BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

     “Ko? to andai ji kunya Ustazai da rowan nama, idan kina son kanki da arziki muje ki bani nawa naci kokuma na ɗiba rabona a can” 

Yay maganar cikin ɗage mata gira ɗaya yana miƙewa. Batare da ya jira cewarta ba ya fice abinsa. (Uhm, su Ramadhana an fara zama ƴan is…????????????)

    Filo Raudha ta ɗauka ta balla masa cizo tana matsesa a ƙirjinta. Sai kuma ta tillashi ƙasa tare da dafe kai tana faɗin, “Ni Raudha yama haukatar dani”.

    Babu yanda ta iya dole ta miƙe ta ɗau mayafinta na ɗazun dan kayanne a jikinta har yanzun ma ta fita. Tsaye ta samesa a falo hankalinsa gaba ɗaya akan television da ake nuna labarai. Koke-koke da taji anayi a tvn ya sata saurin kallo gabanta na faɗuwa. Jikinta ya kama rawa, domin kuwa rahotone na wani ƙauye a ƙaramar hukumar Gaman dake jihar Kuddo faɗa ya ɓarke a tsakanin ƙabilun dake ƙauyen. Gawarwakine zube na yara da manya harma da dabbobi, wasu jina-jina da raunika abin babu daɗin gani. Ga wasu nata kuka durkushe gaban gawarwakin ƴan uwansu da aka kashe ko aka raunata.

   Kuka da Raudha ta fashe da shi ne ya maido Ramadhan da ga ɗaukewar numfashi da ya tafi na tashin hankali. Ya kai zaune jib cikin kujera hajijiya na neman ɗibarsa. Ba yau ne aka fara irin wannan rikicin a ƙauyen ba, sai dai bai taɓa gani ba kamar yau, ga shi yau ɗin daya gani kuma yana amsa sunan shugaban kasar NAYA ne da hakkin kowa ya rataya ne a ƙarƙashin mulkinsa….. Yanda jikin nasa ke rawa ya sakashi riƙo Raudha data kai dirƙushe a gabansa tana kuka ya rungume, itama ƙanƙamesa tayi kawai tana sakin wani sabon kukan…..  

    Wayarsa ya fara laluba da hannu ɗaya a aljihu, yayinda ɗayan ke tallafe da Raudha. Yana cirota kafin ma ya aiwatar da abinda yake shirin yi kira ya shigo masa. Da ƙyar ya iya controling kansa tsabar ruɗani ya ɗaga, da ga can hankali tashe cos ya ce, “Ranka ya daɗe kaga abinda ake nunawa a tashar Q-TV kuwa? Kodai halin ƴan adawa ne kawai….”

     “No Jafar, karka kawo wannan, ka bincika yanzu abun ke faruwa ne ko tun ɗazun?”.

   “Okay sir ina zuwa”.

 Wayar ya jefa saman kujera, ya kai zaune shima har yanzu Raudha na jikinsa tana sharɓar kuka. Ji yake kamar shima ya fashe da kukan, amma ya daure ya ɗago Raudha, cikin dakiya yake faɗin, “Please Ameenatu relax mana. Kukanki sake tadamin hankali yake, bayan daga gareki ya kamata na samu ƙarfin gwiwa”.

   Hannu tasa tana sharar hawayen, “Kayi haƙuri”. Ta faɗa tana ƙoƙarin tashi daga saman cinyarsa da take zaune ɗare-ɗare gudun kar Bilkisu ta fito, kuma a karankanta ma dai da kunya ai.

   Komai baice mata ba, sai wayarsa data fara ring ya kai hannu ya ɗauka ganin cos ne.

   “Ranka ya daɗe a yanda suka faɗa su dai yanzu ne. Amma dai yanzu I.G ya tabbatar min tun kusan magrib ne abun ya fara faruwa kamar yanda C.P ɗin jihar Kuddo ya sanar masa. Sai dai ka kwantar da hankalinka ya tabbatar min komai ya dai-daita zuwa yanz…….”

      A matuƙar tsawace shugaban ƙasa Ramadhan ya katse cos, “Taya zan kwantar da hankalina Jafar? mutane na cikin irin wannan tashin hankalin!! Ka duba fa kaga mata ne da yara kanana a cikin jini saboda rashin imanii!!! Yanzu da akan familyna ya faru zakace na kwantar da hankalina ne? Na shiga uku ni Ramadhan!……..”

    A yanda yay maganar dole ne ya baka tausayi ya kuma tayar maka da hankali, dan abun al’ajabi sai ga hawaye na sakko masa. Wayar yay jifa da ita tare da dafe kansa yana yamutsa gashinsa da duka hannayensa biyu.

   Sosai Raudha ta sake rikicewa itama, dan yanda yake birkita sumarsa yana hawaye da ambaton ya shiga ukun itama sai ta sake fashewa da kukan da zuwa gabansa ta durƙushe hannayenta duka biyu akan gwiwoyinsa…………✍

Kubaku gane nima a tsorace nake da dawowar Ramadhan ba, karya haɗa dani????????.

End of book

Leave a comment

Post

Comments

serlmerh2
Oooh Allah….nxt page plz

18 minutes ago

bilki
Takwara a karo mana

19 minutes ago

bilki
Wayo president abun tausayi

21 minutes ago

104835043420935222197
To Aishikknan munyadda atsorace kike amma yanxu aiya hakura pls kisamana wani Dan Allah ????

22 minutes ago

Contact Us
Arewa Books Publishers

WhatsApp: 09031774742

Email: arewabookspublishers@gmail.com

Navigation
Home
About
FAQ’s
Legal
Privacy Policy
Terms of Service
Social
Facebook
Instagram

Copyright 2021, Arewa Books | ALL RIGHTS RESERVED | Powered by thinkcrypt.io
Menu
Dashboard
My Library
Create Story
Home
About us
FAQ’s
Privacy Policy
Terms of service
Logout

BAKAR INUWA…!!
Chapter: 44

Share:

Report

BAKAR INUWA…!!
View: 405

Words: 3.1K

Chapter 44
44

……….Su dukansu fuskokinsu washe suke da fara’a da farin ciki. Gasashshen naman rago ne a banƙare a tsakiyarsu. Sai lemuka masu tsada da daɗi ajiye gaban kowa. Gaba ɗayansu hankulansu nakan tv da ake nuna abinda ke faruwa a ƙauyen Kauci na ƙaramar hukuma Gaman. Cikin ƙyalƙyalewa da dariya Mr MM ya kai tsokar nama daya cako da pork spoon bakinsa yana faɗin, “Wato ranka ya daɗe dabarar nan taka tayi ɗari bisa ɗari, yaje ya dawo yana farin cikin samun na sarori sai yaci karo da ƙyaƙyƙyawar tarba ta musamman”.

    Kwashewa sukai da dariya baki ɗayansu, Alhaji Haladu Gwandu dake dariya harda hawaye ya ce, “A to ba gani yake shi yanada dabarar shinfiɗa aiki ba ta hanyar ɗaura ƴan uwansa matasa kan manyan muƙamai, to sai yayi aikin mugani. Basai da zaman lafiya a ƙasar talakan zai ga aikin ba?”.

   Wata dariyar suka sake kwashewa da ita. Sai dai banda oga kwata-kwata da yake murmushi kawai yana cin namansa shima. A cikin God fathers ɗin nasu ɗaya ya tsaida dariyarsa ya ajiye wuƙar daya yanko wani ƙaton nama ya ɗauka da hannu yakai baki. “Ai indai mune baima ga komai ba. Sai mutuwar fitinannen tsohon kakan can nasa ta tabbata nan da kwanaki uku, a kuma ranar plan B zai bayyana shima, yanda mutuwar Alhaji Hameed Taura bazatayi tasiri a zukatan mutane ba balle ya samu addu’a da nuna tausayawa”.

    Dariyar suka sake tuntsirewa da shi. Forma president ya ce, “Wa yaga gaba kura baya sayaƙi. Bashi gani yake mulkin wasan yara bane ba, zai yabawa aya zaƙinta. Yanzu nan fa ina shirin fitowa ma nakejin wani ƙishin-kishin ɗin gulma, wai da yayi niyyar bincike akan kwangilolin da muka bada, sai dai ya dakatar dalilin wani abu da ba’asan tabbaci ba………”

    Vice president Alhaji Yaro glass ya karɓe zancen forma president da faɗin, “Wannan maganar kam tabbas ce, sai dai nima ina kan bincike miye dalilin hanashi fasa binciken. Dan yanzu haka ma gobe za’a zauna da masu kwangilan meeting tare da J.P.S”.

     “What!! Alhaji Haladu Gwandu (Mahaifin Amnah) Ya faɗa aɗan razane. Dan kuwa akwai yaronsa a cikin wanda aka bama kwangilolin, kuma tabbas yau kusan kwanaki uku yana kiransa bai samu damar ɗaga wayar tasa ba saboda busy da yayi…..

    “Wlhy da gaske haka zancen yake”.

   Alhaji yaro glass ya faɗa a yanayin takaici da jin ɗaci. Waya Alhaji Haladu Gwandu ya lalubo a aljihun babbar rigarsa. Da sauri ya shiga laluben lambar yaron nasa. cikin sa’a kuwa bugu ɗaya ya ɗauka tamkar dama kiran nashi yake jira. Ko sauraren gaisuwar tasa baiyiba ya jeho masa tambaya. Sai dai amsar daya bashi tai matuƙar firgitashi ya saki baki da hanci yana saurare har yaron nasa ya gama bayanin saƙon da suka samu na kira da ga ofishin Minister.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button