BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

★★
“Ya ALLAHU miya faru? Suma yay?”.
Cewar Anne dake shigowa falon Bappi idonta akan Ramadhan da suka shimfiɗar a ƙasan carpet Pa na kokarin shafa masa ruwa. Kai kawai Bappi dake zaune kan Ramadhan ɗin a cinyarsa ya ɗaga mata. Wani nannauyan numfashi Ramadhan ya ja a fisge sai kuma ya sake riƙe kansa zai fasa ƙara Bappi ya rufe masa bakki.
“Tabbas akwai matsala, inaga akwai lamarin azzaluman aljanun sihiri tare da shi”. Cewar Yafendo tana kuka. Da sauri Anne ta fita a ɗakin tana faɗin bara ta ɗakko alkur’ani. Bappi na kiranta tazo ta ɗakko na ɗakinsa bama taji ba harta fice. Zaune ta iske Raudha na karatun alkur’ani da alama sallar shafa’i da wutiri ta idar. Ai tama manta da batun bedrest da Raudha keyi ta kamo hanuntan.
“Ameenatu taso ga inda ake buƙatar karatun nan naki can.”
Hankali tashe Raudha ta dakata, ganin Anne a firgice yasa batabi ba’asi ba ta mike kawi ta bita. Sanye take cikin dogon hijjab fari har ƙasa. Dan haka baka iya ganin komai nata sai fuska da tafukan hannu………✍
Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹????♀️⛹????♀️????
ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA????????????????????
1~ KUFAN WUTA????
Safiyya Huguma
1~ BAQAR INUWA????
Billyn Abdul
1~ RAYUWAR MACE????
Hafsat Rano
1~ MASARAUTA????
Miss Xoxo
1~ NOOR ALBI❤????
Mamuhgee
Guda 1????300
Guda 2????400
Guda 3????500
Guda 4????700
Guda 5????1k
ZAKU BIYA KUDINKU ANAN????????
Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank
Number shaidar biya????????
09032345899
KATIN MTN????????
09166221261
JAMA’AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan????????
Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F
ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA????????
+227 95 16 61 77
TEAM ZAFAFABIYAR????????????????
BAƘAR INUWA…????????
Da ɗumi-ɗuminsa????????????????????????????????
Please
Follow me
Share
Comments akan abinda ya shige maka duhu.
_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar????????????????????????_
YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za’a cike Form ɗin kamar haka: –
Enter your name: (Cikakken sunanki)
Enter your mail: (Email ɗinki)
Enter an username (Sunanki)
Enter your password: ( misali 12341234)
Confirm password: (misali 12341234)
Sai a taɓa Sign Up shikenan an buɗe account a ArewaBooks????????????.
Continue with Google – Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za’a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
Register – Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.
AREWABOOKS LINK kai tsaye
Masu iPhone
Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App… Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine.
MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER
+234 903 177 4742
Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan????????????????????????.
ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????
Typing????
Episode. 61-62
………..Wani irin tsargawa kanta yay ganin Ramadhan shimfiɗe a ƙasa Bappi ya toshe masa baki, ga Pa a kansa yana karatun suratul baqara. Tuni jikinta ya fara rawa. Ta matsa da sasaarfa takai duke gabansa cikin rufewar idon manta waɗanda suke a falon. “Ya ALLAHU na shiga uku ni Raudha Ya Ramadhan mike faruwa da kai haka?”.
“Kinga Ameenatu yi hakuri baya cikin hayyacinsa yi masa karatun kawai”.
Ai Bappi baima kai karshe ba ta fara karatun itama cikin suratul baqaran. Wata muguwar zabura ya kara yunkurowa zaiyi saboda masu karatun sun zama biyu, ga zazzaƙar murya da ALLAH ya azurta Raudha da ita inhar tana karatu komai taurin zuciyarka saika nutsu a saurare. Tun sunayi yana fisge-fisge har ya fara lafawa a hankali. “Idan ma mu an koremu ai akwai wanda suke tare da shi tun yana yaro”.
Bakin Ramadhan ɗin ya faɗa a kausashe, amma a tabbaci bashi bane sai kuma ya fara sakin tari mai ƙarfi. Raudha da Pa basu dakataba suka cigaba da karatunsu sudai. Yayinda Anne ke duke gabansa tana rike da kansa ita da Bappi. Tsahon mintuna talatin suka sake kwashewa suna karatun kafin jikinsa yayi laƙwas. Duk da hakan Raudha bata dakata ba har sai da takai karshen suratul baqara lokacin agogo ke nuna karfe ɗaya da wasu mintuna na dare.
Ta matuƙar birgesu, sun sake jin kaunarta mai tsanani da taya gudanjininsu murnar samunta matsayin mata uwar ƴaƴansa. Bayan ta rufe da addu’a suka shiga sanya mata albarka. Ita dai kanta a ƙasa tana sharar hawaye. babban burinta tasan miya kawo mijinta gidan a wannan halin? Yama akai yazo? Miya faru da shi?. Waɗan nan sune jerarrun tambayoyin dake mata yawo bisa kai. Sai dai ta kasa furtasu ga kowa.
Anne da tasan lokacin barcin Raudhan ya gota cikin sanyin murya tace, “Ameenatu kije ki kwanta kinga kema fama kike da jikinki. Tunda Alhmdllhi da alama komai ya dai-daita barci ne ya ɗaukesa. Kamar Raudha zatace a’a sai kuma tay yunkurin mikewa domin bin umarnin Anne. Caraf taji an ruƙo mata hannu, bama ita kaɗai ba kowa a ɗakin sai da ya kalli hanun Ramadhan ɗin, kafin ya firta. “Ameenatu ruwa! Bani ruwa na sha inajin ƙishi”.
A hankali yake maganar amma hakan bai hanasu jinsa ba. Raudha duk kunya ta isheta. Amma saita daure ta dauka goran ruwan dake kusa da Anne, a sanyaye tace, “Ga ruwan to buɗe idonka”.
Bakinsa kawai ya buɗe mata yana ɗan girgiza kansa, kamar zata sake magana sai kuma Bappi ya dakatar da ita ta hanyar ɗago kan Ramadhan ɗin yanda zata iya zuba masa ruwan batare da ya cutar da shi ba. Duk da kunyar da takeji haka ta daure ta ɗora masa gorar a baki. Sai ko gashi yana zuƙarsa da yawa harya shanye. A hankali ta janye goran shi kuma ya ɗan buɗe idanunsa yana kallonta. “ALLAH yayi miki albarka”. Ya faɗa a hankali tare da maida idanunsa ya lumshe.
Kusan atare duk suka amsa da amin tare da sauke ajiyar zuciya. banda Raudha datai kasa da kanta ta amsa a kan laɓɓa. Bappi ne ya basu umarnin zuwa su kwanta, shi kuma zai kwana da Ramadhan ɗin sugani ko zuwa asuba zai dawo hayyacinsa su samu ya koma can government house kafin a farga. Dan sun tabbatar fitar ɓadda kamar daya sabayice yayo yau ɗin ma.
Badan Raudha taso ba ta mike. Koda suka isa ɗaki Anne wanka ta sakatayi, ta bata tea tasha kamar yanda ta saba turketa a duk dare kafin ta sakata kwanciyar dole. Sai dai ta lumshe idanune kawai badan barcin ba. Amma ita kanta tasan idan tace zatai barci a irin wannan halin yaudarar kanta zatai kawai…
A ɓangaren su gimbiya Su’adah kam kowa tunda baiga Ramadhan ba sai hankalinsa ya karkata akan Addah Asma’a da suka samu a kasa wanwar. Ruwa aka bata tasha, aka kuma dagata zuwa kujera sannan suka shiga mata sannu. Bayan numfashinta yaɗan daidaita Gambiya Su’adah ta sallemsu su duka falon ya rage daga ita sai Adda Asmah da Aynah.
“Adda inaga kuje gida zanzo da safe na sameku, dan zamanku yanzu anan akwai matsala zai iya fargar da jama’ar gidan wani abu. Su kuma ku barni dasu game da Ramadhan zanma tufƙar hanci”.
Addah Asmah da ba fahimtar komai takeba a yanzu gudun kar gimbiya Su’adah ta ɗagota ta jinjina mata kai ko maganin da suka kawo ɗin bata samu bata ba suka fice cikin taraddadin da ƙaulani. Numfashi gimbiya Su’adah saukewa, kafin ta nufi sashen su Anne. Sai dai tana tu karowa taji sautin karatun Raudha da Pa. Wani irin kunci da duhu zuciyarta ta sake shiga najin tsantsar tsanar Raudha da batasan yaya akai tazo gidanba ya riketa. Tunanin ko dama tare da Ramadhan sukazo ya sata juyawa ta fasa shiga baki ɗaya ta koma sashenta tana haɗiyar zuciyarta data cika kirjinta fam kamar zata fashe.