BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

★Sai da Raudha ta warke sosai aka fara shirye-shiryen taron suna, amma kowa dai yasan sunan yaron Abdul-Hameed anma Bappi takwara. Ramadhan yaso ayi suna a Taura house Bappi ya hana yace ayi a government house kawai. Badan yaso ba dole hakan aka shirya. Taron sunane daya haɗa manyan mutanen ƙasar NAYA lungu da saƙo, inda amaryar jego da baby sukaci ƙyau har suka gaji. Shi kansa angon jegon yayi tsaf dashi kamar yana shirin yin sabon aure. Anci ansha an kumayi bishasha, inda yaro ya samu ƙyaututtuka masu ban mamaki wasuma dan riya sukai badan ALLAH ba. Dan kawai wane yayi kar ace su basuyiba.. Hatta M. Dauda ba’a barsa a bayaba ya haɗo kayansa na jego harda saitin robobin wanka da saƙe saƙin wanka na icce da ƙatuwar garwarsa ya kawo. Wannan abu yasa su Aunty Hannah takaici duk da ba’a wajen taron ya bayarba. Sai dai ita Raudha farin ciki tai ita da Ramadhan.
A zahiri taro ya tashi lafiya, sai dai a baɗini wasu sun iso wajen taron ransu da ƙulli. Ba su kowa bane sai su Alhaji Yaro glass da ko Aunty Hannah yanzu batajin sirrinsu. Bayan taro ya tashi lafiya wajen ƙarfe biyar na yamma a tsakanin government house zuwa Taura house aka buɗema motar Alhaji Hameed Taura wuta. Harbi ne irin na kwararrun maharba da ko a nesa suka harbo harsashi sai ya isa ga wanda suka hara ɗin. Sai dai in ALLAH ya kaddara da kwananka a gaba ka tsalle domin ikonsa.
Tabbas masu harin sunyi nasarar kaima motar hari sai dai basu taki sa’a ba, amma duk da haka ɓarnarsu ta shafi Taura house. Bayan kammala walima Alhaji Hameed ya shiga mota shi da Anne da su Yafendo domin komawa gida. Sai dai kiran Daddyn Aynah ya riskesu akan rikicewar jikin Adda Asmah gashi ya kira Gimbiya Su’adah bata amsa ba. Hakanne yasa suna ɗan gota government house Bappi da Anne suka fita amotar suka shiga wata harda Yafendo, Inna kuma dake fama da ƙafa tunkan su tafi wajen walimar dama danta dagene Bappi yace a wuce da ita gida. Kasancewar motar da su Muneera ke ciki suka amsa ɗin yasa Muneera dawowa wajen Inna ita kuma. Su Alhaji yaro glass basu san da wannan canji da aka samuba suka sanarma yaransu tahowar Bappi da sanar dasu motar da yake ciki su shirya.
Idan UBANGIJI bai ƙaddara mutuwarka ga makiyiba, komai wahalar mai wahala sai dai ya dawwama cikin wahalar farautar zafin rana data ɗacin zuciya babu nasara.
ALLAH ka shiga tsakaninmu da maƙiyanmu????????????.
Take a wajen ma ALLAH yay ma Inna Rasuwa, dan sai gawarta aka nufi asibiti da ita. Driver da Muneera ne kawai ke numfashi. Shima driver ko mintuna biyar basu cikaba ya rasu.
Karaɗewar labarin wannan hari da aka kaima Alhaji Hameed Taura cikin kanƙanin lokaci yasa ko zama basuyi a gidan Adda Asmah dake a mawuyacin hali itama suka taho. Hakama Raudha da Ramadhan da su Aunty Zuhrah duk sun rikice a government house. Dan kuwa babu abinda kake gani a yanzu akowane gidan tv sai harin da aka kaiwa Alhaji Hameed Taura. Amma abinda yaba mutane mamaki kamar yanda yan jarida ke faman shelantawa babu shi a motar duk da kuma daga government house kowa yaga motar ya shiga har shugaban ƙasa yay masa rakiya.
Zamu iya cewa a wannan dare gaba ɗaya NAYA a hargitse ta kasance. Dan ba’a samu damar bizne gawar Inna ba saboda jami’an tsaro sun rike. Kuka Raudha take tana sambatu da ambaton “Su din azzalumai ne. Dama sun ce sai sun kashemu, miyay musu, mi kai musu kaima mijina?. Na tsanesu, da ace sun samu nasara kan Bappi yau da kaina zan kashesu, amma ko yanzu karka ƙyalesu Ya Ramadhan. Na rokeka karka barsu suma su dukansu”.
Kalaman Raudha sun girgiza Ramadhan, dan haka ya tsareta ta sanar masa suwaye? Mita sani? Mi take boye musu. Shi tun sanda ta karema Bappi hari ya tabbatar tasan wani abu.
Cikin kuka ta shiga girgiza masa kanta. “Wlhy bansan komai a sannanba Ya Ramadhan, sannan bansan su wanene ba. Nayi hakane saboda shima ya taimaki wani tsohon daya fisa shekaru a filin idi. Amma badan na sanshi ba. Badan nasan komai daga garesaba. Sai dai zan faɗa maka abinda na sani nima, amma wlhy ka yarda dani, ban yarda da aurenka saboda su ba. Nayine kawai dan yima mahaifina biyayya da gujema mahaifiyata tsinuwa da Gwaggo tace zatai mata inhar ban yarda da aurenka ba………..”✍
Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹????♀️⛹????♀️????
ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA????????????????????
1~ KUFAN WUTA????
Safiyya Huguma
1~ BAQAR INUWA????
Billyn Abdul
1~ RAYUWAR MACE????
Hafsat Rano
1~ MASARAUTA????
Miss Xoxo
1~ NOOR ALBI❤????
Mamuhgee
Guda 1????300
Guda 2????400
Guda 3????500
Guda 4????700
Guda 5????1k
ZAKU BIYA KUDINKU ANAN????????
Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank
Number shaidar biya????????
09032345899
KATIN MTN????????
09166221261
JAMA’AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan????????
Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F
ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA????????
+227 95 16 61 77
TEAM ZAFAFABIYAR????????????????
BAƘAR INUWA…????????
Da ɗumi-ɗuminsa????????????????????????????????
Please
Follow me
Share
Comments akan abinda ya shige maka duhu.
_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar??????????????????????_
YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za’a cike Form ɗin kamar haka: –
Enter your name: (Cikakken sunanki)
Enter your mail: (Email ɗinki)
Enter an username (Sunanki)
Enter your password: ( misali 12341234)
Confirm password: (misali 12341234)
Sai a taɓa Sign Up shikenan an buɗe account a ArewaBooks????????????.
Continue with Google – Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za’a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
Register – Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.
AREWABOOKS LINK kai tsaye
Masu iPhone
Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App… Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine.
MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER
+234 903 177 4742
Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan????????????????????????.
ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????
Typing????
Episode 76
……….Tsaf ta zayyane masa komai data sani na firar su Aunty Hannah da taji, har zuwa aikama bappi takarda, da batun canja driks nashi da ake kawowa cikin gidan.
Ya daɗe da bincike akanta game da drinks saboda yanda kuɗi ke yawan fita a accaunt ɗinta, wanda duk watan duniya ake saka mata kason kudi na Taura family da ake bama kowa. Bai mata magana ba ya shiga bincike akan son sanin mi take da kuɗi, cikin ikon ALLAH kuwa yay azamar ganowa saboda companyn da take aikama kuɗin. Ta hanyarsu ya gane ana kawo drinks gidan, baiyi ƙasa a gwiwa ba yasa akai masa bincike akan wanda take canjawa da wanda take sakawar. An gano wanda take cirewar wasunsu akwai guba a jiki mai shiga jiki a hankali, wanda take canjawar kuma lafiya lau yake. Tun a sannan yasan Raudha tasan wani abu, shiyyasa koda suka samu rubutunta yazama irin na wanda aka aika musu wasiƙa bai tada hankalinsaba. Burinsa kawai yasan asalin tushe da mafari, yau kuma ta zayyane masa komai.
Kyawawar runguma ya bata yana mai sanya mata tarin albarka. Sai dai hakan bazai hanashi kafa kwamitin bincike ba domin tabbatarwa. Badan bai yarda da itaba, sai dan haka dokar shari’a take shaidarta bazata wadatar ita kadaiba dole sai da wasu shaidun musamman da su forma president suka zama manyan kusoshin ƙasar. Dama Dr Ingoze dake hanun security na gidan ta tabbatar musu ita ba laifinta bane sanyata akai ta hakala Raudha da jaririnta inba hakaba itama za’a halaka kaf family nata.