BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

      Su kansu su Anne a rikice suke da jin wannan al’amari musamman ma aunty Hannah da tasan suna da alaƙa da kuku. hasalima yaronsu ne su yakema aiki a gidan. A gefe kuma ta shiga mamaki da ruɗanin mizaisa kuku ya zubdama Raudha ciki? Saboda koba komai suma suna buƙatar cikin matsayinsu na jinin Raudha mafi kusanci.

(To koma dai miye, wannan wata sabuwar cakwakiyace kuma???????????? Aunty hannaty).

★★★

       Ramadhan bai sake cewa komai ba akan batun duk da yaji cewar Raudha tasha ƙwayar ne da ruwan shayi. Hakan na nufin kuku’s ne da aika-aikar, a yanzu haka kuma shugaban kuku’e ɗin dake da alhakin kula da abincinsu yana hanun securitys na gidan.
       Bayan sallar isha’i su Anne suka wuce gida har aunty Hannah. Sai dai zuwa lokacin Ramadhan yasa an dawo da Raudha cikin gidan tana ma ɗakinta. Alhakin dubata ya koma wuyan Dr Hauwa’u a yanzun gaba ɗaya, sannan Mama Ladi aka bari a ɗakin zata cigaba da kula da ita.
        Ramadhan ya nunama Dr Hauwa’u yana son kowa ya cigaba da ɗaukar hakan har su Anne cewar cikinne da Raudha kuma ya zube. Batasan dalilinsa ba, amma kuma ta karɓa alfarmarsa dan ta fahimci akwai ƙulli a cikin al’amarin mai girma. Badan ma ALLAH ya taƙaita ba komai zai iya faruwa da mahaifar Raudha ɗin, a yanzu hakama basu da tabbacin komai zai iya zama normal.

★★

          Washe gari da safe ya tashi babu wani damuwar jinin da aka ɗiba masa. Dan har massallaci ya fita sallar asuba. Bayan dawowarsa massallaci ya jima zaune cikin sofa yana ƙullawa da kwancewa akan al’amarin. Wajen shidda aka kawo masa tataccen haɗin shayin lemon tsami da wasu ganyayyaki na shayi da yake sha a duk safiya dan shi ba ruwansa da wani coffee.
        Har kukun dake kula da shayin nasa ta kammala ta fita bai motsa ba. Baima amsa ko gaisuwarta ba. Hakama bayan fitarta bai sha shayin ba dan tunaninsa ma baya tare da duniyar mutane. Bazai so ya zama silar hana wani cin abinci ba, amma dolene ya ɗauka wani mataki game da wasu ma’aikatan gidan musamman kuku’s dake da alhakin basu abu suci.    
         A hankali ya furzar da iskar daya tara a ƙirji yana miƙewa batare da yabi takan shayin ba. Ba tsoron an zuba masa wani abu yake ba, kawai dai yau bama shi da ra’ayin shan komai ne kawai. Wanka yayo yay shirin office, tamkar kullum yau ma yayi ƙyau matuƙa yana ta baza ƙamshin turarurrukansa da suka amsa sunansu turare. Koda ya fito ɗakin Raudha ya nufa, kowa bai samu ba a ɗakin ba sai dai an gyara shi yanata ƙamshi. Raudha kwance a gado cikin bargo babu alamar ta farka. Tsaye yay akanta ya tsurama cute face nata ido, ta sake haske sosai, ta kuma rame. A hankali yakai zaune bakin gadon tare riƙo hanunta dake saman cikinta ya riƙe cikin nasa. Kasa jure abinda ya ratsa sa yayi, sai kawai ya rumtse hanun da ƙyau a cikin nashi har sai da taɗan motsa.
       Tabbas ya yarda ita ɗin ƙyaƙyƙyawa ce, sai dai a ganinsa tayi yarinta da yawa. A zuciya yake wannan tunanin, a zahiri kam ido kawai ya tsura mata. Yanada meeting da shuwagabanin tsaro baki ɗaya, dole ta sashi miƙewa yana ƙoƙarin zare hannunsa a cikin nata sai dai ta riƙe nasa ita kuma. Tsamm ya tsaya yana kallon hanun nata yanda ta matse yatsun nasa biyu tamkar tana ido biyu. A bazata murmushi ya suɓuce masa, sai dai komai baice ba ya zare yatsun nasa yana ɗon furzar da huci.

       ★
   Koda ya fita kafin yaje office ma wajen meeting ɗin ya fara zarcewa, dan ya makara, kuma zama ne mai matuƙar muhimmanci. Harkar tsaro da lafiya da ilimi sune sahun farko da yake burin fara shimfiɗawa al’ummarsa kafin komai. Dan haka yasa aka shirya masa zama da shuwagabanin jami’an tsaro ta kowanne ɓangare, dana lafiya takowane nangare, dana ilimi takowane ɓangare. Zai fara zama da jami’an tsaron ne kafin sauran suma.
      Meeting ɗin ya jasu lokaci saboda muhimmancin sa. Dan a ƙalla sun sami good 3hours. Koda ya shiga office bai iya taɓuka wasu abun arziƙi ba. Yadai gana da vice president Alhaji Yaro glass akan wasu muhimman batutuwa. Sanda suka kammala lokacin salla yayi. bayan dawowarsa massallaci ya gana da COS daga nan ya tafi hutun awanni biyu. Maimakon zaman hutun sai yay zaman yin waya da Bappi.

      Ƙarfe biyar na yamma ya shigo gidan yau. Sai da ya fara zuwa ɗakinsa yay wanka ya kimtsa cikin ƙananun kaya sannan ya fito domin duba jikinta. Bai samu kowa a ɗakinba yanzu ma. Motsin ruwa da yaji ya tabbatar masa tana toilet, agogon dake a tsintacciyar hanunsa ya kalla tare da ɗan bin ɗakin da kallo. Saukar idanunsa akan hoton dake saman bed side drawer ɗinta ya sashi takawa a hankali garesa hannayensa duka cikin aljihun wandon jeans ɗin sa, hoton ya tsurama ido duk da bawani fitaccen hoto bane, hasalima ya ɗau shekaru, dan mace ce da mijinta sai yara huɗu, ɗaya jaririya a hanun mijin, sai ƴar shekara 7 da kamanin Raudha ke tare da ita tabbacin dai itace ɗin. Sai biyu da bazasu wune shakara tara ba da alama twins ne.
      Kiran da akaima wayarsa ne ya katse sa da ga kallon hoton, ya zarota a aljihu yana mai janye idanunsa a hoton gaba ɗaya. A kuma dai-dai lokacin Raudha ta fito da alamun wanka tayi.
       A hankali take takowa cikin ɗakin dan da farko bata lura da shi ba. Sai dai kuma yanda ƙamshinsa ya cika ɗakin ya sata tsarguwa harta kasa ƙarema ɗakin kallo. Sallamar da yay lokacin da yake kai wayar a kunnensa ya sata tsayawa cak daga takowar da take, gaba ɗaya jitai ta daburce, gashi ta riga da tazo kusan tsakkiyar ɗakin tasan dai ya riga ya gama ganinta kuma. Kallonsa ta ɗan sata kaɗan, ya ɗan zuba mata idanu tamkar mai shirin gano wanda ya aikata mata abun a jikinta.
      Da sauri ta maida idanun nata ƙasa. Shima ya janye nasa yana cigaba da sauraren masifar da gimbiya Su’adah ke masa ta cikin wayar, shi gaba ɗaya ma ya rasa dalilin faɗan nata shiyyasa saurarenta kawai yake batare daya fahimceta ba har tayi ta gama ta katse kiran bayan ta bashi umarnin ganinsa.
      Kansa ya ɗan girgiza kawai yana sauke numfashi, a zuciyarsa mamakin daru irin na mahaifiyarsa yake. A zahiri kam idonsa ya maida ga Raudha datai tsaye tamkar an dasata
    “Ƙaraso mana”.
Ya faɗa a hankali tamkar baya so.
            Duk da bathrobe ce a jikinta gaba ɗaya kunya ta dabaibayeta. Amma saita daure ta ƙarasa bakin gadon dan jiri take gani ma. Tana gab da isa jirin ya kwashe tai tamkar zata faɗi ALLAH ya taƙaita sai jinta tai jikin mutum…………✍

Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan????????????????????????.

ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????
……….Ba sai an mata wani explanation ba tasan shine. Dan mayataccen ƙamshinsa tuni ya ƙara ƙarfi a ƙofofin hancinta. Kasa buɗe ido tayi ta kallesa dan kunya, ga shi bata da ƙarfin da zata ƙwace jikinta a nasa.
      “Kina ganin jiri ne?”.
   Ya faɗa a hankali yana tallafo fuskarta cikin tafin hanunsa. Bata yarda ta buɗe idanunta ba, sai ta jinjina masa kanta, zuciyarta babu abinda take sai luguden daka kamar zata fito waje, ga tsigar jikinta sai yamutsawa take. Dan wannan shine karo na farko da ya taɓa mata irin wannan riƙon a cikin jikinsa sosai kamar haka. Shi kansa danne yanayin kawai yake a zuciyarsa, yay ƙoƙarin kaita zaune a bakin gadon…. 
         Dai-dai lokacin Mama Ladi da batai zaton samunsa a ɗakin ba ta turo ƙofar da sallama ta shigo saboda tasan Raudha ɗin ma ta barta ne tana wanka batai tsammanin ta fito ba. Shigowar tata baisa ya janye jikinsa da ga na Raudha ba, sai ma itace data ɗan dabirce har ta samu ƙarfin yin mutsu-mutsu amma sai ya shareta. A ɗan rikice Mama Ladi ta juya zata koma ya dakatar da ita
      “A gafarce ni ranka ya daɗe wlhy bansan kana ciki ba”.
     “Is ok”. Ya faɗa tamkar baya so yana matsar da jikin nasa daga na Raudha ya zaunar da ita da ƙyau ya miƙe akan ƙafafunsa, nuni yayma Mama ladi data ajiye kayan hanun nata. Cikin girmamawa ta ƙaraso ta ɗora tray ɗin saman table da alama abinci ta haɗoma mata.
         “Babu dai wata matsala zuwa yanzu ko?”.
       “Eh ranka ya daɗe Alhmdllhi. Likitama da tazo ɗazun tace komai ya dai-daita sai dai a cigaba da kula da maganinta, ta kuma dinga cin abinci sosai dan ƙarfin jikinta ya dawo”.
      Baice komai ba sai kallon Raudha da yayi. Sosai ta rame, ƴar ƙibar da tayi duk ta zube. Idanun ya janye yana ɗan furzar da iska. Sai kuma yace, “ALLAH ya ƙara lafiya”.
        Mama Ladi ta amsa da “Amin”. Raudha ma data kai kwance saboda rashin ƙarfin jiki ta amsa a laɓɓanta.
        Bai sake cewa komai ba ya fita a ɗakin ya barsu, dan Taura house yake son zuwa amma a ɓadda kama zai fita gidan. Ɗakinsa ya koma ya ɗaura jacket saman kayansa da p-cap ya fita, odilan ɗinsa dake jiransa dan dashi kaɗai zasuyi fitar yay saurin risinawa yana masa barka da fitowa. Kansa kawai ya jinjina masa.
       “Saifu muje lokaci yaja”.
   “Okay sir, odilan Saifudden ya faɗa da sauri yana buɗe masa back sit.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button