BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

       ★

    Duk da aunty Hannah ta lura zazzaɓi ne kawai da damuwa ke damun Raudha babu wani taɓata da ango yayi saita zaɓi yi musu ƙarya da zaunar dasu akan hasashensu na cewar ai ta gasa Raudha a ruwan zafi, dama batayi bane da ƙyau shiyyasa. Shi kuma shugaban ƙasa yana sauri yaje office bai sake taimka mata ta shiga ba da safen nan.
      Kalamanta sun sake baƙanta ran su Safina har Aina’u najan tsaki da hura hanci, zuciyarta kam kamar ta ɓallo ƙirji ta fito dan takaici. Aunty Hannah najin za’a kira doctor daga Taura house tai ruwa tai tsaki akan akwai ƙawarta anan kusa zata kirata basai an saka kowa wahala ba. Ilaiko haka akai, Doctor Farhat tazo ta duba Raudha, ta kuma bata magungunan zazzaɓi harda allura da ledar ruwa ɗaya. Sai suka haɗa baki koda su aunty Mariya suka shigo nuna musu sukai dai har ciwo shugaban ƙasa Ramadhan ya jima Raudha, amma basai anyi ɗinki ba zai warke.
        Sosai mamaki ya kashe Raudha a kwance, dan kuwa tanajin lokacin da suke ƙulla zancen a toilet da suka shige, ita kuma ta bisu ta laɓe dan ca take allurar mutuwa zasu mata ma tunda yanzu aunty Hannah ba’abar yarda bace ba. Sai matuƙar kunya ta hanata iya buɗe ido ta kalli kowa a cikinsu duk da addu’oin da suke jera mata na samun lafiya da albarka. Ga wani takaicin aunty Hannah da mamakinta. To miye nayin ƙaryar dan ALLAH anan? Koda ma hakance ta faru sai an fallasata ma duniya da dangin miji.
      
      Har suka bar gidan ran adda Asmah da su Safina a ɓace yake. Aina’u kam ai ba’a magana. Dama can batazo bikin ba jiya ta iso Bingo saboda bikin rantsar da shugaban ƙasa. Yau ko tazo ne danta gansa duk da akwai shakkar hakan tare da ita a dalilin wasan ɓuya da sukeyi ita da shi game da wani al’amari daya faru a america kusan shekara huɗu kenan. Lokacin yana farko-farkon shiga ruɗanin rasa Amnah da Haseenah.

     Bayan wucewar su aunty Mariya, Aunty Hannah da aunty Halima suka buɗe akwatunan lefen suka gani. Har cikin rai sai da aunty Hannah taji hassada ta soketa, dan ko ita data ɗauka tsahon shekaru tana kutsetseniya cikin manyan mutane bata taɓa ɗaura wani zanin ba. Kayane masu tsada da ƙyau. Ita kanta gimbiya Su’adah da wannan takaicin masu kawo lefen suka barota. Aunty Halima dai daɗi taji ta kumayi addu’a, dan koba komai uwarsu ɗaya ubansu ɗaya da Asabe. Ballema ita mace ce mai zafi da sauƙi, tana da kirki kuma da son dangi. Gata ƴar gaskiya da gaskiya. Dan tun bayan auren Asabe itama ta fahimci aure shine mutuncin ƴa mace ba rayuwar da mahaifiyarsu ta ɗorasu a kaiba. Batai shawara da kowaba ta nutsu ta tuba, wanda ta tuba dominsa kuma sai ya kawo mata mijin aure cikin sauƙi bisa rahamarsa.
        Duk yanda aunty Halima ta hana karsu ɗauki komai aunty Hannah bata saurareta ba. Kowa a gidansu sai da aka ɗaukar masa wani abu a lefen sannan suka wuce bayan sun damƙa Raudha hannun Tambaya wai ta kula da ita idan ta tashi a barci. Aunty halima dai ba haka taso ba, taso suyi haƙuri har Raudha ta farka suji ko tanada buƙatar wani abu, amma babu yanda ta iya tunda aunty Hannah na gaba da ita.

TAURA HOUSE

        A Taura house kuwa sabuwar fitina su Adda Asmah suka sake kunna gimbiya Su’adah. Wani irin zogi takeji a ƙirjinta da jin mai rabata da Ramadhan sai ALLAH……
      “Wlhy Ramadhan yaban mamaki, banyi zatoba daga garesa, bansan mi yarinyarnan ta mallaka ba da har ya ruɗesa da kusantar ta….”
       A hasale Fulani dake shirye-shiryen komawa masarauta saboda kiran da mai-martaba ya mata tazo ta tare gidan surukai ta katse Adda Asmah mai maganar a hasale. “Aiko yayi na farko yayi na ƙarshe dan ubansa. Bandama namiji duk inda yake maye ne (ba ni na faɗaba fulani ce????) har miye a jikin yarinyarnan na bibiya. Yayta wani ɗaga kai da izzar banza a waje ashe shashasha ne”.
       Cikin taɓe baki Addah Asmah tace, 
“Ammy shiyyasa tun jiya nace a fara bata maganin nan na hana ɗaukar ciki ai, shima muyi masa gargaɗin karya raɓu yarinyarnan dan nidai nasan yanda Ramadhan ya jima babu mace koda bai son yarinyarnan zaiyi ruwan kashe gobara da ita. Amma sai kukace babu abinda zaiyi da ita. A tunaninku yanda take ƙyaƙyƙyawa ɗin nan zai iya kauda kansa gareta tunda ma ba tabbacin baya sontane damu ba……”
      Gimbiya Su’adah ta haɗiye wasu hawayen baƙin ciki dake neman zubo mata. Cikin kaushin murya da jin tsananin sakejin sabuwar tsanar Raudha ta katse yayar tata, “Aiko zaiyi aman abinda ya taɓo dan ubansa. Itako sai na maida rayuwarta abin tausayi a ƙasarnan itada karuwan dangin uwarta da faƙiran dangin ubanta. Shiko zaiyi nadamar haɗa shimfiɗa da ita da yay, zaizo ya sameni ai”.
     Kuka Aina’u ta sake fashewa da shi dan duk suna zaune a falon ita da su Safina. Basma da Bilkisu ne kawai babu. Lubnah dake bima Safina kam tafi kowa ɗaukar zafi, dan halinta kaf irin na gimbiya Su’adah ne dama. Rashin son Raudha ya hanata zuwa fadar shugaban ƙasar tun jiya.
     Cikin takaici Munirah dake bima Bilkisu ta harari Aina’u. “Wlhy aunty Aina kina bada mata. Miye abin kuka dan Yaya Ramadhan ya kwanta da waccan wawuyar yarinyar. Nifa kune kuke ganin laifinsa Maa. Karfa ku manta jinin karuwaice, wama ya sani ko itace taja ra’ayinsa ga hakan tunda iyayenta sun koya mata. Kuma koba komai ya mora sadakinsa da wahalar da aka sakashi yakeyi na yawon zuwa ƙauye da kisan kuɗi. Ni dama ya farka shegiya yanda bazata ɗinku ba mtsoww!!”.
         Duk da kasancewar Muneera ƙaramar yarinya a cikinsu sai maganarta tai musu daɗi, dan daga Yusrah sai auta Basma a ɗakin Gimbiya Su’adah, a yanzu hakan shekarun Muneera gaba ɗaya bai wuce ashirin da ɗaya ba zuwa da biyu. Amma har take iya waɗannan zantukan.
        Safina ta ɗanyi dariya, “ALLAH kumafa zancen Muneera haka yake, baima kamata muga laifin Brother ba. Dan haka kibarma fushi da shi Maah. Yarinyar zamu cima ƙaniya kawai. A kuma ɗorata akan maganin hana daukar cikin nan da lalata mahaifarta. Sannan tunda Muneera ta kammala karatunta ta koma can da zama ita da Lubnah, sune zasuci mana ubanta cikin sauƙi kuma suna kawo miki abinda duk ke faruwa a gidan.”
        “Shawararki yayi dai-dai Safina”. Fulani ta faɗa cike da isa da ƙasaita. batare da ta basu damar cewa wani abuba ta cigaba da faɗin, “Harma da Aina’u. Tsakanin Bilkisu da Basma ma wata taje su haɗu su zauna”.
      Adda Asmah tace, “Eh hakan yayi Ammy. Sai dai kinsan Halin Ramadhan zai iya cewa sunyi yawa. Kodai su Bilkisun su zauna su”.
       “Aiba lokaci ɗaya zasu tafi ba, da daɗɗaya kodan waɗan can tsoffin suma da basa iya gani su ƙyale. Amma zuwa Basma ko Bilkisu nada nasa amfanin. Su nuna suna sonta suke, zatafi sakin jiki da su har su san komai nata. Su kuma su Lubnah ta hanyarsu zasu dinga sanin wasu abubuwan ai ko”.
       Cikin gamsuwa suke jinjinama Fulani kawunansu. Banda gimbiya Su’adah da har yanzu zuciyarta ke a matuƙar ƙuntace. Dan ko magana bata iya sakeyi ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button