BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Tarba ce ta musamman tawagar shugaban ƙasa ta samu a Taura house, dan kuwa wannan shine karo na farko da yazo gidansu a bayyane kuma da shirin kwanaki. Sosai bakin Anne da su Yafendo ke a buɗe, ganinsa ya musu wahala yanda suke buƙata tunda ya hau mulkin nan. Raudha dai gaba ɗaya a takure take. Jitake kamar kowa zai iya gabe abinda ya faru a tsakaninsu jiya. Ga anne da su Yafendo sai nan-nan suke da ita kowa na saka mata albarka. Bayan gaishe-gaishe da addu’oi Ramadhan da su Bappi suka fita salla dan tawagar datai masa rakkiya sun koma. Sai dai Taura house tako ina zagaye yake da securitys kai gaba dayama anguwar. Dole ne ka shaida shugaban ƙasa na nan koda matakan tsaron dake kewayen anguwar baki ɗaya, kai kace ko ƙuda bazasu bari ya gitta ba.
Da ƙyar Raudha ta iya tsarki da ruwan sanyi tsabar zogin da wajen ke mata zuwa yanzun. Har jin kanta take kamar wadda zazzaɓi zai saukarmawa. Anne na lure da yanayin nata sai dai batace komai ba dan zuciyarta bai kai ga zargin abinda ke faruwa da Raudha ɗin ba kai tsaye. Gashi tunda suka shigo dama yanayin idanunta na wadda taci kuka ya tsayama Anne a rai. A ɗakin Anne sukai salla duk da kuwa an gyara sashen Ramadhan ɗin tsaf domin su.
Bayan idar da salla gaba ɗaya gidan ƴaƴa da iyaye aka haɗu domin yin lunch a katafaren falon Bappi. Abincine mai rai da lafiya da gamsarwa a wajen iri-iri. Anyi hakanne kawai domin walimar zuwan Ramadhan ɗin da Raudha. Sai yanzu Raudha taga gimbiya Su’adah da sauran matan gidan, dan kuwa bata shiga gaishesu ba Anne tace sai zuwa yamma sun huta. Sai dai shi Ramadhan ya shiga ya gaida Gimbiya Su’adah ɗin kawai ganin bata a masu fitowa tarbarsa. Kasancewar salla zai fita yasa bayan gaisuwa babu wani abu daya shiga tsakaninsu ya fito suka fice massallaci.
Har ƙasa Raudha takai tana gaishe da iyayen. Kowa ya amsa mata cike da kulawa banda gimbiya Su’adah da ko kallon inda take bataiba. Ƙasan ranta wani takaicine da baƙin ciki da kishin yanda Raudha ta kara murjewa komai na halittar jikinta ya ƙara girma sai kace ƴar 25years. Ga tsadadden material ɗin dake jikinta wanda ta tabbatar za’a iya sayen abincin watanni na gidansu Raudhan da kuɗinsa. Ita saima taga kamar yarinyar tana wani jin kanta.
Oho Raudha batasan tanai ba. Ita abinda ya dametama ya isheta. Komai yinsa take cike da dauriya. Abincinma tana matuƙar bukatarsa amma ta kasa ci saboda bakinta babu daɗi. Sai juya spoon take a ciki tana ɓata fuska. Ramadhan na lure da ita. Kuma hankalinsa na kanta. Burinsa su haɗa ido amma taƙi kallon ko inda yake. yana zaune ne tsakkiyar Bappi da Pa. Sai Anne a gefensu da Yafendo da Inna. Ita kuma tana kusa da Bilkisu da Zainab ne. Su Lubnah sai faman jan tsaki suke ƙasa-ƙasa suma kamar su halaka Raudha sukeji musamman ganin suturar data sanya kosu da suka tashi gidan kuɗin basu saka ba. Tsadajjen agogon hanunta da zabba da bangles kawai duniyane. Balle ita kanta data kara wani kyau na musamman da su sam basa lura da shi sai yau duk da kuwa suna tare da ita.
Da gangan Ramadhan yay kamar ya sarƙe yaja gyaran muryar data saka kowa maida hankalinsa a kansa ana rige-rigen jera masa sannu. Bappi dake shafa masa baya kamar wani ƙaramin yaro ya kai masa kofin ruwa bakinsa yana masa sannu. Kaɗan yasha yana jinjina musu kai da satar kallon Ustazahr tasa. Sai dai bata yarda ta kallesa ba tun bayan ɗagowar datai kamar yanda kowa ya ɗago lokacin daya sarƙe. Ita sanun tatama a kan laɓɓa tai masa ta tsuke bakinta. Ganin dai ba samun yanda yakeso zaiyi ba sai ya haƙura. Takaici ya cika Aynah da duk hankalinta ke akansu. Hakama Muneera da idonsu akan yayan nasu da abinda yake yawan kallo. Jin hawaye na neman zuboma Aina’u itace ta fara mikewa wai ta ƙoahi. Babu wanda yace mata komai, hakan sai ya ƙara baƙanta ranta. Dan a ganin bai kamata aƙi bata kulawaba kodan mata ta biyu da take shirin shigowa ga ɗansu kuma ɗan uwanta.
Raudha da dama ba abincin take ci na kirki ba itace ta ukun tashi a wajen. Ramadhan ya ɗan bi yanda take tafiya da kallo. Hannu ya kai ya dafe goshinsa a zuciyarsa yana ayyana (Yarinyar nan zata tonamin asiri fa). Bayan sun kammala kowa ya tashi a wajen yaso janta sashensa dan ya fahimci mugunta taima kanta bata shiga ruwan zafin daya haɗa mataba da asuba, bayajin kuma da safe ta sake kula da kanta. Takaicin kansa yaji dabai tsaya akanta ya taimaka mataba duk boranta. Sai dai duk yanda yaso ya keɓe da ita ɗin hakan bata yuwuba dan su Basma na zagaye da ita a falon Anne suna hirar school duk da ba wani saka musu baki take sosai ba. Sai dai ganin Inna da Yafendo da Anne na wajen ya sashi haƙura ya shige shi acewarsa zai ɗan huta………..✍
Ayi haƙuri da jina shiru, banda lafiya ne.
Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹????♀️⛹????♀️????
ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA????????????????????
1~ KUFAN WUTA????
Safiyya Huguma
1~ BAQAR INUWA????
Billyn Abdul
1~ RAYUWAR MACE????
Hafsat Rano
1~ MASARAUTA????
Miss Xoxo
1~ NOOR ALBI❤????
Mamuhgee
Guda 1????300
Guda 2????400
Guda 3????500
Guda 4????700
Guda 5????1k
ZAKU BIYA KUDINKU ANAN????????
Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank
Number shaidar biya????????
09032345899
KATIN MTN????????
09166221261
JAMA’AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan????????
Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F
ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA????????
+227 95 16 61 77
TEAM ZAFAFABIYAR????????????????
BAƘAR INUWA…????????
Da ɗumi-ɗuminsa????????????????????????????????
Please
Follow me
Share
Comments akan abinda ya shige maka duhu.
_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar????????????????????????_
YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za’a cike Form ɗin kamar haka: –
Enter your name: (Cikakken sunanki)
Enter your mail: (Email ɗinki)
Enter an username (Sunanki)
Enter your password: ( misali 12341234)
Confirm password: (misali 12341234)
Sai a taɓa Sign Up shikenan an buɗe account a ArewaBooks????????????.
Continue with Google – Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za’a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
Register – Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.
AREWABOOKS LINK kai tsaye
Masu iPhone
Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App… Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine.
MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER
+234 903 177 4742
Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan????????????????????????.
ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????
Typing????
Episode 51
……..Anne ta cigaba da maida hankalinta ga Raudha har zuciyarta ta fara hasashen abinda yake dai-dai. Sai dai ta danne komai batace ba har la’asar da aka tashi salla. Ramadhan ya fito sanye cikin ƙananan kayan daya canja suka sake fita massallaci da Bappi dan Pa na sashensa shima da iyalinsa. Har lokacin su Rumaisa na tare da Raudha harma sun kara samun yawan ƴan hirar su Sumayya. Magana kawai yay musu su tashi suje suyi salla ya wuce abinsa yana satar kallon Raudha da tun fitowarsa tai ƙasa da kai tana wasa da yatsun hanunta da jan lalle ya ƙawata dogayen faratanta.