BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

★★★_★★_★
Da asubar fari Bappi ya fita raka Ramadhan government house, kamar yanda ya fita ta barauniyar hanya yanzun ma tanan yabi da taimakon odilan nashi da shi kaɗai dama yasan da fitar. Tunda yaga bai dawo akan lokaci ba hankalinsa yake a tashe. Shi kansa yasan irin waɗannan fitar da shugaban ƙasar keyi akwai haɗari a cikinta. Sai dai shi ko’a jikinsa. Ko’an nuna masa illar fitar ɓadda kamar baya nuna damuwa ko hango wata matsala. Amma har cikin rai odilan ɗin nasa na tsoron randa wani zai farga a cikin gidan ko waje.
A taura house kam koda aka wayi gari babu wanda ya tada zancen. Musamman daga sashen Anne. Ita kanta gimbiya Su’adah tana son ma Pa magana tanajin tsoron a yanda ya tashi yau fuska kamar hadarin gabas. Amma har cikin rai tana buƙatar jin halin da yaronta ke ciki. Ta kira wayarsa amma ba’a ɗaga ba, ta rasa inda zata tsoma ranta ta huta har baƙi dai suka fara isowa irin su Safina da tawagar ƴaƴanta. Sai daga masarautar Bina kuma.
Zuwa Azhar gidan ya fara ɗaukar baƙi sosai. Hakan ne ya tilasta Gimbiya Su’adah fasa fita gidan Addah Asmah dan tun jiya da suka bar gidan bataji daga garesu ba. Ta kira duk wayoyinsu a kashe. Ta aika Muneera ta dawo ta sanar mata Aynah da Addah basa gida wai tun safe suka fita baƙi ma daketa isowa babu wanda ya samesu a gidan sai ma’aitan gidan keta saukesu. Wannan zance ya sake tada hankalin gimbiya Su’adah matuƙa dan haka ta kira fulani da suke shirin tahowa da yamma ta sanar mata. Duk da fulani tasan komai sai ta ɓoye mata akan ta kwantar da hankalinta zata bincika. Amma tasan Addah Asmahn bazataje wani waje ba daban. A sanyaye tace to.
Fulani ta sauke wayar tana taɓe baki. Dan yanzu sun ƙudiri aniyar daina faɗa gimbiya Su’adah komai akan shirinsu. A ganinsu sakacintane ya lalata komai a daren jiya kokuma akwai abinda take son gujemawa. Itako fulani burinta da alwashinta sai ta nunama Anne ba itace kaɗai keda iko da Ramadhan ba, yayinda Addah Asmah ke nuna itama shine burin nata. Sai dai acan kasan rai ba haka bane. Baƙar hassadar ƴar uwartace kawai ke cinta akan ta fita komai na rayuwa. A ganinta mallakar Ramadhan matsayin mijin ƴarta, zaisa abinda Gimbiya Su’adah ke takama da tinƙaho da shi ya dawo tafin hanunta ƙarƙashin ikonta.
Faruwar komai a jiya yasa Aynah kwana kuka akan bazata iya haƙuri da Ramadhan ba a yanzu. Ita duk ma yanda za’ai ayi ƙoƙarin gyara matsalar nan da suka tabbatar komai ya watse. Wannan shine dalilinsu na tafiya gidan boka bayan tun dare sun kirashi yanata faɗa akan abinda tunkan su sanar masa yace musu ya sani tunda aljanin daya turama Ramadhan yaci ubansa hanun Raudha da Pa da ayar ALLAH. Tun tafiyar da sukai da asubahin nan suna can har yanzu anata sake tsumo Aynah da shaiɗanci kala-kala akan Ramadhan kawai….
To bara muga wazaiyi winning anan kuma????????????.
_________________
Ƙarfe biyar na yamma dai-dai tawagar shugaban ƙasa Ramadhan ta iso Taura house bisa rakkiyar jami’an tsaro da wasu na jikinsa. Kamar wancan hutun tako ina anguwar ta zama ƙarƙashin mulkin mallakar jami’an tsaro ne. Sauƙin ma dama can anguwar manyace bawai hayaniya ko yawan shigi da fici ake samu ba. Sai dai abin ya shafi masu tururuwar zuwa biki. Dan duk waɗanda suka iso yau dasunci karo da jami’an tsaron nan sai tsoro ya kamasu duk da sunsan yanzu Taura house yana da wani sabon girma bayan wanda kowa yasan gidan da shi.
Babu wanda yaga Ramadhan, domin motar da yake ciki har jikin ƙofar falon Bappi ta baya aka kaita, yana fita kuma ya shige ciki abinsa.
Raudha na bedroom ɗin Anne kwance ta gama ƙwallar shan kunu da Annen ta tsareta tayi Bilkisu ta shigo ɗakin da sallama. Wayar ta dake hanunta tana game ta ajiye, dan dama game ɗin kawai takeyi amma hankalinta naga mijinta da tunanin miyake ciki yanzun? Yana ina? Jikinsa da sauƙi ko babu?.
“Sai a daina mana shagwaɓa ga boss nan ya iso”. Bilkisu daba sanin abinda ya faru da Ramadhan ɗin tai jiya ba ta faɗa tana dariya bayan takai zaune kusa da Raudha. Murmushi kawai Raudha tayi da faɗin, “Kai aunty ni shagwaɓar mi nayi?”.
“Ai ba abun jayayya bane bara na lissafa miki yanzu kuwa ɗaya bayan ɗaya ta Brothe……”
Ta kasa karasawa saboda wanda ya shigo ɗakin. Da farko tsoro taji sosai ita kanta Bilkisun, sai dai yanda taga yanayinsa kamar a sanyaye ya sata ɗan sassautawa ta gaisheshi zata mike. Sai dai Raudha tai saurin riƙo hanunta idanunta na cika da ƙwalla. Sosai yanzu tsoronsa takeji, tsoro mai tsanani dan ita kaɗai tasan azabar da taci a hanunsa har sau biyu da bazata taɓa iya mantawa ba.
Raunanannun idanunsa ya sauke akan hannayen da Raudhan ta sarƙe. Sai yaji wani irin tausayinta mai tsanani yana dirar masa daga tsakkiyar kai har tafin kafa. Da ido yayma Bilkisu alamar ta fita. Dan haka tai saurin son zame hanunta cikin dabara tana faɗin, “Aunty Raudha bara na dawo tanan sai Yaya ya zauna nan”.
Sam Raudha bata yarda ba, saita ƙara ƙwaɓe fuska zatai kuka. Bilkisu da ita kanta tausayinta takeji tunda batasan ko yayan nasu bai dawo cikin hankalinsaba har yanzu ta zame hanunta ta gudu. Sosai jikin Raudha ya fara rawa ganin ya maida ƙofar ya kulle harda key. Babu shiri ta miƙe a kan gadon tana ƙoƙarin sakkowa. Sosai tayi ƙiba, tako’ina komai yayi zam, damma doguwar rigar jallabiyace a jikin nata baƙa. A hankali ya lumshe idanunsa tare da harɗe hannayensa duka a ƙirjinsa, sai kuma ya sake buɗesu ya zuba mata. Yanda take rawar jiki yasa ko’ina nata ke motsawa, ga rigar mai santsi ce, sai hakan ya ƙara taimakawa wajen motsawar jikin nata.
Murmushin takaici da tausayin kansu ya saki. Baiga laifinta ba, dan yasan dolene taji irin wannan tsoron nasa. Ya ɗan furzar na numfashi tare da warware hannayensa daga ƙirji ya fara takowa gareta cike da nutsuwarsa da kasalar yanayin rashin jin daɗi da yake a ciki……..✍
BAƘAR INUWA…????????
Da ɗumi-ɗuminsa????????????????????????????????
Please
Follow me
Share
Comments akan abinda ya shige maka duhu.
_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar????????????????????????_
YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za’a cike Form ɗin kamar haka: –
Enter your name: (Cikakken sunanki)
Enter your mail: (Email ɗinki)
Enter an username (Sunanki)
Enter your password: ( misali 12341234)
Confirm password: (misali 12341234)
Sai a taɓa Sign Up shikenan an buɗe account a ArewaBooks????????????.
Continue with Google – Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za’a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
Register – Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.
AREWABOOKS LINK kai tsaye
Masu iPhone
Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App… Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine.