BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

????????????aimun afuwa. Jin daɗi baya dorewa sai da ƙaddara. A lokuta da dama jarabawa itace ke ƙara. kai mutum ga ajin nasara. Ba’a samun wannan nasarar kuma sai da haƙuri da juriya.????????
BAƘAR INUWA…????????
Da ɗumi-ɗuminsa????????????????????????????????
Please
Follow me
Share
Comments akan abinda ya shige maka duhu.
_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar????????????????????????_
YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za’a cike Form ɗin kamar haka: –
Enter your name: (Cikakken sunanki)
Enter your mail: (Email ɗinki)
Enter an username (Sunanki)
Enter your password: ( misali 12341234)
Confirm password: (misali 12341234)
Sai a taɓa Sign Up shikenan an buɗe account a ArewaBooks????????????.
Continue with Google – Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za’a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
Register – Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.
AREWABOOKS LINK kai tsaye
Masu iPhone
Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App… Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine.
YADDA ZAKA SIYA LITTAFI A AREWABOOKS????????????????????????????????????????
Recharge – inda ake shiga domin saka kudi cikin account.
Balance – Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin kasuwar ArewaBooks.
Credit/Debit Card – Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku.
A inda (Enter your amount) za’a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba “Proceed”. Zaibude muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye (instant).
Akwai wasu hanyoyin saka kudi a ArewaBooks account kamar:
Bank Transfer
Airtime Transfer
Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai 1hour za’a gansa a Balance.
Bank Transfer – kamar yadda akwai bayani a sama da kuma account number ArewaBooks.
Account No – 1220077999
Account Name – Arewa Books Publishers
Bank – Zenith Bank
Bayan anyi Transfer dinne sai a cike wannan Form din:
Amount Paid: – Nawa aka tura?
Name used for transfer: – sunan da aka saka wajan turowa
Transferred time: – lokacin da aka turo
Name of bank: – sunan bankin da aka turo dashi
Deposit date: – ranar da aka turo
Sai ayi SUBMIT.
Airtime Transfer – muna bada shawaran ayi amfani da Debit Card kokuma Bank Transfer akan Airtime Transfer , amma idan yakama babu mafita saishi tau muna amsar:
MTN,
9Mobile
Glo
Airtel
Amma kamar yadda akayi rubutu a sama afara tuntubar ArewaBooks a WhatsApp domin akwai percent da ake cirewa na canji(convert) kafin kudinka yashiga Balance.
WANNAN SHINE BAYANAN
MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER
+234 903 177 4742
Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan????????????????????????.
ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????
Typing????
Episode 57
……….“Innalillahi wa’inna’ilaihirraji’un aunty Raudha jini kuma?”. Bilkisu data shigo ɗakin a birkice ta faɗa tana ƙarawo gareta. Kamata tai suka nufi toilet, ta haɗa ruwa mai ɗumi ta taimaka mata ta wanke fuskar da hanunta, jinin dai bai tsaya ba. Sai dai sun tare da tissue. A bakin gado ta zaunar da ita, ta ɗakko first aid box ta shiga ƙoƙarin tsaida jinin, da ƙyar aka rufe wajen da audiga da bange. Ita dai Raudha babu abinda take sai sakin ajiyar zuciya.
“Aunty Raudha wai garin yaya? Ina Yaya kuma?”.
Komai Raudha kasa cemata tai, sai hawaye take sharewa kawai. Hankalin bilkisu ya ƙara tashi, sai dai ta barta bata sake maganaba. Tana niyar mikewa ta maida first aid box ɗin ma’ajiyarsa ta lura da kumbirin hanun Raudha kuma. Gaba ɗaya saita sake ruɗewa ta kamo hanun tana kallo. “Ya ALLAHU, nan ma ai ciwon kikaji Aunty! Kinga bara na kira Yaya da mama ladi dan ta iya gyaran ƙashi”.
Ita dai Raudha komai batace ba, babu jimawa suka dawo da mama ladi, bilkisu ta sake fita. Duk da ta fahimci akwai matsala ƙofar Ramadhan ta dingama knocking a ɗarare. Shiru babu ko motsi, sai ta ɗan tura ƙofar ta leƙa. Gabanta ne yay masifar faɗuwa hango Yayan nasu zaune akan tum-tum ya dafe kansa. Babu shiri ta shigo ɗakin da sassarfa. Muryarta har rawa yake ta durƙusa gabansa “Yayanmu dan ALLAH mike faruwa ne? Aunty Raudha taji ciwo sosai wlhy har a hanunta mi’akai mata”.
Da ƙyar ya samu damar fisgo kalmar innalillahi… A cikin zuciya. Ya ɗago jajayen idanunsa ya zuba kan Bilkisu datai matuƙar razana. Dan rabon da su gansa a irin wannan yanayin tun rasuwar su Haseenah. Baya taɗan ja jikinta na rawa. Shima sai ya cije lips sinsa da ɗago hanunsa ya kalla. Sai kuma ya dafe kansa dake matuƙar juya masa. Kusan minti ɗaya ya sake ɗagowa ya dubi Bilkisu da gaba ɗaya ta gama tsorata. Cikin yanayin damuwa yace, “Ina Ameenatun?”.
“Tana ɗakinta Yaya, nabar Mama ladi zatai mata gyara a hanunta dan harya kumbura, ga goshinta ya fashe da ƙyar na iya tsaida jini….”
Ai bama ta ƙarasa ba ya miƙe hankali tashe. Sai dai hakan bai hana bayyanar nutsuwarsa ba. Fita yay Bilkisu tabi bayansa. Kai tsaye ɗakin Raudha ya nufa, sai dai yana ɗaura hanunsa bisa handle ɗin ƙofar ya dafe kansa da yay masifar sara masa. Da sauri ya shiga girgiza kansa yana ja da baya. Barin wajen yay ya sake komawa hanyar ɗakinsa. Bilkisu ta bisa da sauri tana kiransa. Wata razananniyar tsawa data sakata jan birki ya daka mata, yay shigewarsa ya bugo ƙofar da ƙarfi har Bilkisu na zabura.
Kuka Bilkisu ta fashe da shi. dan kuwa ta fahimci lallai akwai matsala, sai da tayi mai isarta ta koma ɗakin Raudha. Ta jiƙe sharkaf da zufa kamar ba ac a ɗin saboda gyaran da mama ladi tai mata. Mama ladi dake naɗe mata hanun da bandage ta dubi Bilkisu. “Taji ciwo sosai, dan gocewar ƙashi ta samu. Garin yay hakan?”.
Kafin Bilkisu ta bada amsa cikin share hawaye Raudha tace, “A toilet ne na zame”.
Sannu Mama ladi ta shiga jera mata. Bilkisu dai wani irin tausayin Raudha ɗinne ya lulluɓeta. Dan ta tabbatar daga yayansu aka samu matsalar musamman da taga shatin yatsu a fuskar Raudha alamar marinta akai. Magani ta sha ta kwanta bayan tayi sallar magrib da isha’i, babu jimawa kuwa barci mai nauyi yay awon gaba da ita. Bakajin komai sai ajiyar zuciyarta.
Tagumi Bilkisu tai zuciyarta nata kaikawo. tama rasa ina zata kama akan wannan al’amari. Kusan tara na dare sai ga kiran Basma ya shigo mata. Da farko kamar bazata ɗaga ba sai kuma ta daure ta ɗaga wayar na gab da tsinkewa. Wani irin dummm kunen Bilkisu yayi jin abinda Basma ta faɗa. Muryarta har rawa take wajen maimaita “Basma shi Yaya Ramadhan ɗin da kansa yace zai auri Aynah?”.
Daga can Basma tace, “Wlhy kuwa Aunty B. A gabana Maah tai waya da shi yanzun nan sai farin ciki take tana saka masa albarka. Ni nama rasa wanda zan tunkara da wannan abun al’ajab shine fa na kiraki naji ko wani abu ya faru anan”.
“Nan dai babu abinda ya faru, sai dai yana ɗakinsa. Amma dai wannan lamari da ɗaure kai. Basma anya Adda Asmah bata fara cin galaba akan Maah ba?”.
“Aunty Kamar ya?”.
Saurin dafe kai Bilkisu tai jin zata saki layi. Ta manta ita kaɗai taji abinda Adda Asmah ta taɓa faɗa akan Mahaifiyarsu kwanakin baya sanda ake tsaka da rikicin auren Yayansu da Raudha. Kuma bata taɓa nuna ta saniba ko taɓa faɗama wani. Sai dai tana kallonta da abun kuma tun daga ranar taji bata sonta duk da yayar Maah ce. Hasalima tafi shiri da ita fiye da kowa a ƴaƴan gidansu, dan ita takan iya zuwa ta kwana gidansu Aynah ɗin ma ba kamar su Basma ba.