BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

        Yanzu kam Raudha ce ta fara farkawa. Ta buɗe idanunta da sukai mata nauyi matuƙa. Akan fuskar gogan nata ta saukesu. Idanunsa a lumshe, ƙyaƙyƙyawar fuskarsa tayi wani fayau. Duk da haushinsa na murzar da yay mata jiya babu tausayi da takeji haka ta shagala a kallonsa. Itama kanta tasan shiɗin ƙyaƙyƙyawa ne, ga yanayin jin daɗin rayuwa daya tashi a ciki, bai san wahalar komai ba sai ta karatu. Ahankali takai yatsanta saman girarsa data daɗe tana kwaɗayin taɓa tsagar wajen da zuciyarta ke bata wanzami yay masa. Sai dai me, koda ta shafa wajen sai taji santsi irin na tabon ciwo. Mamaki ya kamata, a zuciyarta tace, (Ashe ba tsaga masa akeba tabon ciwo ne) a fili kam mamaki ƙarara ya bayyana gareta da sake girmama sunan UBANGIJI, dan babu mai kallon wajen yace ciwone. Sosai tsagar ta fita da tsari kamar yimasa akai akan sani. A hankali ta sauke numfashi da maida gashin girar data yamutsa masa ta maidashi ya kwanta. Tana ƙoƙarin sake janyewa taji an riƙe hanun. Babu shiri tai saurin rumtse ido tana fisgewa amma yaƙi saki. Nasa lumsassun idanun dake cike da barci ya buɗe a hankali a kanta. Sai kuma ya sumbaci hanun nata daya riƙi ya turashi ƙasan kuncinsa yay filo da shi.  Ɗayan hanunsa kuma ya ɗaura a jikinta saitin ƙugunta.
     “Good morning sweetheart”.
  Wani bala’in kunyane da yafi na ɗazun da asuba ya lulluɓeta. Tai ƙoƙarin kauda kanta yay azamar tallafosa da hanunsa dake a ƙugunta ya hanata hakan. Cikin ɗan marairaicewa yace, “Ki amsa min mana Baby luv”.
        Da ƙyar ta iya buɗe baki tace, “Ina kwana”.
      Ahankali ya shafo kanta tun daga sumar gaban goshin har zuwa ƙeya yana ɗan murmushi. “Ya jikin ki? Duk da nima dai ya kamata a tambayeni nawa kodan yaƙushi da cizon dana sha”.
      Ina ƙasa Raudha ta shige ta huta. Tai ƙoƙarin jan hanunta da yay filo da shi amma ta kasa. “Kibar wani gulma Ustazah, nasan kina son mijinki kar kiyi sake wata ta ƙwace miki ni”.
      Kanta tai ƙoƙarin sinnewa a jikinsa. Yay murmushi yana riƙeta ya hana hakan. “Gara na faɗa miki gaskiya matsayina na abokinki babban amininki. Bazan so a miki kishiyaba kina ƙawata ta hanun damar, dan sai na fiki kishi kilama kullum dani zaki dinga cin dabe da ita a gidan ga muna lakaɗa mata duka ko ya kikace?”.
       Duk yanda taso riƙe dariyarta ta kasa. Ta saki murmushi tana turesa. “Kai Ya Ramadhan….”
      “K nifa bana wani kalar dangi ƙannena sun isheni, inama laifi da muke abota niba yayanki bane”.
   “Toni ai bazan iya faɗar sunanka ba”. Tai maganar tana sake son cusa kanta a ƙirjinsa. Haɓarta ya riƙo ya ɗago fuskar tata da sumbatar laɓɓanta. Cikin sake ƙanƙan da murya yace, “To basai ki canjamin da wani ba. Amma sam bana son Yayan nan kamar wani zamanin iyaye da kakanni, bayan kuma jiya na gama turmusheki a gadon na….”
       Dariya ta ɗan ƙyalƙyale da shi tana kaimasa ƙaramin duka a ƙirji. Shima sai ya rungumeta yana murmushi. Zuciyarsa fes da farin ciki.

       Duk yanda taso zamewa kar suyi wanka tare bai bata damarba. Amma kuma taƙi sakin jiki haka ya gama nashi ya barota a bayin. Sanda ta fito yana zaune yana waya. Dan haka tai wuff ta fice a ɗakin bayan ta saka hijjab.
       Ciwo take ɗanji kaɗan-kaɗan a ƙasanta amma ta daure ta shirya cikin wani material da yay mata ƙyau sosai da fiddo kalar fatarta. Tayi fayau da ita daka ganta kaga amarya, sai dai fuskar babu walwala sosai ga idonta duk wanda ya kalleta yasan taci kuka. Yunwa takeji amma batajin son cin abinci kuma. Bakinma ɗaci takeji yana mata kamar mai malaria. Tana fesa turare ya shigo, sanye yake cikin shadda ash color datai bala’in masa ƙyau. Sai maiƙo take da ɗaukar iadanun mai kallo. Ya murza hula baƙa data fiddo ainahin hasken fatarsa da ƙyallin angwanci. Duk da waya ya shigo yanayi hakan bai hana Raudha shiga jin kunya ba, ya ƙaraso inda take yana riƙe kwalban turaren da kunya tasata cigaba da fesa ƙasa-ƙasa dan karya tada mata asthma. Ajiyewa yay saman mirror ɗin ya riƙe hanunsa cikin nata idanunsa a saman ƙyaƙyƙyawar fuskarta da yakeji kamar ya haɗiyeta. Ga ɗaurin datai ya sake fiddo ƙyanta kamar dai ya haɗiyetan ya huta kawai. Ita dai kanta a ƙasa tana shaƙar daddaɗan ƙamshin turarensa na Dolce & gabbana daya gauraya da burberry brit. shiko yanata wayarsa da murza yatsun hanunta.
      Tsawon lokaci harta fara gundura da tsaiwar kafin yay sallama da wanda yake maganar wanda ta fahimci kamar akan harkar kasuwanci ne. Saman mirror ya ɗaura wayar da kamo fuskarta cikin tafukan hanunsa ya sumbaci goshinta, sai kuma ya sakko a hankali ya sumbaci lips ɗinta dake ƙallin lips gloss. Shima ya duƙo kaɗan yana nuna mata nasa kumatunsa da goshi.
       “Kai Ya Ramad……”
Sai kuma ta kasa karasawa saboda ɗallin daya bama bakinta. “Dole na fara hukunta wannan bakin idan yaya ɗin nan bai fita a cikinsa ba”.
     Hannu tasa ta rufe laɓɓanta da zafi ya maimaye idonta na cika da ƙwalla. Hannunta ya kamo ya zuba mata link ɗinsa da agogonsa hublot dayay mata ƙyau sosai kalar ash. Batai musu ba, dan koba komai tasan aiki garesa lada ne. Links ɗin ta fara saka masa sannan agogon.
     “Thanks bestie”.
Ya faɗa a hankali idonsa a kanta. Sai kuma ya janye yana ƙoƙarin barin wajen mirror ɗin. “Ƙarasa mu wuce so nake na more gida sosai lokaci nata tafiya”.
       Duk da batasan ina zasu ba cike take da ɗokin tafiyar. Ta ɗauka hijjab da zai shiga da kayanta ta saka tare da haɗa abinda zata iya buƙata a karamar handbag. Tana duba takalmi a akwatin lefenta ya sake shigowa. Bai yi magana ba yabi duk kayan wutar ɗakin ya kashe komai. Dai-dai tana gamawa yake faɗin, “Ko breakfast bazamu tsaya yiba mayi acan kawai”.
     Kanta ta jinjina masa, sai dai har yanzu taƙi yarda su haɗa ido. A hankali ya matsa gefenta yay musu hoto bayan ya faɗi abinda ya sakata ɗagowa ta kallesa a ɗan tsorace. Sai hoton ya bada wani style mai ƙayatarwa kamar anyisane da shiri.

        Bayan sun sallami su Mama Ladi suka fito compound inda jerarrun motocin da zasu fitan suke. Yau ce karo na farko da zasu fita tare da shi a bayyane. Sai gaisuwa ake miƙa musu cike da ɗunbin girmamawa wadda har Raudha takejin babu daɗi akanta. Dan kuwa da yawansu sun haifeta da girmarta. A motar da tafi kowace mota ƙyau da ɗaukar idanu ga tutocin ƙasar naya a jikinta suka shiga. Kafin wanda zasu musu rakkiya Taura house ciki harda cos da wasu ministers uku suma suka shiga. Ba wani tafiya mai tazara bace ba, amma ta fahimci an bama fitar muhimmanci matuƙar dan har a redion motar da driver ya kunna saiga sanarwar yau shugaban ƙasa Ramadhan B. Hameed Taura zaije hutun ƙarshen shekara gidansu a karo na farko tun bayan hawansa mulki na watanni kenan. Anan aka saka zantukan mutane daban-daban daketa masa addu’a shi da iyalinsa akan yasha hutu lafiya cikin farin ciki.
     Sosai ya ƙara samun nutsuwa a ransa dan kuwa zuwa yanzun ayyukan daban-daban da suka faro na talakawa sun kankama matuƙa. Abinda zai matuƙar birgeka duk wani mai kwangilar gwamnati sunansa da aikin da zaiyi a bayyane yake ga al’umma. Hakan yasa yake ƙara samun addu’a ga talakawa dan kuwa babu wani ƙunshe-ƙunshe balle a cucesu a ƙiyi musu aiki kuma su rasa daga ina matsalar take. Kai hatta kuɗin da aka bama masu kwangilan da wanda sukebin bashi sai sun kammala a cika musu duk an sanar da duniya babu wani rifa-rufa. Hakan da yay ya matuƙar taimakawa da saka tsoro a zukatan masu kwangilar dan sun san kam inma basuyiba sune a ruwa tsundum. Gashi har adadin watanni ko shekarun da aikin zai ɗauka kowa ya sani a bayyane. Bashi kaɗaiba hatta da gwamnoni da ƴan majilusu, ciyamomi, kansiloli duk aikin da zakai ma ƴan yankinka a jihohin nan 41 dolene ka sanar da komai talakawa su sani.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button