BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

TAURA HOUSE
Kowa ya hallara su kaɗai ake jira, mai-martaba da ransa ya gama ɓaci yana ƙoƙarin cewa a kirasu sai ga kiran daddyn Aynah ya shigo masa. Cikin tashin hankali ya shiga ambaton kalmar innalillahi…. Har ƙarshe, kafin ya ajiye wayar ya sanarma ƴan falon da duk hankalinsu ke kansa iya abinda Daddyn Aynah ya sanar masa. Zaram Ramadhan ya miƙe amma sai Bappi ya dakatar da shi.
“Ina zaka kuma?”.
“Bappi can gidan mana, kanajifa faɗa mizai haɗa Maah da Mom faɗa a duniyar nan?”.
“Koma miye ai zamu sani yanzu, ko kana mantawa da matsayinka a yanzune wai. Koma ka zauna Basheer yaje ya taho da su”.
Babu yanda ya iya ya koma ya zauna kamar zaiyi kuka. Zuciyarsa sai kaikawo take da tunanin mike faruwa? Miya faruwa? Mi akayi?. Hakama sauran kowa tunaninsa kenan sai dai babu mai bada gamsashiyyar amsa akai zaman jiran isowarsu.
★Kusan awa guda suna zaman jira dan sai da Pa yay jan ido suka yadda suka taho dalilin ita gimbiya Su’adah na tsoron nata mijin, itako Adda Asmah ta raina nata. Wujiga-wijiga suka shigo musamman gimbiya Su’adah da sai da Safina ta bata taimakon gaggawa acan amma da yanzu labarin ba wannan ake ba kuma. Kowa hankalinsa ya tashi da yanayin nasu, musamman ma Ramadhan da cikin rawar jiki yaje ya taya Safina riƙo Maah dake tafiya kamar zata zube ƙasa sai hakki take sama-sama. Shidai Bappi uffan baiceba, binsu kawai yake da kallo hakama mai-martaba. Pa kuwa yanayinsa na nuna ko’a jikinsa dan dama irin wannan ranar yake addu’ar tazo duk da bai san mike faruwa ba shima har yanzun.
“Inaga muyi abinda ya taramu kamar zaifi”.
Cewar Pa da alamun ɗaci a muryarsa. Bappi zaiyi magana Mai-martaba ya katsesa.
“Gaskiya Basheer ya faɗa dan nima sonake na wuce akan lokaci”.
Bappi ya haɗiye abinda yay niyyar faɗa kawai yana girgiza kansa. Daga haka aka buɗe taro da addu’a sannan aka fara abinda ya tara ɗin game da sauya maganar auren Ramadhan da Aynah.
Bayan dawowar Ramadhan hayyacinsa, adare ranar Bappi ya sanar masa duk abinda ake ciki, amma sai ya dage akan shi bai taɓa jin son wata Ayna’u ba. Bakuma zai fara a yanzu ba bayan so na ƴan uwantaka dake tsakaninsu. Ya kuma tabbatar masa komi za’ai shi bazai aureta ba matarsa ta ishesa. Babu irin lallashin da Bappi bai masaba a wannan dare amma yace shifa yana akan bakansa.
Washe gari ma daya dawo gidan kafin yaje ga Raudha maganar da suka fara tattaunawa da Pa da Bappi da Anne harma da su Yafendo da Mai-martaba a waya kenan amma Ramadhan yace yana kan bakansa. Baice zai auri Ayna’u ba kuma ayanzu bazai amsa ba. Dagiyarsa ya sake tabbatar musu akwai sihiri tattare da shi sanda ya dinga musu hauka akan auren Ayna’u garda ɓatawa da su Anne. Wannan dalilin ya sakasu sallamarsa suka tattauna abinda ya dace a tsakaninsu. Mahaifin Aynah shine ya kawo shawarar a rufe komai iya su ranar ɗaurin aure yanada wanda zai aurama Aynah dan a raba gardama komai ya zama ƙarshe basai anta jan zancen ba. Wannan shawara tama kowa, dan haka suka rufe komai hatta Ramadhan baisan da haka ba sai da aka ɗaura aure da wani daban ba shi ɗin ba.
“ALLAH na gode maka da hakanma ta kasance, Ramadhan ka yafemin, duk halin daka shiga akan Ayna’u hardani a ciki, daban basu goyon bayaba da ba’a nema sabautamin rayuwarka har gashi yau ana iƙirarin kashemin kai ba…”
Gimbiya Su’adah ta faɗa cikin kuka hanunta riƙe dana Ramadhan. Tsitt falon yay cikin rashin fahimtar kalaman nata……….✍
Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹????♀️⛹????♀️????
ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA????????????????????
1~ KUFAN WUTA????
Safiyya Huguma
1~ BAQAR INUWA????
Billyn Abdul
1~ RAYUWAR MACE????
Hafsat Rano
1~ MASARAUTA????
Miss Xoxo
1~ NOOR ALBI❤????
Mamuhgee
Guda 1????300
Guda 2????400
Guda 3????500
Guda 4????700
Guda 5????1k
ZAKU BIYA KUDINKU ANAN????????
Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank
Number shaidar biya????????
09032345899
KATIN MTN????????
09166221261
JAMA’AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan??????
Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F
ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA????????
+227 95 16 61 77
TEAM ZAFAFABIYAR????????????????
BAƘAR INUWA…????????
Da ɗumi-ɗuminsa????????????????????????????????
Please
Follow me
Share
Comments akan abinda ya shige maka duhu.
_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar????????????????????????_
YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za’a cike Form ɗin kamar haka: –
Enter your name: (Cikakken sunanki)
Enter your mail: (Email ɗinki)
Enter an username (Sunanki)
Enter your password: ( misali 12341234)
Confirm password: (misali 12341234)
Sai a taɓa Sign Up shikenan an buɗe account a ArewaBooks????????????.
Continue with Google – Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za’a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
Register – Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.
AREWABOOKS LINK kai tsaye
Masu iPhone
Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App… Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine.
MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER
+234 903 177 4742
Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan????????????????????????.
ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????
Typing????
Episode 71
………“K Su’adah wace maganar banza ce wannan kike haka?”.
Fulani ta katseta a harzuƙe.
“Ammy karki wani rufe gaskiya da son zuciya. Dole ne sirrin ɓoye ya fito fili, ban taɓa zaton Asmah zata zamemin BAƘAR INUWA ba sai yau. Ashe gara ranar da nake gudu da ita. Asmah bazan taɓa yafe miki ba, kuma insha ALLAH haka zaki ƙare rayuwarki a rashin nasarar da kike gani kina ciki……”
A harzuƙe Adda Asmah ta yunƙuro zatai magana Fulani ta ƙatseta, hakan yasa mai-martaba bama gimbiya Su’adah damar faɗar duk abinda ke faruwa. Bako ta ɓoye ba, dan tun daga lokacin da riƙon Ramadhan ya koma hanun su Anne hanyoyin da Adda Asmah ta dinga sakata ita da Fulani har zuwa aurensa na farko, da kuma aurensa da Raudha zuwa son haɗasa da Aynah a yanzu da abinda suka jiyo ita da Safina yanzun. Bugu da ƙari dan ma kar Addah Asmah ta musa haka Safina ta ajiye wayarta da tayo recording duk maganganinsu kowa yaji.
Sallallami kowa ya shigayi a falon, yayinda Adda Asmah ta haukace musu akan ita ƙarya ake mata. Saharri ne kawai saboda gimbiya Su’adah na borin kunya ta hana ɗanta auren ƴarta. Idanma kuwa tayi wani abun ai tare sukayisa. Wannan magana ta Adda Asmah ta sake tada ƙura, dan ko ba kunya gimbiya Su’adah ta daddage ta yarfama Adda Asmah mari,
“Su’adah ni kika mara?!”.
“An mareki Asmah, kaɗanma kika gani wlhy, na tsaneki, na tsani ganinki, nayi dana sanin saninki matsayin ƴar uwata ciki guda. Kuma insha ALLAH Ramadhan yafi ƙarfinki har abada yafi kuma ƙarfin ƴarki, sai dai ki mutu da baƙin cikina dana zuri’ata. Munafuka kita zugani akan su Anne da suka riƙemin yaro tsakani da ALLAH kina cemin macutane ashe kece azzaluma mai cin amanar zuminci. Da iznin ALLAH ƙarshenki bazai ƙyauba…..”
“K ce ƙarshenki baizai ƙyauba su’adah”. Adda Asmah ta faɗa tana kaiwa Gimbiya Su’adah mari, amma saita riƙe hanun ta murɗesa dan ko dai gimbiya Su’ada tafita ƙiba dama zuciya.
Idanu Ramadhan ya sake rumtsewa kansa na juya masa. Yayinda su Bappi keta faman musu magana amma sunƙi sauraren kowa. Dan wata irin hankaɗawa ma Gimbiya Su’adah taima Adda Asmah tai taga-taga zata daɗi Aynah dake kuka ta riƙota.
Nuna gimbiya Su’adah tai a kausashe. “Su’adah bakici bulus ba wlhy, ina matsayin yayarki kikaimin wannan abubuwan saboda kina auren mai kuɗi. Ni Asma’u nayi alƙawarin saina sabautar da rayuwarki data ahalinki baki ɗaya, dan wlhy sai kinyi dana sanin sanina. Sai kinsan na haifu cikin uwata da ubana, sai kin gwammaci daban kasance jininki ba!!”.
Tana gama faɗa ta juya zata fita cike da borin kunya. Ana dakatar da ita bata saurari kowa ba taja hanun Aynah suka bar falon tana mai jaddadama gimbiya Su’adah bazata yarda da ƙazafin da sukai mata ita da Safina ba da mari ta jiraci sakamako..
Wannan Al’amari ya firgita kowa ya kuma bama kowa mamaki. Mai-martaba da tun ƙuruciyar yaran nasa ya fahimci halin kowa ya share ƙwallar da suka cika masa idanu.
“Ni nasan wannan ranar zatazo. Bammayi tunanin sauƙinta zai kasance hakaba. Tabbas Su’adah nada halayen banza da takejin zata iya taka kowa da komai idan taso. Girman kai, ɗaukar kowa ba kowaba duk halayyartace. Sai dai abinda mutane da yawa basa saurin ganewa daga gareta shine, abin kowa bai dameta ba. Su’adah bazaka taɓa jinta ta zauna surutu akan damuwa da cigaban wani ba, sannan dan taga wani da abu bazakaga ɓacin rai daga gareta ba balle damuwar kishinsa. Itako Asma’u da kuke gani, tanada sauƙin kai da son mutane, sai dai tanada nunkufurci da hassadar bata yarda kowa ya fita ba. Waɗan nan halayen nasu sune suka banbantasu, dan ita Hassada na cinye ayyukan bayi, tana maida mai son yin nasara bayan wanda yake gani bai kai ya fisa ba. Sai kaga mutum da halayen banza. Kai kullum cikin ibada da sauransu amma yanata samun nasariri kai sun gagara zuwa gareka karasa yaya haka? Nafi wane komai a rayuwa mizaisa ya dinga bani tazara? Amsar itace hassada. Hassada na ƙwace nasarori, ga wanda baida ita tana bashi nasarori koda bai kaika ba. Wasu suna tunanin Hassada itace kawai naga wane da abu banji daɗi ba. Hassada na zuwa kashi-kashi a cikin ayyuka.
Kaji kai kaɗai kake son kai nasara a rayuwa. Kaji kanajin zafin wanda kafi da komai na rayuwa ya samu wani abu kai baka samu ba. Ka dinga damuwa da yawan maganar cigaban wane. Mutum ya gina ƙyaƙyƙyawan abu ka ruguza masa. Misali mutanen da ke fidda mana littafi ko zuwa su saya dan su yaɗa hassada ce. Shiyyasa zasuga kullum suna wahalar banza da tunanin dakushemu mukuma munata nasara a rayuwarmu domin basu isa hanamu samun abinda ALLAH ya rubuto a ƙaddararmu ba.
Hassada na shigowa cikin ayyukan mutane daban-daban ƙarama ko babba, ka sani ko baka sani ba. ALLAH ya rabamu da hassada. Ka tsarkake mana zukatanmu akoda yaushe. Ka wajabta mana tsoronka da soyayyar ANNABINMU (S.A.W).
Nasiha sosai mai-martaba yayi a wajen harda Bappi, daga karshe aka sake rufe taron da addu’a kowa ya kama gabansa..
A ranar aka miƙa amare ɗakunansu zukatan wasu duk babu daɗi. Musamman ma gimbiya Su’adah dake kwance babu lafiya, dan jininta ya hau matuƙa sai dai gyaran ALLAH. Amma Safina da Mardiyya na tsaye a kanta harma da Fulani.