikenan an buɗe account a ArewaBooks????????????.

Continue with Google – Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za’a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

Register – Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.

AREWABOOKS LINK kai tsaye

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3

Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com

Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App… Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine.

MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER

+234 903 177 4742

Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan????????????????????????.

ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????
Typing????

     *_????BAƘAR INUWA....!!????_*
              _{Gara rana dake}_




       *_Bilyn Abdull ce????????_*

“Kamar yanda na faɗa tun farko labarin, Littafin BAƘAR INUWA ƙirƙiraren labari ne, dan haka duk wani sunan gari da zai iya zuwa cikin labarin shima ƙirƙirarsa akayi, komai ma da zai iya shigowa cikin labarin ƙirƙirarsa akayi. Baida alaƙa da wata ƙasa ko wasu mutane. Koda kuwa kaji abinda ya shafeka ko yay kamanceceniya da kai to ka ɗauka kamarce kawai yayi bawai yana da alaƙa da kai bane ba. Dan Bilyn Abdull bata sanki/ka ba balle ta dasa alkalaminta akan ka. Rubutu ne kawai nayi dan nishaɗi, faɗakarwa, ilimantarwa, harma wani abun zai iya zuwa muku da ban haushi saboda wannan karon ma a haka alƙalamin nata yazo.????????????


Episode 2

ƘASAR NAYA

………(DALLO STATE): HUTAWA L.G.A. Da gudu budurwar ta miƙe ta shige ɗaki tana cigaba da kuka, ganin a yanda ta shigo ta wuce tana kuka, ƴammata biyu da za’a iya kira tagwaye kuma yayunta suka kwashe da dariya suna faman taɓe baki da ɗaga kwalbar lemonsu suna ɗaɗɗaka hankali kwance.
Sai kuma suka maida dubansu akan Asabe data shigo tana cigaba da zazzaga ruwan tujara.
“Kina wuta momyn mu!!????????”.
Ƴammatan suka faɗa suna mata jinjina da kwashewa da dariya a karo na biyu. Zama tai kusa da su taja kwalbar lemo guda tasa haƙori ta ɓalle murfin tana huci. Batare data cema ƴammatan komaiba ta ɗaga tasa a baki, kamar ƙiftawar ido sai gashi ta zuƙi kusan rabi sannan ta dire tana sauke ajiyar zuciya.
Wadda tafi hasken sosai dake kallon kwalbar lemon ta ƙyalƙyale da dariya da faɗin, “Mommy sunan wannan shan lemon naki shan huce takaici”.
Tsaki tayi tana gyara zama da ɗaukar tsokar nama dake gabansu ta danna a bakinta. “Yo wannan uban naku inba shan huce takaicin kakema ni’imar da ALLAH yay maka ba ai tuni yake tsotse maka ruwan jiki, ga waccan mara mutuncin dake abu uwa ba jinina ba.”
“Yo Mommy bayan kamanin da take dake ai sai muce muma ko’an canja miki ita ne a asibiti? Muda yakamata muyo kamanin naki hegiyar mai taurin kan tsiya da kicifi duk an haɗa ita an bata.”

   Duk abinda suke budurwar nan na jiyosu daga uwar ɗaka. Dan haka ta sake fashewa da kuka zuciyarta na mata ƙuna da raɗaɗin halin iyayen nata da ƴan uwanta. Tun tana ƴar ƙaramarta takejin ana zagi da la'antar halin mahaifanta a cikin layinsu, har gashi yau tsahon shekara goma sha bakwai bataji komai ya canjaba sai ma abinda ya ƙaru a dalilin ƴan uwanta guda biyu da kullum cikin janyo masu wata sabuwar maganar suke. Duk da dai itama ta fara rashin ji mai kama da nasu ALLAH ya tarota ta nutsu sanadin malamin islamiyarsu sayyadi Abubakar.
        Hannu tasa ta share hawayenta da gyara kwanciyarta zuwa rufda ciki, duk da yunwa dake cinta saboda azumin data kai hakan bai dameta ba, ta lumshe ƙyawawan idanunta data gada wajen mahaifiyarsu Asabe a hankali Murmushi na suɓuce mata mai haɗe da hawayen tausayin kanta na rasa Abubakar. Tabbas zuwa yanzu ta yarda ta rasashi, ya tafi har abada bazai sake dawowa gareta ba kamar yanda iyayensa suka faɗa. Wannan ciwone a rayuwarta mafi muni da har abada bata tunanin warkewarsa, dan ya zama gyambo a ƙirjinta. A tsaye take da sunanta, amma a zuciya ta jima da mutuwa tun sanda iyayen abubakar suka saka ya fita a rayuwata.
    “Ya ALLAH ka ɗauka raina inhar zaifi zama alkairi a gareni”. 
   Ta faɗa cikin kuka mai ban tausayi da tsum rai.


   Sunanta shine *_AMINATU_* sai dai ana kirana da *_RAUDHA_* sakamakon sunan kakarta da taci wadda ta haifi mahaifinta. Kamar yanda kukaji a bakin mahaifiyarta sunan mahaifinsu DAUDA, sai dai ana kiransa ɗan-azumi. Tun a ƙuruciyar mahaifinsu mutum ne marajin magana. Al'amarin nasa ya sake turewa a lokacin daya fara bin wani ɗan anguwarsu driver matsayin karen mota. Kamar yanda kakarsu ta taɓa basu labari tarbiyyar Abbansu da rayuwarsa ta sake gurɓacewa a dalin wannan bin mota, dan bai rufa shekara ba a hanun uban gidansa sai shima ga tashi motar. Tun yana jan ƙaramar mota harya koma babba irin ta company ɗin nan da ake ɗaukar kaya trailer. Fara jan motar trailer yasa albarka a hanunsa, dan babu wani tazara da hakan kuɗi suka fara zauna masa. Da ƙyar ya yarda ya auri matarsa ta farko Nafisa, wadda ɗiyar ƴar uwace ga kakarsu. Nafisa tanada matuƙar haƙuri, hakan yasa bata taɓa kai karan ɗan-azumi ba a duk gallazawa rayuwarta da yakeyi. Basu rufa shekara da aure ba ya auro sabuwar amarya mai suna Larai. Larai fitinanniyar mace ce mai kauɗi da rashin barin kota kwana. Yanda ta hana Nafi zaman lafiya haka ta hana Mal. Ɗan-azumi. Mahaifiyarsa tayi-tayi ya saketa yaƙi. Babu jimawa da auren Larai Nafi ta haihu, itama Laran bata cika shekara ba a gidan ta haihu. Zamansu ya cigaba da kasancewa babu wani daɗi, yayinda Mla. Ɗan-azumi ya cigaba da sake kutsa kai a yawon tazubar. Dan kuwa a kaso biyu bisa ukun kuɗin da yake samu suna tafiyane ga neman mata da ashararancinsa. Sune manyan ƴan duniyar duk wani gari na baɗala da ire-iren gurare na ashararanci da akasan direbobi na kakkaɓe dukiyarsu a wancan zamanin. 
 Nafi ce kawai ke damuwa da halin banza na maigidan nasu, Larai ko ko'a kwalar rigarta tunda akwai kuɗi, dan ita kam dama sune matsalar rayuwarta tunda itama acan ya kwasota a tashar ƴan tazubar ɗin. Suna da haihuwa hurhuɗu Nafi da cikin na biyar Ɗan-azumi ya sake sabon aure daga birinin Loss. Ba kowa ya auroba kuwa sai Asabe ɗiyar *Ɗahare (Hajiyar birni)* mai tuwo-tuwo a ƙarƙashin gada. 
   Ɗahare mace ce mara mutunci da duk wani shege daka sani ɗan yankin nan dake zaman tazubar a Loss ya san da zamanta. Asalinta a ƙasar saudia take tana TIKARI tsahon shekaru, a wani yaya da akayo alƙawarin ALLAH ya cika aka yayota zuwa ƙasar Ghana. Kasancewarta shaharriya acan ɗin ma yasata ko NAYA bata dawo ba ta sake komawa. Dan kuwa yaranta nacan su huɗu wanda ta haifa da wasu larabawa biyu, sai dai dukansu aure tai da su. Na farko rasuwa yay ya barta da yara biyu mata *Samiha da Hannah*, na biyu kuwa rabuwa sukai saboda Ɗahare ta wuce dukan tunanin mai tunani. Kwasotan ma da akai shine yay shunenta dan yana so ya sace yaransa dake hanunta su biyu. Sai dai kuma ta koma domin tanada hanya sosai. Komawar Ɗahare da biyu ne. Na farko da ƙudirin ɗaiɗaita rayuwar balaraben nan ne uban ƴaƴanta guda biyu, *Halima da Nasiba (Asabe)*. Na biyu ƙudirin rabo ƴaƴanta biyu daga hanunsa ne, dan labari yazo mata tana barin ƙasar yana zuwa ya kwashesu yabar wanda ta haifa da mijinta na farko. Kamar yanda ta tsara kuwa hakance ta kasance, dan kuwa dai duk da balaraben nan bawani mai shaharren arziƙi bane, dan kuwa baƙauyene ma. Sai dai yana da arziƙin dabbobi matuƙa na kiwo dana tatsar madara. Duk irin makircin da Ɗahare ta ƙware sai da tabi wajen ganin ta rabashi da wannan dukiyar, jin ana bincikenta a kama yasata tattaro duka ƴaƴanta huɗu ta baro saudia bisa taimakon wasu mutanenmu dake can masu ɗaure musu ƙugu. Koda ta dawo gida kuma babu inda ta yada zango sai tsakkiyar birnin jihar Loss. Inda ta fara tuwo-tuwo yaranta huɗu ƴammata zagaɗa-zagaɗa na taimaka mata.
     Game da ƴaƴan nata tamkar kumbo kamar kafinta ne. Dan kuwa a kaf halayyarta babu wacce suka bari musamman ma Asabe mafi ƙyawun fuska da ƙyan sura a cikinsu. Dan kuwa ƙyaƙyƙyawar balarabiyace da kallo guda bai isar mai dubanta. Dan-danan alhazan birni suka fara wawarsu da sheɗanci, dan kuwa inma kace da aure kazo garesu to tabbas kuwa Ɗahare da sunanta ya koma Hajiyar birni ba daga maka kafa zatai ba. Zatai maka wankin babban bargo tace bata gama more wahalarta ba za'a tura mata ƴa cikin ɗaki, sam bata yarda ba.
   Ko'a jikin ƴaƴan, dan suma basu buƙatar auren sai harkar neman kuɗin kawai, sai dai banda Asabe. Dan duk kauɗi da rashin mutuncin Asabe ita dai tafi buƙatar aure sama da rayuwar barikin. Bawai batayi bane, a'a bata cika sakin jiki tayi ɗin bane tamkar wata karya. A wannan halin ALLAH ya haɗata da Mal. Dauda ɗan-azumi, wanda yake tsaka da tashen kuɗi. Gashi shima masha ALLAH ƙyaƙyƙyawan bakatsine bafulatani. Dandanan ya fara sakar mata kuɗi na hauka, tare da zazzafar soyayya dan kwashi dai tunda ya ɗana sau ɗaya yaji bazai iya haƙuri yabarta ba sai ya aureta. Duk wani shigi da fici irin na ƴan bariki kwararru ɗan-azumi yayi ga malamsa na masa aiki, cikin ƙanƙanin lokaci ya rikita zuciyar Asabe tace inba shiba sai rijiya mai gaba dubu. Hankalin uwarta ya matuƙar tashi dan tafi kallon sa'arta jikin Asabe fiye da sausan ƴaƴanta saboda ƙyawu da ALLAH ya bata na larabawan asali da ko'a cikin ƙasar saudiyar abin kallo ce. Ganin Hajiyar birni zata bashi matsala itama ya rufe mata baki ruf. Babu ɓata lokaci aka shiga hidimar bikin daya bama kowa mamaki.
  An ɗaura auren Asabe da Dauda, aka ɗakko amarya zuwa garin hutawa dake a jihar Ɗillo inda Dauda ke zaune da iyalansa. Ƙyawun Asabe yasa ake layin zuwa ganinta har wasu na faɗin ɗan-azumi ya auro aljana wadda zatai maganin sheɗancinsa. A zahiri ba aljanar bace, amma bakin mutane kam ya bisa dan Asabe ta zame masa *BAƘAR INUWAR..* daya gwammaci aljanar ya aura. Asabe ta take Larai rashin mutunci ta shanye. Dan ita ko kusa ko alama bata shakka ko kunyar tsige Dauda tas a bainar nasi ko gaban ƴaƴansa balle uwarsa. Inhar zai faɗa mata cuta saita mayar masa da mutuwa koda zata kaisu da dambe a tsakar anguwane. A haka ta samu ciki, inda ALLAH ya azurtata da haihuwar ƴaƴanta mata ƴan biyu masu tsananin kamanni da DAUDA. dan ko kaɗan basu biyo Asabe ba sai dai ace ko na jini dole ka gani a fisge. Ko kaɗan bata damuba, dan kuwa ƴaƴan soyayya ma take kiran ƴan biyun nata mata da sukaci sunan Faɗima da Fatisa. Bayan haihuwar su Fatisa ko wata uku bataiba ALLAH ya sake bata wani cikin, wanda shima ta sulluɓo ƴarta mace mai tsananin kamanni da ita a wannan karon. Dan kuwa ƴar nan duk da jinjirace duk wanda ya kalleta sai ya sake duba. Dan ta wani fannin za'ace ta hado ƙyawune na uwa da uba. Saboda ta ɗakko ɗan duhun fatar Dauda da hasken mahaifiyarta. Idan ka kalleta kai tsaye zaka kirata half cast kawai. Itako taci suna *Aminatu* asalin sunan inna kenan mahaifiyar dan-azumi. Sai dai kuma Asabe tace ana ce mata *Raudah* dan duk kishiyar data faɗar mata sunan uwar miji a gidan ranar za'aga ƙarshen bala'i da jidali. Bayan haihuwar Rauda Asabe ta sake haihuwar mace itama mai suna Yasmin. Itama dai kamanni biyu ta ɗakko na Asabe da Dauda. Sai dai itama baƙace sosai ba kamar Rauda ba.
      Basai an faɗa makaba, dan kuwa batun tarbiyyar babu ita ga ƴaƴan Asabe a gidan, tasu ta fita daban data saura. (Ƴaƴanmu kan fara koyon ilimine daga ɗabi'unmu iyaye, dan haka sai mu kula dan ALLAH kodan gaba da zasu kai girma su gallabemu). Sam ƴaƴan Asabe ƴaƴane na rashin ƙwaɓo a gidan, duk taɓararsu babu ubanda ya isa nuna musu yatsa har a wajen Dauda. Dan har gori yakema sauran matansa akan basu taɓa haifa masa ƙyawawan yara ba balle mai kama da shi, dan su kam ƴaƴansu tamkar haɗin baki duk kamanninsu suka kwaso. Ko aike babu wanda ya isa aiken ƴaƴan Asabe sai ita, ita ɗin ma sai sun gadama suke zuwa. Hakan kuma bazaisa ta nuna ta damu ba. Hatta da Raudha ma haka ta taso a cikin nasu sai a hankali, dan itamadai halin ƴan uwan natane tsaf sai dai ma ace ta ɗarasu da shegen miskilanci da baƙar zuciyar tsiya da jan magana, dan kullum cikin faɗa take da yara harma da manyan. Sai dai kuma tanada ɗan sauƙin kai ta wani fannin kaɗan idan taso, ba komai ya jawo rashin jin Raudha fin na sauran ƴaƴan Asabe ba sai gatan da Mal ɗan-azumi ke mata a gidan fiye da kowa dan tana da sunan mahaifiyarsa.........✍️

????karfa ku bari ayi babu ku, dan ba’a far komai ba har yanzun????????????.

ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA????????????????????

1~ KUFAN WUTA????
Safiyya Huguma

1~ BAQAR INUWA????
Billyn Abdul

1~ RAYUWAR MACE????
Hafsat Rano

1~ MASARAUTA????
Miss Xoxo

1~ NOOR ALBI❤‍????
Mamuhgee

Guda 1????300
Guda 2????400
Guda 3????500
Guda 4????700
Guda 5????1k

ZAKU BIYA KUDINKU ANAN????????

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya????????

09032345899

KATIN MTN????????

09166221261

TEAM ZAFAFABIYAR????????????????


BAƘAR INUWA…????????

https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09
     _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar????????????????????????_

YADDA AKE BUDE ACCOUNT A AREWABOOKS

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za’a cike Form din kamar haka: –

Enter your name: (Cikakken sunanki)

Enter your mail: (Email ɗinki)

Enter an username (Sunanki)

Enter your password: ( misali 12341234)

Confirm password: (misali 12341234)

Sai a taɓa Sign Up shikenan an buɗe account a ArewaBooks????????????.

Continue with Google – Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za’a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

Register – Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.

AREWABOOKS LINK kai tsaye

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3

Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com

Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App… Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button