BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

NAYA (BINGO CITY)
Cikin ɗan barcin daya ɗauketa takejin wayarta da ke a bedside drawer na faman vibration data sata. Babu wanda ta kawo a ranta sai Yasmin dan tunda tai wayar nan haka take damunta da flashing da wayar Mummysu ko tasu Fatima. Cikin jan ƙaramin tsaki ta miƙa hanunta ta lalubo wayar batare data tashi ba, da ƙyar ta buɗe ido kaɗan ta ɗaga ta maida kanta a filon da ɗora wayar bisa kunne tace, “Hallo Yasmin!”.
Wani irin tashi tsigar jikinsa tayi saboda jin yanda sautin muryar tata ke fita a mayen barci-barci. Cikin dakiya ya ture abinda ya tsikari ran nasa.
“Dama abinda kikaje yi a Saloon ɗin kenan?….”
Tuni idanunta suka watsatsake ta tashi zaune dakaka dan bata buƙatar fassara ta gama haddace mai muryar. Batare da ya bata damar yin magana ba ko amsa gaisuwar data fara masa irin na suɓul da baka ɗinnan ga wanda ya shiga ruɗani ya cigaba da magana a zafafe a kuma kausashe.
“Tunda ga ɗan iska wanda bai san abinda yake ba ko. Matata ta zama hajar da kowane kare da doki zai iya kalla har a yanar gizo. Tunda tallar jikin kike da sha’awar yi miyyasa baki zauna a gidanku kinyi ba, sai da aurena! Da aurena kike saka wando da riga ana miki hoto a ɗora a shafin yanar gizo! Jikin da ni ban taɓa gani a haka ba wasu dabbobi suke tururuwar gani I hate you!! Na tsani ballagazar mace da bata iya kame jikinta stupid girl!…..”
Tuni hawaye sun wanke illahirin fuskar Raudha. Babu abinda jikinta keyi sai tsuma kanta harya fara sarawa saboda yanda yake mata magana a kausashe a kuma tsananin zafafe. Duk yanda take masa kallon mai tsauri ta fahimci ya zarce haka a yau. Dan babu komai a cikin kalamansa sai ɗaci da matuƙar hasala…
A hankali Bilkisu data shigo ɗakin ɗauke da roba ice-creem da kwalin pizza ta ƙaraso gareta bayan ta ajiye kayan hanunta kan table ɗin gaban sofa. Duk barkwancin data shigo da shi cikin ɗakin tuni ta haɗiye abinta ganin yanda fuskar Raudha ke wanke da ruwan hawaye ga waya a kunnenta. Wayar ta zare a hankali ta kashe batare da ta duba da wa Raudha ke waya ba.
Ta kamo hanunta sosai tare da jawota jikinta ta rungume. “Please aunty Raudha relax. Kibar kuka dan ALLAH na roƙeki. Ke da wanene haka da har zai saki kuka ta waya..?”
Ɗagowa Raudha tayi tana share hawayenta da hannu biyu. “Aunty B dan ALLAH kece kika ɗora hotunan da mukai a yanar gizo?”.
Cikin ɗan zaro ido Bilkisu tace, “What! Akansu ne kike kukan nan?”.
“Aunty shine fa ya kira yake faɗa akan ɗaurawan”.
“Wai kina nufin Yaya!”.
Kai ta jinjina mata wasu hawayen na sake rige-rigen sakkowa. Da sauri Bilkisu ta ɗauka wayar tana ambaton “Ya ALLAH shike nan na mutu, shine na kashe masa kira”. Bata jira amsar Raudha da ba tai dailing number back. Ba’a ɗauka ba, dan yana can ya sake harzuƙa akan kashe masa wayar da akai. Ya riga ya gama fassara ƙarfin rashin kunya da rashin tarbiyyar Raudha. Har shine zata kashema waya? Kalmar mahaifiyarsa na ƴar karuwai danginta karuwai suka shiga masa kai kawo saboda kishi ya hautsinashi. A take kansa ya fara juyawa zuciyar ta sake tunzura da ɓacin rai ya fara huci…….
Kira ne ya sake shigowa a wayar tasa, tana gab da tsinkewa ya ɗaga da shirin yimata abinda bazata sake gigin kiran layinsa ba ma har abada.
Bilkisu da ƙirjinta ke luguden daga dan cike da ƙarfin hali ta sake ƙundunbalar kiran ta rumtse ido sakamakon cin karo da kausasan kalaman yayan nasu….. Ta rumtse ido itama da ƙarfi gabanta na faɗuwa dan ta fahimci a birkice yake. cikin rawar murya da ƙarfin hali tace, “Yaya… Am sorry Please nice. Wlhy ba laifinta bane laifina ne batama san na ɗaura pictures ɗin b….”
“Shut-up stupid!!!”.
Ya faɗa cikin tsananin tsawar da tafi wadda yay ma Raudhan. Dan ya gane bilkisun ce ta amshi wayar.
“Na baki mintuna biyu ki saukesu wawuya kawai. Zan sauke miki abinda ke miki yawo a brain tunda media gidan ubanki ne da zaki ɗauketa hoto a haka kikai musu….”
“Dan ALLAH kayi haƙuri Yaya na tuba na san nayi kuskure”.
Ƙittt ya yanke kiran batare daya amsa ta ba…..
ENGLAND (LONDON)
A kwanaki biyun da suka rage tawagar shugaban ƙasa Ramadhan sun fahimci bashi da walwala. Kai bama walwala ba gaba ɗaya a cikin yanayin fushi yake. Dan komai yana yinsa ne cikin faɗa-faɗa. Ko a wajen meeting da sukai na ƙarshe kalaman da yay amfani da su da suka nema tada ƙura a ƙasar NAYA ya sake tabbatar da zuciyarsa a wuya take.
Dan daga Bappi har Anne da Pa kai tsaye suka fahimci haka lokacin da suke kallon labaran. Sai dai mai magana da yawunsa ya sake faɗaɗa kalaman yanda zasu cire ƙulli a zukatan ƴan ƙasar musamman waɗan da suka ƙullacesa a rai. Wasu sun gamsu wasu ko sun riga sun hau da takaici matuƙa…
Oho shi baima san sunayi ba. Dan in yana a irin wannan yanayin bawai yana gane yaren kowa bane ba. Shi kansa baya gane kansa ballantana wani. Hatta da su Anne dan karsu kirasa ya kashe wayarsa ne. Sai dai hakan bai hana Bappi bin ta ɗayan layinsa ba shi ya kirashi. kamar bazai ɗaga ba ya dai daure ya ɗaga. Da ƙyar yake magana hakan ya sake tabbatar ma da Bappi akwai matsala…
Koda ya matsa masa da tabbaya bai ɓoye ba ya sanar masa abinda ya ɓata masa ran. Dan tun yana ƙaraminsa Bappi da Anne sune abokansa, aminansa, iyayensa, kakaninsa. Da wahala yayi wani abu batare da shawararsu ba ko bijirema umarninsu idan sun masa.
Dariya sosai ta kama Bappi amma sai ya gimtse ta da ƙyar sai murmushi yake. tsaf ya fahimci kishi mai tsanani ke ɗawainiya da Ramadhan. Ya daɗe da sanin jikansa nada kishi mai zafi irin nasa. Dan shima haka yake da tsananin kishi ga matarsa Anne. Kafin suyi aure yasha fasa bakin samari idan ya gansu tare da Anne koda ƴan family nasu ne. Kishinsa na ɗaya da ga cikin abinda yasa iyayensu aurar da su batare da sun jira sun kammala karatunsu ba.
“To ALLAH ya huci zuciyar maza”.
Bappi ya faɗa murmushi faɗaɗe a saman fuskarsa idonsa akan matarsa data zuba masa ido da son jin mike faruwa da jikan nata.
Bappi ya cigaba da faɗin, “Bilkisu itace mai laifin bata ƙyauta ba sam. Amma ayi haƙuri a kori gaba. Na tabbata da Aminatu tasan zata ɗaura zata hanata tunda tasan baka so…”
“Amma Bappi wando da riga fa ta saka itama ta fita waje matsayinta na matar aure. Da bata sa kayanba ita Bilkisun zata ɗauketa hoton ne?…”
“Uhm itama tayi laifi anan, amma bilkisun ai ta girmeta ya kamata ta fita hankali tunda tare suka fita. Sai dai ina roƙa mata afuwa a tari gaba, idan ta ƙara ni kaina zance a hukuntata kaji babban mutum. Ayi haƙuri zuciyar ta huce haka nan dan ALLAH, dan naga muma ƴan ƙasa fushin ya shafemu har ana mana dogon gargaɗin da gashinan ya tashin hankalinmu baki ɗaya”.
Murmushi Ramadhan ya saki mai sauti yana kai hannu a goshinsa yana murzawa. “ALLAH Bappi bamma san na faɗa ba yarinyar nan ce duk ta harmutsani.”.
Dariya sosai Bappi ya ƙyalƙyale da ita da faɗin, “Ja’iri da alama dai kazo hannufa. Ni nasan Aminatu na ba kalar matan da za’a kira na cushe bane ai”.
Ramadhan ya ƙyalƙyale da dariya harda kwanciya a kujera. “Oh sweet bappi karda ku cika baki, dan nidai cusamin akai”.
“Nima naga alamar hakan kuwa yau”. Bappi ya faɗa yana dariya shima.