BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

   Cikin ɗan Murmushi Raudha tai gaba dan bata son gwasale Agnes ɗin. A tare suka haura saman, Agnes zata nufi dining Raudha ta dakatar da ita ta amsa da mata sannu. Kai tsaye ɗakin Ramadhan ta nufa, haka kawai murmushi ya suɓuce mata tunawa da abinda ya faru jiya dama abinda taji yana faɗa ɗazun, ta gama fahimtar baya ƙaunar raini sam. A zuciyarta take faɗin (karka damu, indai Aminatu ce har abada babu raini tsakaninmu). 

   A fili kam sai tai knocking ƙofar kaɗan dayin sallama. Bataji an amsaba sai kawai ta tura ƙofar tana ƙarayi. Duk abinda take yana kwance yana jinta, sai dai yay luf fuska a tamke dan kawai yasan tunda har jiya yay abun kunya ta gama samun hanyar rainasa. Raudha har zuciya bata kawo lanbo yay mata ba. Ta ajiye basket ɗin ta fita.

    Da kallo ya bita harta fice.

  ★★Sai da ta kammala shirinta na fita tsaf cikin kayan mutunci sannan ta fito tare da kulle ɗakinta dan tasan a koda yaushe su Lubnah zasu iya dawowa gidan. Koda ta koma ɗakinsa ta iskesa still kwance sai jikinta yay sanyi, duk zumuɗinta na son tafiya makarantar kuma sai ya fita mata a kai. Ajiye bag ɗinta da hijjab tai ta nufi toilet, tsaftacesa tai ta fito ɗakin shima ta gyara iya inda bazata takura masa ba. Daga haka ta ɗauka bag ɗinta ta koma ɗakinta dan ta haƙura da makarantar kawai tunda shima bazai fita ba.

    Acan waje tuni securitys ɗinta da jiya ta gudumawa suna falon ƙasa suna jiran fitowarta. Hakama driver ya shirya tun da wuri dan gani suke jiya sakacinsu ne ya sata fita a gidan badasu ba. Basma ta kira ta sanarwa yau bazata shigo school ba. Daga baya sa nuna mata abinda aka kawai. Bata bama Basma damar yin ƙorafi ba ta kashe wayar gaba ɗaya itama ta kwanta, dama barcine taf a idonta ga ciwon da jikinta ke mata akan kwanciyar jiya.

   Tunda cos ya ga takwas ta wuce shugaban ƙasa bai fitoba yasan murar jiya ta kwantar da shi kenan. Saƙo ya tura masa kawai ya cigaba da abinda ya dace dan Alhmdllhi ma yau abubuwan da Ramadhan ɗin zaiyi duk ba masu tsawwalawa bane. Zaman meeting ne sau kusan huɗu duka kuma an riga an tsara wanda zasuyi zaman. Abinda yake tilas saka hannu ne akan wasu takardu.


     Tunda su Basma ke bada labarin Raudha ta fara karatu a school ɗinsu zuciyarta ke a ƙuntace. Lallai ta sake tabbatarwa ɗanta baya tare da ita. Komai daya shafesa sai dai taji a shanun ƴan talla. Tana cikin wannan yanayi Mardiyya tazo gidan, ɗiyarta ta biyu dake bin Ramadhan. Daga office take taga ya dace ta biyo ta gaishesu dan rabonta da gidan tun bikin Ramadhan ɗin. Haka take ita bata da kwaramniya, ga haƙuri. Lokuta da dama mutanen gidan kan ɗauketa wadda bata ɗaukar abu serious, sai dai kuma ba haka bane. Ita irin mutanen nan ne da babu ruwansu da shiga sabgar daba tasu ba, muguwar ƴar I don’t care ce ta bugawa a jarida. Halayyarta ya saka bata wani shiri na’azo a gani da Gimbiya Su’adah. Yaranta huɗu, tare da mijinta suke aiki a companyn su na kansu da sukai haɗin gwiwar ginawa ita da shi. Ba ƙaramin bala’i a lokacin taci ga Gimbiya Su’adah ba. Amma tai fumfurus ta shareta. Da farko robobi companyn ke fitarwa, a hankali abubuwa suka kara bunƙasa takai har designes na wasu abubuwan daya shafi kayan kitchen suna sarrafawa. Kamar wasa sai gasu sun bunƙasa suma ana kwatantasu a jerin manyan kamfanoni dake sarrafa abubuwa masu muhimmanci a ƙasar.

    “Maah! Lafiya kuwa naga kamar ranki a ɓace?”.

  Duk da tasan halin ɗiyar tata na rashin ɗaukar abu da muhimmanci hakan bai hanata fara zayyane mata cikinta ba rai ɓace. 

      “Miyema bai faruba Mardiyya. Yanzu a duniyar nan babu abinda ke cimun rai da ƙonan zuciya sama da auren ɗan uwanku. Na tsani yarinyarnan da duk wani mai alaƙa da ita a duniya. Ji nake zan iya kasheta da hannnuna wlhy…..”

   “Wa’iyazubillah Maah miya kawo wannan maganar haka?”. Mardiyya tai saurin katseta.

    “Humm Mardiyya kenan, yanzu ke tunda kike a duniya kin taɓa jin matar shugaban ƙasa mai shekara sha takwas? Jahila da ko karatun sakandire banajin ta kammala? Daɗin daɗawa ƴar karuwai marasa tarbiyya da kowa yasan aikinsu a bayyane yake.” hawaye suka silalo mata, ta kai hannu ta share da cigaba da faɗin, “Mardiyya na tabbatar a ƙuntace Ramadhan yake, biyayyar da yakema kakanninku ce kawai ta sakashi haƙura ya amshi raunanniyar yarinyar nan, wai dan takaici sai yanzu take shiga jami’a. Matar shugaban ƙasa fa daya kamata ta zama vary educational, wayayya ta nunawa a duniya, wadda duk inda tasa ƙafa zata fiddashi a kunya muma ta fiddamu. ALLAH dai ya tsinema wannan aure na Ramadhan albar…….”

    “Haba dan girman ALLAH Maah wane irin furicine haka babu daɗin ji. Idan kin tsinema auren Brother tamkar shi kika tsinemawa dan zata iya yuwuwa yanzu haka an samu rabo tsakaninsu. Maah ki kwantar da hankalinki dan ALLAH, ni wlhy banga wani aibu ga yarinyarnan ba. Inma iyayenta sunada wancan halin ai ba itace kedashi ba. ALLAH kuma yana fidda rayayye a cikin matacce, ya fidda matacce a cikin rayayye. Karatu ko karancin shekarunta normal ne ni a wajena. Miye amfanin ya auri wayayyar mai ilimin tazo ta zame masa damuwa shi da mulkin nasa damu kammu. Yanzu ko shi zai bama matarsa tarbiyyar data dace akan tsarin mulkinsa ta tashi akai kuma yay alfahari anan gaba Maah. Dan ALLAH ki cirema kanki damuwar nan ki musu addu’a sai kiga wataran komai ya zama yanda kike so. Kwana nawane zata kammala karatun ma, ina amfanin ya auri sa’arsa tazo ta rigashi tsufa……..”

   Hannu Gimbiya Su’adah ta ɗaga mata a fusace. Cikin zafin rai ta nuna mata ƙofar fita. “Tashi ki fitarmin kafin na saɓa miki Mardiyya. Nama manta tare nake da mara kishin kanta balle waninta. Shasha kawai da batasan abinda ke mata ciwo ba”.

   Miƙewa Mardiyya tai ta ɗauka bag dinta da faɗin, “ALLAH ya huci zuciyarki Maah, amma nidai gaskiya na gaya miki, ita rayuwa bata da tabbas. Banga kuma aibun yarinyarnan ba, hasalima yanda take da ƙarancin shekaru idan kika jata a jiki zakisha mamakin ribar da zaki samu akan shi kansa Ramadhan ɗin da kike ganin kamar an nisantaki da shi. Ni na wuce dama zuwa nai na dubaku tunda ban samu shigowa gidan ba koda babbar salla”.

   Ko kallonta Gimbiya Su’adah bata sakeyi ba. Itama saita fice a ranta tana nemawa mahaifiyar tasu shiriyar ALLAH da fatan ganewa. Dan tuni ta fahimci Adda Asmah na ɗaya daga cikin masu rikita lissafinta akoda yaushe. Su kansu wani lokacin haɗata ake dasu taita zuba musu tujara kamar ba ita ta haifesu ba.

   Waɗan nan maganganu na Mardiyya sun sake harzuƙa gimbiya su’adah. Rai ɓace ta shirya bayan sallar zuhur ta nufi sashen Anne. Abinda takan haɗa kwanaki huɗu batai ba. Dan gaida surukai kullum baya cikin tsarinta duk da gida ɗaya suke rayuwa. Anne tayi mamakin zuwan nata amma sai ta danne ta tarbeta kamar yanda suka saba. Babu wani ɓoye-ɓoye gimbiya Su’adah ta sanarma Anne abinda ke a ranta. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button