BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

     Bayan kamar mintuna goma sha biyar Ramadhan ya fito, a lokacin sun bar dining sun koma falo.
      “Yaya jikin nata?”.
Bappi ya tambaya cike da kulawa. Cikin damuwa Ramadhan daya koma duk wani kalar tausayi yace, “Bappi na barota kwance zan sama mata wani abincin a kuma kira Momyn Jabeer”.
          “No kiran Mommyn Jabeer ba shine mafitaba ai. Da alama kamshin naman kan canne bataso. Taci abinci saita kwanta ta huta ALLAH ya raba lafiya”.
         Wani irin yarrr yaji har saman kansa. Cikin rawar harshe yace, “Anne ban gane ba?”.
     Hannu Bappi ya mika masa da faɗin, “Ajiye goro na ganar da kai”.
    Ganin Bappi a serious sosai Ramadhan yay ƴar dariya yana shafa aljihu. Sai dai babu komai a ciki, hatta wayoyinsa na ɗaki. “Bappi na maka alƙawarin baka koma mi kakeso faɗi dan ALLAH”.
     “Tabb ai an daina aikin banza a NAYA kai dai ajiye kasha labaru”.
         Rasa mima zaiyi yay, sai kawai ya kwanto agogon hanunsa ya ɗora a hanun Bappin. Bappi ya ɗan juya agogon, sai kuma ya taɓe baki. “Ba laifi mai nauyine ai. Bilkisu bashi yasha”.
     Bilkisu dake dariya cike da ɗoki ta nufi Yayan nata tayi ɗan hugging nashi, sai kuma ta sakeshi. “Yaya na kusa zama Mummyne fa, Aunty nada cikin wata biyu da kwanaki….”
       “What?!!!”.
Ai kafinma ta ƙarasa bayani ya juya da sauri ya bar wajen zuwa sashensa. “Na yafe miki sauran labarin”. Ya faɗa yana ɗago hannu sanda yake gab da shiga.
        Mi su Anne zasuyi inba dariya ba. Pa dake tsaye tun ɗazu batare da sun sani ba yay murmushi kawai yana girgiza kansa. Ɗansa kenan abin alfaharinsa. Murɗaɗɗen mai wahalar fahimta ga wanda ke nesa da shi. Da yawan mutane akace musu Ramadhan mai sauƙin kaine a cikin gida zasu karyata. Domin shi mutumne mai yanyin mutanen da ake kira da girman kai kai tsaye. Dan kuwa tabbas magana ma sai yaso da wanda yay niyya yakeyinta. Dariya ko mutane da yawa kance basu taɓa gani daga garesa ba. Dan akan jima baiyi hakan ba sai a inda yaso. Sai dai ga wanda yaso kuma ya aminta shi mai sauƙin kaine da iya mu’amula matuƙa.

        Cikin ɗan barcin daya fara figarta kawai taji an rungumeta. Tare da fara bata zafafan kiss’s tako ina da ina a jikinta.
        “Ya Ramadhan lafiya?”.
Raudha ta faɗa a kasalance dan da gaske barci ya fara ɗaukarta. Bai bata amsa ba. Sai rungumeta da yay tsam a jikinsa yana jero addu’ar nan ga wanda abin farin ciki ya sama.
       الْحَمْدُ للهِ الَّذِي بِنِعْمَتِهِ تَتِمُّ الصَّالِحَاتِ .
Alhamdu lillahil-lazee bini’imatihi tatimmus-salihat.
     Godiya ta tabbata ga ALLAH wanda saboda ni’imarsa ce kyawawan ayyuka suke cika.
اَلْحَمْدُ ِللهِ عَلَى كُلِّ حَالٍ.
Alhamdulillahi ala kulli halin
       Godiya ta tabbata ga ALLAH a cikin kowane hali.
        Rigar dake jikinta ya ɗaga nanma yana sumbatar cikinta. Kafin ya kwantar da kansa akai wasu hawaye na tuna Haseenah na sakko masa. Ashe bayan Haseenah yana da rabon sake haihuwar ƙanen a duniya. Ɗagowa yay ya sake sumbatar cikin, sai kuma ya fara karanto addu’ar nemawa ƴaƴa tsari (iyaye dan ALLAH a dingayi, kai ko yaron cikine dake karanta ki shafe cikinki kafin ya fito ki ɗora dayi masa a zahiri????????. Domin kuwa MANZON ALLAH tsira da amincin ALLAH su tabbata a gare shi, ya kasance yana nema wa Hassan da Husain tsari da wannan addu’ar: ).
             أُعِيذُكُمَا بِكَلِمَاتِ اللهِ التَّامَّة، مِنْ كُلِّ شَيْطَانٍ وَهَامَّةٍ، وَمِنْ كُلِّ عَيْنٍ لاَمَّةٍ.
O’eezukuma bikalimatil-lahit-tammah, min kulli shaytanin wahammah, wamin kulli ‘aynin lammah.
       Ina neman muku tsari da kalmomin ALLAH cikakku daga dukkan shaiɗan da wata dabba mai dafi, da kuma dukkan wani mai kambun baka, mai cutarwa.
        Raudha dake murmushi takai hannu ta shafa kansa. “Irin wannan security ba ɗaga ƙafa haka?”.
      Tasowa yay gareta shima fuskar tasa da murmushi, ya kwanta kusa da ita tare da tokare kansa da hanunsa ya lakace mata hanci. “Uhmm barni gara na tofe abina tun yanzu kodan masu ƙarancin tsoron ALLAH. Yanzu nan Baby Luv kinsan da wannan abin farin cikin tun ɗazu kikaƙi sanarmin? Anya kuwa kina sona?”.
     Dariya tayi tana mai saka tafukan hanunta ta rufe fuska. “Kai Ya Ramadhan kawai kuma saina kama faɗama inada cikin ɗan fari dan banda kunya”.
        “Lallaima yarinyar nan”.
Ya faɗa shima yana dariya da son zame hanunta. Ƙin yarda tayi, sai ma juyowa datai da sauri ta sinne kanta a ƙirjinsa. Idanu ya lumshe a hankali tare da rungumota ya kanƙame ta shima. ji yake kamar ya haɗiyeta kawai ya huta. “I love you sweetheart”.
        “I love you too Noorullah”.
“Nice name dear I love more. Na huta an daina kaƙabamin Yaya babu dangin gabas babu na yamma. Dolene yau nayi celebrations biyu kenan”.
        Siririyar dariya ta saki tana mai ɗagowa ta sumbaci lips nasa ta sake maida kanta ta kudindine a jikinsa.
      “Hummm wlhy yarinya ki bani kwana uku kacal saina maidaki mara kunya ta bugawa a jaridar duniya”. Yay maganar yana mai rungumeta sosai a jikinsa murmushi yaki barin fuskarsa.
        Babu wanda ya karajin ɗuriyar Ramadhan da Raudha a gidan, kuma babu wanda ya nemesu. Garama ya kira Bilkisu daga baya ta kawoma Raudha sabon abinci taci ya busar mata da gashinta daga nan sukai kwanciyarsu…………✍

Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹????‍♀️⛹????‍♀️????

ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA????????????????????

1~ KUFAN WUTA????
Safiyya Huguma

1~ BAQAR INUWA????
Billyn Abdul

1~ RAYUWAR MACE????
Hafsat Rano

1~ MASARAUTA????
Miss Xoxo

1~ NOOR ALBI❤‍????
Mamuhgee

Guda 1????300
Guda 2????400
Guda 3????500
Guda 4????700
Guda 5????1k

ZAKU BIYA KUDINKU ANAN????????

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya????????

09032345899

KATIN MTN????????

09166221261


JAMA’AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan????????

Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F

ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA????????

+227 95 16 61 77

TEAM ZAFAFABIYAR????????????????


BAƘAR INUWA…????????

Da ɗumi-ɗuminsa????????????????????????????????

Please
Follow me
Share
Comments akan abinda ya shige maka duhu.

     _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar????????????????????????_

YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za’a cike Form ɗin kamar haka: –

Enter your name: (Cikakken sunanki)

Enter your mail: (Email ɗinki)

Enter an username (Sunanki)

Enter your password: ( misali 12341234)

Confirm password: (misali 12341234)

Sai a taɓa Sign Up shikenan an buɗe account a ArewaBooks????????????.

Continue with Google – Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za’a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button