BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

 Wata irin muguwar hajijiyace ta fara ɗibar Ramadhan. Dan dama can shi bayason ihu, musamman idan yana akan gaɓar bacin rai tuni ake samun matsala kansa ya nema juyewa saboda tsananin yanda ƙwalwar kansa ke kasa ɗaukar tashin hankali mai shallake tunani. Lokacin da yana yaro idan hakan ta faru ansha cemusu yanada aljanu ne masu ƙarfi sosai. Sai dai basu taɓa yarda ba dan su sam basu cika ɗaukar waɗan nan abubuwan da muhimmanci ba (kamar yanda kowa yasan ɗan boko????????), sai dai hakan baya hana duk lokacin da abu ya faru makamancin matsalar ta biyo baya Anne ta zauna tai masa addu'a a ruwa da saman kansa har sai ya samu nutsuwa sannan. Amma abin mamaki zai iya yini yana ajiyar zuciyar wannan ɓacin ran, ko kuma ya yini a ɗaki yana barci. Sannan sai ya haɗa kwanaki biyu zuwa uku baiyi magana da kowa ba. sai dai ya samu wajen ruwa ya zauna, ba kuma zaici abinci ba duk da kasancewar sa ma'abocin son abinci sai Anne ta takura masa shan abu mara nauyi kamar su fura yogurt, fresh nonon shanu ko na raƙumi da makamantansu. Dan yana tsananin son madara da dukkan nau'ikanta a rayuwarsa. Bayan aurensa da Amnah idan ransa yay irin wannan ɓacin yakan hucene a kanta ta hanyar yin tarayya da ita yanda zata jigata har sai an kwantar da ita a asibiti abinka da sikilla. Dan likitocin kance ko mai lafiya akaima irin wannan kamun babu shakka zataji a jikinta balle Amnah ɗin. A duk lokacin da fushin ya sauka yakan shiga damuwa idan ya kalli yanda ya fiddata hayyacinta. kai wani lokaci ma har saida akai mata ɗinki tsabar lamarin Ramadhan yana bukatar addu'a????????. Amna kam tana jin jiki da shigar Ramadhan irin wannan yanayin, sau biyu yana sakata ɓarin ciki. da tana raye na tabbatar zatace hakan shine mafi girman tashin hankali a rayuwar aurenta da Ramadhan ɗin, shiyyasa duk wani fushinsa take gujewar wanzuwarsa a karan kanta.
   Yanda ya fara juya kai jijiyoyin na tashi sama da maƙogwaronsa dake kai kawo a wuyansa, gashin kansa na mimmiƙewa yasa Bappi fahimtar mike shirin faruwa. Yasan Ramadhan bazaice komaiba, dan shi mutum ne mai tsananin tsoron saɓama iyaye, shiyyasa daya dage akan bazai dawo NAYA ba a shekaru biyar ɗin nan abun ya basu mamaki matuƙa, dan duk rintsi baya ƙetare maganarsu.
Da sauri Bappi ya girgizama Alhaji Basheer kai yana miƙewa ya riƙo hannun Ramadhan daya fara ƙoƙarin ɗaga ƙafa yana jujjuya kansa cikin tafukan hannunsa daya riƙe kan nasa. Tuni idanunsa sun rufe ruf saboda wata baƙar hajijiyar da yake gani falon na juya masa da wani irin shegen gudu.
  Babu abinda ke maimaita kansa a kwakwalwar Ramadhan da zuciyarsa sai *_“Ramadhan!! Nace ka fita a gidan nan yanzun nan!. Bana son sake ganin wannan fuskar taka!!”._* da Pa ya faɗa.
  “Zan tafi Pa, bazan sake nuna maka fuskar nan ba nayi alƙawar.....”
 “Shut up!!”.

Bappi ya faɗa da ƙaraji shima yana katse Ramadhan ɗin bayan ya fisgosa ya zube a saman kujerar kusa da shi. Juyawa Alhaji Basheer Taura yay a fusace yabar falon, shi kansa wani irin jiri-jiri na neman fara ɗibarsa. Sai hakan yasa yakejin yana tafiya tamkar akan iskar dake kaɗawa har zuwa sashen nasa. Bai iske gimbiya Su’adah ba. Da alama taje shirin barci. Dan haka yay kwanciyarsa, koda ta shigo bayan kusan mintuna talatin da kwanciyarsa bai motsaba. Hakan yasa tai tunanin ko yayi barcine. Sai kawai taja bargo ta lulluɓa masa bayan ta rufe wasu a murafan windows ɗin dan iskar ta fara yawa.

WASHE GARI

     Da mamaki kowa ya tashi yaga Ramadhan a gidan. Sai dai a yanayin da yake na hawa saman dokin zuciya yasaka bakin yaran gidan rufewa ruf. Dan ko kallonsa kayi bakaso sake ganiba fuskar tamkar zatayi aman wuta????. 
     Gimbiya Su'adah ce kawai ya iya tankama tambayarta itama a taƙaice, dan ita firgitama tayi da ganin nasa. Har zuciyarta na raya mata kodai da gaske Ramadhan ɗin nada aljanune wai?.
 Ko amsa ɗaya bata samu daga tarin tambayoyin da take jera masa ba, sai ma miƙewa yay yana sanar mata cewar zai koma America.
  “America!”.

Ta maimaita da yanayin ruɗani da tashin hankali. ita dake murna ɗanta ya dawo gareta kuma. Kafin ta sake cewa wani abu yayo waje. Dan dama a bedroom ɗinta ya sameta kasancewar ta duba an kammala shirya abincin breakfast na Pa tazo dan ta shirya, sannan taje ta tadashi a barcin daya ɗan koma na safe bayan dawowarsa masallaci.
Har ya fice a sashen baki ɗaya bata dawo hayyacinta ba. Dan da alama sumar tsaye tayi kawai.

“Shiga mota muje”.
Bappi ya faɗa idonsa akan Ramadhan daya fito daga sashen iyayen nasa a wani irin yanayi. Duk da alamu sun nuna yayi wanka ya canja kaya hakan bai hana fuskarsa bayyana yanayinsa na jiya ba. Sanye yake cikin wani tattausan tissue yadi da basai ance komai game kallo ba wajen hasashen irin kuɗin daya lasa na sayensa dana ɗinkinsa. Duk da simple style ne a jikinsa hakan bai hana bayyanar tsadarsa da fitar ɗinkin ba a bisa ƙyaƙyƙyawar ƙirarsa ta mazantaka da ƙuruciya ba, ga shi baƙi sai farar fatarsa ta sake haskawa. Babu alamar sumar kansa ta samu gyara yau tsabar yanda ta hargitse, sai dai hakan bai hana ƙyawunsa bayyana ba harma ya ɗauka hankalin wasu mutane koda ba kowaba.
A tunaninsa airport ɗin zasuje, kamar yanda ya sanarma Bappin yau zai koma bayan sun fito da ga sallar asuba. Dan haka babu musu ya shige inda M. Adamu ya buɗe masa kusa da Alhaji Hameed Taura (Bappi). A wata jiƙaƙƙiyar mota data gama haɗuwa. A tsammaninsa ƴan kayan buƙatarsa dake cikin bag an riga an fiddo masa tuni………✍

Tofa ina Bappi zai kai mana wannan young tiger ɗin mai kama da barkonon noman ranin?????????.
Typing????

Episode 14

………..Sai da motar ta tsaya a harabar asibitin sannan Alhaji Hameed Taura ya dubi Ramadhan da ke kwance jikin sit ido a rufe. Sai faman jan numfashi yake a gwame alamar ransa har yanzu a ɓace yake. Sumar kansa yayma kallon second goma ya sake ɗauke kansa, batare da yace komai ba ya miƙa hannu a booth ya ɗakko ledar dake ajiye da huluna a ciki ya duba wadda yake zaton zata dace da shigar Ramadhan ɗin ya ɗakko. Dama shekaran jiya ya sayesu domin Ramadhan ɗin, sai dai ya mantasu ne a motar bai kuma sake shigartaba sai yanzun.
Kari yay mata sannan ya ɗaura masa akan hannu, hakanne yasa Ramadhan buɗe idanunsa da suka ƙanƙance da canja launinsu.
“Saka hular nan muje”.
Komai baice ba ya ɗauka hular ya ɗora saman kansa kawai batare da duba tayi ko bataiba. Kai Bappi ya ɗan girgiza da riƙo hannunsa ganin zai fita. Batare da shima yace masa komai ba ya gyara masa ita ta zauna ɗas tamkar dan shi akayita. Sosai ya fito asalinsa na bahaushe cikakke. Wanka na ɗaukar jikin Ramadhan ko wanne irine. Sai dai a duk lokacin da ya saka manyan kaya yakan zama babban mutum da cikar kamalarsa ke daɗa fitowa a zahiri ga masu kallonsa. Sai kaga yayi maka wani irin kwarjini dake saka mutane jin shakkarsa da bashi girma koda basuyi niyya ba.
Duk da ya fahimci asibiti sukazo bai tanka ba har suka shigo ɗakin da Raudha ke jinya, police ɗin da president ya bamma Alhaji Hameed Taura biye dasu tamkar jela. Ko’a dacan da ƙuruciya Alhaji Hameed baya son bodyguard tare da shi balle yanzu da tsufa yay masa kamun kazar kuku, yake ganin rayuwar ƙiris ta rage masa ma.
Bappi ne kawai yay sallama a zahiri duk da yasan babu kowa a cikin. Ramadhan kuwa a saman laɓɓansa yayi yana biye da Bappin tamkar dole. Ɗaki ne babba dake ɗauke da komai na buƙatar mara lafiya ɗan gata. Sai Nurse ɗaya dake tare da Raudha data farka tun asubahin yau. Tun ɗazun doctor ya shigo yay mata dukan abunda ya dace tare da dubata. Aka kuma bata abinci taci tare da magunguna. Yanzu haka idanunta biyu tana kallon television ɗin ɗakin da ake nuna wani wasan salla na yara daya ɗauke hankalinta, yayinda Nurse ɗin ke zaune tana faman latsa wayarta.
“Barkanku da zuwa ranka ya daɗe”.
Nurse ɗin ta faɗa cikin ɗan rawar jiki tana miƙewa zaune. Ranta fes kamar an bata ƙyautar kujerar makka yau gata ga babban ɗan kasuwar nan daya gawurta a ƙasar NAYA da ƙetare a gabanta. Tare da young millioner grandson ɗin sa a gefensa. Dan fuskar Ramadhan sananniyace ga mutane sakamakon rawar da yake takawa shima akan dukiyar tasu wajen juyata da kuma nuna bajintar taimakon talaka akan aikinsa na lauyanci. Babban abinda ya sake bayyanama duniya fuskar tasa lokacin daya rasa matarsa sakamakon shan guba da sukai, dan labarin babu gidan jarida da redio da yanar gizo da bai zagaya ba. Hatta da Raudha taga labarin duk da a lokacin tana jss 2 ne a secondary.
Dan in bata manta ba alokacin har gulmar tsarin halitta da iya ɗaukar wankan Ramadhan ɗin tayi a ranta, duk da kuwa a jikin jarida ta gani ita a wajen wata ƙawarta Rahma Salisu…..
“Masha ALLAH, Alhmdllhi ya rabbi”.
Bappi ya faɗa yana duban Raudha murmushi na sake faɗaɗa akan ƙyaƙyƙyawar fuskarsa.
Murmushin ƙarfin hali itama tai masa, dan haka kawai ita dai dattijon ya shiga mata rai. “Abba ina kwana”.
Ta faɗa da dasashshiyar muryarta tana satar kallon Ramadhan da ko kallon ɗaya a cikinsu baiyi ba balle ɗakin. Tunda suka shigo ya jingina da bangon farkon shigowa ya tura hannunsa a aljihu ya fiddo wayarsa dake tsuwwa yana dubawa. Hakan yasa Raudha bata ganin fuskar tasa da ƙyau yanda ya kamata. Sai dai ƙamshin turarensa da yanda kayan suka zauna ɗas a halittarsa yay mugun fisgar idanunta daga kasa barin kallonsa da son tuno a inda ta taɓa ganinsa……
“Lafiya lau ƴar albarka, yaya jikin naki?!”.
Bappi ya sake katse mata tunani a karo na biyu yana kallon ƙafarta da akai hanging jikin wani ƙarfe, har yanzu a kumbure take sosai abin tausayi.
“Alhamdulillahi naji sauƙi Abba”.
“Zadai kiji soon insha ALLAH. ALLAH yay miki albarka. Ya cigaba da baki kariya a duk inda kika shiga a faɗin duniya. ALLAH ya share hawayenki ya azurtaki da zuri’a ta gari da zata zama lulluɓin nagartacciyar inuwa ga ƙaddarorinki”.
Hannu Raudha ta kai ta share hawayen da suka silalo mata tana amsama bappi. Zuciyarta sai sake faɗaɗa take da ƙaunar tsohon.

  Magana da Bappi yayma Ramadhan ne ya sakashi ɗan matsowa gaban gadon, a karon farko yayma Raudha kallo guda yana tura wayarsa a aljihu, tare da ɗauke idon nasa da ya saka tsigar jikin Raudha tashi. Ƙafar yaɗan kalla, sai kuma ya watsa mata harara. Tun a jiya daya karanta abinda ya faru kafin ya iso ƙasar, da kuma bayanin da Bappin yay masa akan yanda abin ya faru sai zuciyarsa ke raya masa akan wani dalili Raudha ta aikata hakan. Dan in babu dalili babu yanda za'ai ta bada jikinta a raunata saboda kakansa. Na farko kodai akwai shiri a lamarin, ma'ana tanada alaƙa da makashin. Na biyu ko tayi hakanne domin kuɗinsu ko wani abu makamancin hakan. Na uku tanada alaƙa da waɗanda suka halaka masa mata da ƴars......
  “Ramadhan!”.

Bappi ya ambaci sunansa a nutse ganin kallon banzar da yake yima Raudha a kaikaice. Fuska ya sake ɓatawa da jan ƙaramin tsaki a ransa. Harya buɗe baki zaiyi magana ya maida abunsa ya tsuke ganin Bappi ya ɗan ja baya yana kai wayarsa da aka kira cikin kunne alamar amsawa.
Tuni Raudha ta ɗauke idanunta daga kallonsa. Saboda kallon banzar da taga yana binta da shi ya saka zuciyarta yin ɗaci. Tanada haƙuri, amma tana da zuciya. Sannan ta tsani wulaƙanci koda ga wanda ya girmeta ne……
A hankali cike da ƙasaitarsa da jin eh ya isa ya taka gaban gadon sosai fiye da farko, ƙamshin turarensa ck one ya sake sirɗaɗawa cikin hancin Raudha yana keta cikin jininta zuwa ɓargo, saboda ƙarfinsa da tasirinsa ga ma’abocin shaƙansa. Ƙarfen gadon ya dafa saitin kanta tare da ranƙwafowa har tana iya jin fitar sautin numfashinsa. Ya saki wani sihirtaccen murmushi mai ɗauke da ma’anoni da yawa dai-dai gaɓar da yake cafke ƙwayoyin idanun Raudha da mamakinsa ya sata ɗagowa ta kallesa cikin nasa.
“Ki daina yaudararsu, ki kuma tabbatar musu ke BAƘAR INUWA ce. Idan kikai wasa da gargaɗina ni zan zame miki BAƘAR INUWAr da sai kin gwammaci GARA RANA DA NI!.
A kausashe furucin ya fita daga harshen Ramadhan, cikin ƙasaitacciyar muryarsa mai faɗi da kauri ya shiga dodon kunnen Raudha. Da ace ba kusa gab yake da kunnuwanta ba, ita da kantace zata ƙaryata cewar shine ya faɗa ɗin, dan duk wanda yaga yanayin nasu zai ɗauka wata maganace mai daɗi a sanadin tausayawa.
Kafin ta iya ce masa wani abu ya fincike idanunsa a cikin nata cike da tabbatar da gargaɗinsa. Ya ɗan dubi Bappi dai-dai yana ɗagowa ya miƙe akan ƙafafunsa da ƙyau. Ganin Bappin su yake kallo sai ya sakar masa murmushi yana ɗan kai hannu ya shafo ƙeyarsa…
Tabbas wani abu da Ramadhan bai kawo a ransaba a wannan gaɓar ya shiga ran Bappi a bazata. Tun a daren jiya yake cuɗawa da kwancewa wajen laluben nemo hanyar da zai kwatantama Raudha da iyayenta alkairinta, amma sai ya gagara samowa. Dan gani yake kuɗi, gida, ko makamantansu dan ya bama Raudha bai biyata ba. Saboda ita ransa ta fansa. Sai gashi cikin ƙanƙanin lokaci ALLAH ya haska masa wata hanya da yake ganin ko bai saka mata ba, zai kwatanta kusantata gareshi harya samu alkairi daga alkairinta a cikin zuri’arsa….. Ya saki wani ƙasaitaccen murmushi yana kai hannu bisa kafaɗar Ramadhan ya ɗan bubbuga cike da salon manya idan abu yay musu daɗi.
(Lallai sun dace) ya ayyana a ransa yana duban Raudha data kauda kanta gefe zuciyarta na luguden daka daga kausasan kalaman Ramadhan da zuciyarta ta kasama fashin baƙi. Sai kawai nan ma Bappi ya fassara kauda kan nata da tunanin jin kunya duk da baisan wane furuci jikan nasa ya furta a gareta ba.
Ramadhan da shi sam baima kawo abinda Bappin ke ayyanawa ba a tunaninsa sai kawai ya nufi hanyar fita dan gaba ɗaya ya gundura da zaman asibitin. So yake yabar ƙasar nan a daren yau dan tuni ya kammala booking flight. Sai dai zai tashi ne ta jihar Loss shiyyasa yake son barin Bingo da wuri yaje can ya ɗan huta kafin daren.
Nanma da kallo Bappi ya bisa yana murmushi, sai kuma ya ɗauke kansa ya maida ga Raudha da har zuwa yanzu ruɗani bai bar tunaninta ba…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button