BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

       Babu wata walwala Ramadhan ya koma wajen Raudha, dan yasan ma’anar shirun mahaifiyarsa. Tuni ita har tayima shirin barci. Tana zaune ne a kan gadon tana assignment ɗin makaranta da aka basu na cikin hutu, sai dai sanye take da hijjab a saman kayan barcin nata. A kallo guda ta fahimci ransa a ɓace yake, cikin dauriya ta masa sannu. Bai amsa ba sai dai ya kwanta a gadon tare da ɗoro kansa saman cinyarta bayan ya ture takardun gabanta gefe.
        “K dole kin zama ƴar boko ko?”.
Ɗan murmushi tayi kawai dan yanda yay maganar kamar mai son huce haushinsa akan bokon nata ne. Cikin san kauda masa damuwarta tace, “Harka tunamin Abbanmu. Idan mukai masa laifi koya tashi baida ko sisi sai ya hana kowa zuwa makarantar boko ranar. Ya ringa faɗin, “Anma fasa bokon, daga yau bazaku sake zuwa ba, bandama shegantaka irin ta bature yabi duk ya katantane duniya ya hana kowa zaman lafiya, komai bazaka samesa yanda kake muradi ba sai kayi wani abu shege a.b.c.d kai nifa shiyyasa ma ana kaini ina tserowa a makaranta da ƙyar na haɗa sakandire ɗin ma”.
      A bazata dariya ta ƙwace masa. Har haƙoransa na bayyana baki ɗaya sai dai ya kai hannu yana karewa. “ALLAH na lura Abba ɗan darune?”. Ganin yanda ya karɓi zancen ya saka Raudha dake nata ƴar dariyar itama faɗin, “Tab damma baka sanshi bane. Wlhy duk randa darun Abba ya tashi gidan nan ranar kowa sai yaji a jikinsa. Ko ruwa ka cika kofi zakasha sai yace ka ƙara masa talauci kana baƙin cikin ya zama mai kuɗi”.
     Yanzu kam sosai yake dariya. Raudha da farin ciki ya cikata itama ta tura yatsunta duka a cikin gashinsa tana masa susa. Nan ta shiga bashi labarin M. Dauda sai dai na hankali wanda tasan mutuncinsa bazai zube a garesa ba. Cikin amincin ALLAH sai gashi ƙaunar mahaifinta ta sauka masa a rai har yanajin sassaucin takaicin halayyarsa tada da bincike yazo da ita.
       “Ya kamata ma muje mu gaishe da Abba Hutawa gaskiya”.
Cak Raudha ta dakata da susan da take masa a cikin gashi ta tsurama ƙyaƙyƙyawar fuskarsa ido idanunsa a lumshe suke yayin da hannayensa duka ke harɗe a ƙirjinsa yana kwance rigingine. Yanda ya nutsu zai baka tabbacin susar da take masa cikin gashi na masa daɗi. Ya buɗe lumsassun idanunsa da suka canja launi a hankali ya zuba mata su. Gira yaɗan ɗaga mata yana sassanyan murmushi. “Yadai naji kinyi shiru Ustazah?”.
     Hawayen da suka ɗan cika mata ido ta haɗiye, cikin ƙaƙaro murmushin itama tace, “Nagode da karamcinka”.
        “Cmon johre. An gaya miki Abban nakine ke kaɗai banson iyayi”.
   Yay maganar yana dungure mata hanci da ƙoƙarin miƙewa zaune. Toilet ya shiga, ita kuma ta sauke ajiyar zuciya da hawaye lokaci guda. Wani abu mai muhimmanci na sukar ranta. Koda ya fito wanka cayay ta kawo masa sauran namansa. Dan bacin ran daya shigo da shi ta riga ta gusar da shi. Kawo masa tai harda kunun, yako ci abinsa yay ƙat sannan ya koma bayin yayo brush, koda ya dawo assignment ɗin ta nuna masa inda bata gane ba.
       “Ustazah! Kibar batun Assignment ɗin nan nima inada nawa Assignment ɗin mai kawo lada ma.”
           “Please Ya Ramadhan dafa an koma hutu idan ALLAH ya kaimu zamuyi submitting”.
     Gadon ya hawo yana ɗaure igiyar rigar barcinsa. Ya zare mata hijjab ɗin jikinta sannan ya ɗauka takardar data rubuta questions ɗin da amsar data rubuta daban na wanda ta gane. “Yarinyar nan kanki fa naja”.
Ya faɗa cikin ɗage mata gira. Murmushi kawai tayi da maida kanta ƙasa. Shima hankalinsa ya sake maidawa ga takardun yana faɗin, “Ai gyaran ma kaɗanne”. Bayani ya shiga mata dalla-dalla harma akan abinda bata tambayesa ba, dan shima yayi course ɗin sanda yana jami’a. Sosai taji daɗin bayaninsa har tana sake zaƙulo masa wasu tambayoyin. Sai dai taƙi sakewa da jikinta sai faman karewa take da hannu kamar mai jin sanyi. Tsaf yana lure da ita amma yay kamar bai gani ba. Zata sake jeho masa wata tambayar ya turo kayan karatun nata ƙasa da jawota jikinsa yana faɗin, “K ni na gaji da aikin bautar bature zo kiji wata magana”.
    Gabantane ya shiga faɗuwa. Sai dai ko saurarenta baiyiba yaja musu bargo ya matseta a jikinsa yana shinshinar wuyanta da kai mata kiss’s……….✍

Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹????‍♀️⛹????‍♀️????

ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA????????????????????

1~ KUFAN WUTA????
Safiyya Huguma

1~ BAQAR INUWA????
Billyn Abdul

1~ RAYUWAR MACE????
Hafsat Rano

1~ MASARAUTA????
Miss Xoxo

1~ NOOR ALBI❤‍????
Mamuhgee

Guda 1????300
Guda 2????400
Guda 3????500
Guda 4????700
Guda 5????1k

ZAKU BIYA KUDINKU ANAN????????

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya????????

09032345899

KATIN MTN????????

09166221261


JAMA’AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan????????

Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F

ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA????????

+227 95 16 61 77

TEAM ZAFAFABIYAR????????????????


BAƘAR INUWA…????????

Da ɗumi-ɗuminsa????????????????????????????????

Please
Follow me
Share
Comments akan abinda ya shige maka duhu.

     _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar????????????????????????_

YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za’a cike Form ɗin kamar haka: –

Enter your name: (Cikakken sunanki)

Enter your mail: (Email ɗinki)

Enter an username (Sunanki)

Enter your password: ( misali 12341234)

Confirm password: (misali 12341234)

Sai a taɓa Sign Up shikenan an buɗe account a ArewaBooks????????????.

Continue with Google – Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za’a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

Register – Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.

AREWABOOKS LINK kai tsaye

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3

Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com

Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App… Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine.

MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER

+234 903 177 4742

Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan????????????????????????.

ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????
Typing????

Episode 55

……….Yau ɗin ma dai kukan tasha sosai fiye dana ranar ma, a ganinta yauɗin ma babu banbanci da shekaran jiyan. Shidai aikinsa lallashi da jinjina ragwantakarta, duda dai yasan shi ɗin bana wasa bane. Bayan sallar asuba koda ya nuna sake ziyartarta kuka ta saka mishi iya gaskiyarta tana roƙonshi idan ya sake mutuwa zatai ita dai. Ta bashi tausayi ta bashi dariya kuma. Amma sai ya gimtse da nuna mata baifa san zancen ba a haka zata saba ai. Kuka sosai ta dingayi tana yarfe hannaye kamar wata ƙaramar yarinya. ALLAH ne ya taimaketa Bappi yay kiransa zasuyi magana, dan dama shirin office zaiyi daga Taura house can ya nufa. Ita kuma sai ƙarfe ɗaya zata wuce gaida su asabe daga can ta zarce gida.
       Badan yaso ba dole ya miƙe ya zura doguwar rigar jallabiya ya fita batare daya kalli Raudha dake maƙure cikin labule ba tana sharar hawaye. Ganin ya fice ta faɗa toilet, wanka tayi da ƙara gyara jikinta dan ita dai harga ALLAH zafi takeji sosai. Yau dai anyi jarumta an shiga ruwan zafi tanata raki ita kaɗai. Koda ta fito harta shirya ta gyara ɗakin bai dawo ba. Dan haka ta saka hijjab ta fita gaida jama’ar gidan.
     Kamar ko yaushe bata wani samu tarban arziki ga gimbiya Su’adah ba. Sai ma zageta tas da Lubnah da Aynah sukayi wai kwana uku batazo ta gaishe da Maah ɗin ba. Bata da abin faɗa dan tasan ita mai laifi ce. Yau ma da taimakon Bilkisu ta baro sashen bayan ta zage Aynah da Lubnah duk da kuwa duk sun girmeta. Masifa taitaima Raudha akan lokaci yayi da zata ƙarfafa ranta tabar zama su Lubnah na takata yanda suke so koda agaban Maah ne. Maah uwace, amma su ai ƙannene a gareta koda sun girneta tunda kanen mijinta ne. Murmushi kawai Raudha tayi amma komai batace ba.
        Ƙin komawa tai part ɗinsu duk da Anne tace Ramadhan ya baro wajen Bappi, suna nan a falon suna taya Anne shirya table Ramadhan ya fito cikin shirin office. Ɗanyar shaddace golden yollow a jikinsa daketa maiko harda babbar riga, sai dai bata cika girma ba dai-dai irin ta matasan zamani da suke yayi. Sai baƙin takalmi chukka boot da hula tangaran daketa ɗaukar idanun mai kallon. Ko kunya babu ya miƙama Raudha dake ƙoƙarin gyara mayafinta agogonsa zenith wai ta saka masa. Sai wani faman ɗaure fuska yake. Sai da taɗan dubi sashen da Bilkisu da Anne suke taga sun ɗauke idanunsu kamar basu san mike faruwa ba sannan ta amshi agogon ta ɗaura masa kunya kamar ta nutse.
      Kona gode babu ya raɓata ya wuce zuwa dining. Ta ɗan bisa da kallo ranta fes dan gara wannan fushin da azabar da tasan zata sake ɗanɗana a hanunsa. Anne ce ta sakata dole ta haɗa masa abinci, sannan suma suka zauna har Bilkisu da data karya anan.
     “Yaya kamar bakajin daɗi?”.
Cewar Bilkisu cike da kulawa. Anne da tun ɗazu hankalinta na kansa itama dai kallonsa tai. Ya ɗan yamutsa fuska da sake tsuketa. Sai dai komai baice ba. Anne ce ta sake maimaita masa tambayar Bilkisun. Cikin ɗan haushi-haushi yace, “Kawai bana son fitar ne”.
     Ƴar dariya Anne da Bilkisu sukai da lallashinsa. Raudha kam da tasan ainahin fushin murmushi kawai tai taƙi yarda kuma su haɗa ido. Shi ya fara miƙewa. Harya gama sallama da Anne zai wuce ya faki idonta ya sakarma Raudha ranƙwashi akai.
    Ba shiri ta saki karamar ƙara. Gaba yay abinsa ko waiwaye babu, Anne da komai ya faru akan idonta tace, “Mugunta dai babu ƙyau wlhy Ramadhan mita maka?”.
      Ƙin tankawa yay, sai ya ɗagama Anne yatsunsa biyu alamar bye. Ita dai Bilkisu dariya kawai take ranta fal nishaɗi haƙarsu ta kusa cimma ruwa. (Batasan tuni tacin ba itace bata da labari). Bayan mintuna kaɗan suka jiyo jiniyar tafiyar motocinsa. Hakan ya bama Raudha damar bararrajewa suka daura hira da Bilkisu da Anne. Kusan ƙarfe goma baƙuwar Anne ta iso……
         Sosai kunya ta lullube Raudha lokacin da hajiya take bayanin kayan da Anne tasa aka kawo mata nagartattu haɗin sakwattawa birnin shehu tun daga ƙasar Nigeria. Hajiya. Bata wuce ba sai kusan sha biyu, a lokacin Raudha ma ta mike taje tai shirin dan lokacin tafiyarsu ya gabato. Umarnin Anne ta bi na zuwa yima su Gimbiya su’adah sallama. Bayan ta kammala da kowane part harsu Yafendo ta nufi part ɗin surukarta a ƙarshe. Ita kaɗai ta samu a falo hakimce cikin kwalliya sai zuba kamshi take, duk da tasan bata kaunarta ta daɗe da bata lambar girma da yabo na iya tsara kwalliya da ado, dan sosai jikin gimbiya Su’adah ke ɗaukar wanka, ƙyaƙyƙyawa ce itama gata fara tas masha ALLAH, matsalarta kawai bata fara’a kamar wata sojiya????.
      Kamar ko yaushe data gaisheta bata amsaba. Ta watsar da ita a durƙushe tsahon muntina, Raudha data ga karta makara tai mata sallama zata mike amma saita dakatar da ita. Cike da gadara da tsanar data kasa haɗiyewa tata tace, “Kin dage sai kin zauna da Ramadhan duk da na nuna miki hanyar salama kin runtse idanunki. Okay fine, sai ki shirya shigowar Aynah ku goga kishi, mai sa’a ta haye”.
     Wani irin dummm kunen Raudha ya ɗauka. Ta ɗan ɗago ido ta dubi gimbiya Su’adah. Sai dai wulaƙantaccen kallon data maka mata ya sata maida idanun ƙasa dole. wani irin abune yake sukar zuciyarta mai zafi da batasan ma’anarsa ba. (Kishi?) kai ina na kishi bane, domin *babu so miya kawo kishi? maybe tsoro no kawai. To amma abinda takeji baya kama da tsoro sai jin ɗaci. Dan har wata hajijiya takeji kamar tana yawo da kanta a sararin samaniya. Sai dai ta danne a nutse taima Maah godiya da sallama ta mike ta fita duk da bata amsa mata ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button