BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

    Yaji babu daɗi sosai, dan kuwa akwai sakacinsa tunda shine bai nuna maida hankali akai ba matsayinsa na wadda take a ƙarƙashinsa. Bai ce a haɗashi da Raudha ɗin ba, sai dai ya tabbatar ma Bilkisu tayi ƙoƙari idan Raudha ta samu lafiya suje asibitin Maman Jabeer ɗin.

    Haka kuwa akai, bayan kwana biyu ta koma ragas kamar ba’ita ba. Dan haka sukaje asibitin da dare gudun idon mutane. Sai dai tana tare da dogaranta duk da hakan. 

   Sosai Dr Hauwa tai mata gwaje-gwaje na musamman yanda ya kamata. Cikin amincin ALLAH kuma ta gano matsalolin dake tare da Raudha ɗin harda imfection. Magunguna ta bata tare da wani bayanai a rubuce tace ta bama Ramadhan ba nata bane. 

     Kamar yanda akace shi ɗin zata bamawa kuwa bata buɗaba ta ajiye ta cigaba da sabgar gabanta. Tayi fes da ita, da alama kuma makaranta ta fara buɗe mata idanu da wasu abubuwan. Gashi bata wasa sam da karatu sosai take nuna ƙwazo dake bama su Basma dama class mate ɗin nata mamaki. Gashi taƙi yarda kowa yasan ita wacece, koda yaushe fuska a ƙunshe da niƙab. Bata shiga harkar kowa sai su Basma. Wasu na mata kallon girman kai wasu kuma tana ɗan birgesu duk da basu san wacece ita ba. Suma su Basma kuma sun kame bakinsu saboda gargaɗin Ramadhan da Anne. 

    ★Kasancewar yau juma’a da wuri ta dawo school. Ta zube a falo Bilkisu na mata dariya. “Aunty ahaka za’ai karatun kuwa?”.

   Dariya itama Raudha tayi tana ajiye ruwan data sha sosai. “Wlhy bazaki ganeba Aunty. Abunfa babu sauƙi sam. Dan masifa yau text har biyu mukayi ga submitting Assignment ɗin masifaffen malamin nan da nake gaya miki”.

    Cikin dariya Bily tace, “Haka ake shan yaƙi ai Aunty har a cimma nasara. Fatanmu dai ki fito da first class duniya tasan firt lady ɗinmu bata wasa bace”. 

  Dariya Raudha tai tana miƙewa. “Uhhm Aunty Rabani da wata first lady. bara na watsa ruwa nazo naci abinci ko breakfast banyiba yau”. 

   Bayan tayo wankan anan suka baje a falon bilkisu na sake nuna mata aikin yau da mata ƙarin bayani. Salla kawai ke tadasu har magrib. Sam Raudha batasan yau shugaban ƙasa zai dawo ba dan tunda ta shigo gidan basu buɗe tv ba. Bayan sallar isha’i taɗan sake watsa ruwa. Fitowarta kenan a toilet ɗin ta samu wayarta na ringing. Cike da zumuɗi ta ɗaga ganin Fatima. Tun jiya suka sanar mata yau zasuje Hutawa duba Abba (Dauda) da baida lafiya. Taso zuwa amma babu dama har kuka tayi. Sai dai ta ƙudiri niyyar idan Ramadhan ya dawo zata roƙesa alfarmar zuwa itama. Bayan sun gaisa dasu Fatima har dasu Inna Fatisa ke sanar mata ga ƙawarta Zubaida da tazo duba Abban su gaisa.

   Cike da mamaki tace “Zubaida fa? Dama bata mance ina duniya ba?”.

   “Ni na isa first lady ɗinmu. Ranki ya daɗe kin wuce a manta dake ai a ƙasar NAYA ”.

  Zubaida data amsa wayar ta faɗa.

“Mara kirki bazaki canjaba dai?”.

Cewar Raudha cikin dariya.

   Dariya itama Zubaida ɗin tayi, kafin su gaisa a mutunce. Zubaida ƙawartace ta islamiyya. Itama yarinyace mai ƙwazo da sanyin hali kamar Raudha. So da yawama akance halinsu yazo ɗaya ne shiyyasa suke abota. Duk da abotar tasu bawai takai mai tsanani bace da har suka san sirrikan juna musamman ma Raudha da ba’a jin cikinta. cikin tsokana Zubaida ke faɗin, “Halan kin kusa sauke mana babynmu ranki ya daɗe”.

    Raudha tai dariya tana ɗakko kayan da zatasa a Wadrobe. “Aiko gashi ma har yana motsi a ciki, ina fatan kun shirya zuwa suna”.

  Dariya sosai Zubaida keyi. Itama Raudha haka. “Uhm matsoraciya keda rakin nan naki ace cikin ya tsufa za’aji muryarki haka ragal”.

   “Tabɗi mi kika ɗaukeni. Ki shirya zuwa Bingo kiga yanda nake daram kuma ga ƙaton cikin ƴan biyunku tare dani. K cikinfa ba wani wahala kwantar da hankalinki ke huɗu zaki samo mana lokaci guda……”

    “Idan ita bata samoba ke zaki samoshi yau ɗin nan”. A mugun firgice Raudha ta juyo har towel ɗinta na ƙoƙarin kwancewa jin muryar wanda batai zatoba balle tsammani. Sanye yake cikin kananun kaya tausasa gaba ɗaya baƙaƙe. Ya ƙara wani fresh abinsa harda ɗan tumbi alamar hankalinsa kwance yake. Ga sumarsa data sake samun kulawa na gyara. Sam batasan ya dawo gidan ba balle shigowa ɗakin dan ko shigowar motocinsa yau batajiba sam kokuwa hankalintane bai a wajen, ta diririce da rasa inda zata tsoma ranta taji daɗi ganin ita yake nufowa. Har yazo gab da ita bata samu mafitar kare kanta da ko saka hijjab ba. Ta cikuykuyo wasu kaya zata yafa a jikinta ya riƙe yana mai zagayawa ta bayanta ya rungumota jikinsa.

    Wayar ya zare da kallon screen ɗin, tuni dama ta yanke kiran, sai dai hakan bai hanashi ganin da Fatima tai wayar ba. “Ai bansan kina bukatar ƴan uku ba Ustazah da tuni na ajiye ƙawancenmu gefe na baki ajiyarsu”.

   Innalillahi ina ƙasa Raudha ta shige ta huta. Ya sake kanainaiyeta jikinsa da kai hannun kan ɗaurin towel ɗinta zai kamar zai kwance. Da wani irin zafin nama ta wulƙito ta rungumesa jikinta na rawa sai ambaton “Innalillahi…” take har ƙarshe. Shiko mizaiyi inba dariya ba. Sai dai yay dauriyar gimtsewa abinsa ya sake kama towel ɗin data ƙanƙanme cikin hannu ta gaba ɗaya. “Dan ALLAH ka rufamin asiri karka cire Ya Ramadhan. Inba hakaba zan iya rasa numfashina”.

    “Sai in baki nawa mu rayu tare ai”.

Ya faɗa cikin raɗa da wata irin murya mai wahalar fassara ga Raudha.

   Raudha ta sake ƙanƙamesa saboda yanda zuciyarta ke masifar gudu cikin ƙirjinta. Tunda suke bai taɓa mata kalar abun nan ba. Iyakarsa taɓa hanunta fuskarta ya dan sumbata ko laɓɓanta. Amma bai taɓa gwada ɗora hanunsa a wani sashe na jikinta ba sai yau. Dan kuwa a bazata taji saukar hanunsa kan ƙirjinta. 

   “Na shiga uku”.

 “Baki shiga uku ba. Ai maganar kunya kuma ta kare insha ALLAH yau zamu neman ƴan huɗu…………✍

End of book
Leave a comment

Post

Comments

104835043420935222197
Masha Allah muah????????????

16 minutes ago

Contact Us
Arewa Books Publishers

WhatsApp: 09031774742

Email: arewabookspublishers@gmail.com

Navigation
Home
About
FAQ’s
Legal
Privacy Policy
Terms of Service
Social
Facebook
Instagram

Copyright 2021, Arewa Books | ALL RIGHTS RESERVED | Powered by thinkcrypt.io
Menu
Dashboard
My Library
Create Story
Home
About us
FAQ’s
Privacy Policy
Terms of service
Logout

BAKAR INUWA…!!
Chapter: 49

Share:

Report

BAKAR INUWA…!!
View: 8

Words: 3.3K

Chapter 49
49

………Gaba ɗaya ya gama sabauta mata tunani da lafiyar jiki. Dan kuwa cak ya ɗauketa a karon farko na tarihi, bai direta ko inaba sai saman gado. Bai damu da rawar da jikinta keyiba da roƙon da take masa ya zame towel ɗin da taketa faman riƙo kai kace igiyar neman tsira ce. Batama san ta daka tsalle ta ruƙunƙumesa ba. Atare suka faɗa saman gadon. 

    “Haba hajjaju ki bini a hankali mana ai zanyi”.

  Yay maganar yana danne dariya da ƙyar. Itako kuka ta fashe masa da shi da sake ƙanƙamesa. Burinta bai wuce karya kallar mata jiki ba. Tausayi ta bashi dan yasan wannan wani sabon al’amarine daga gareta. Yajawo bargo da hanu ya lulluɓesu yalwataccen murmushi shimfiɗe a fuskarsa. Jin bil haƙƙi kukan take kuma taƙi barinsa yay ko motsi ya sashi lalubar bakinta ya manne nashi. Cikin salon tsantsar zalama da yanayin da yake ciki ya fara binta da salon da batasan zai iya aikatawa ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button