BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Sister’s duk wacce batayi anfani da sabulun mg’s ba inamai shaidamuku anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg’s sai sanbarka duk wani Mai tantama Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg’s domin yahadu bakarya zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark dama dukkan wani prblm yajaraba mg’s bi’iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using sabulu mg’s batare da kunbukaci wani Mai b????nd guess what????munyi upgrading kayanmu gbdy domin jindadinku????bama cika Baki kujaraba kugane ma idanku domin ance gani yakoriji Kuma siyan nagari maida kudi gida
???? Natural/organic

maiso yy mgn
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Instagram:glow_with_mgs
Facebook:mg’s skincare

Masu bukatar cream Shima munadashi harda ma complete set nagyaranjiki komai da komai
Akwai soap 3k
Student package 7k
Beauty kit 11k
Bridal kit 18k

Munatura Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free

Be part of the glow team????karkubari abaku lbr????
Typing????

Episode 78

……….“Tabbas dole Hannah ta mutu kafin a miƙata kotu”.
    Forma first lady ta faɗa tana duban su Alhaji Yaro glass dake tare da ita harma da god fathers nasu a yau. Mr MM da duk yake a firgice yay saurin faɗin, “Ina bayanki your excellency maa”.
       Gaba ɗaya falon dubansu suka maida ga Alhaji Yaro glass da tunda ya shigo baice komai ba, sai ma uban tagumi daya rafka. Numfashi yaja mai ƙarfi ganin sun dawo da kallonsu garesa alamar amsa suke nema. Yaɗan ɗage kafaɗa da yarfa hannuwa. “Ni a gareni babu matsala, da nasan ma wannan ranar zata zo da dakaina zan kashe Hannah tun kafin zuwanta. Dan tun randa case ɗin kuku ya shigo ya kamata a ɗauka wannan matakin, amma sai muka ɗauka hakan ba komai ba. Sai dai ku sani ba Hannah ce kawai zata mutu ba harda Kuku, dan kuwa Hannah da Bushira kuku ya sani ba Hannah kawai ba”.
        “Amma kasan shi ɗin ɗanane jinina ko?”.
    Cewar Forma first lady Bushira hamada a harzuƙe.
       “Nima ai Hannah matata ce, cewa a kasheta bashike nufin bana sonta ba. Sannan idan baku manta ba matar Ramadhan jinin Hannah ce, amma da akace zata iya mutuwa a cikin shirinmu batai jayyya ba, ashe kuwa indai nasara muke bukata dolene mu ɗanɗani ɗacin rashin jinanannmu koda kuwa ƴaƴan da muka haifane”.
     A take kowa ya goya bayan maganar Alhaji Yaro glass. Hakan yasa Hajiya Bushira hamada yin shiru. Oga kwata-kwata da baice komai ba sai da duk suka gama hayaniyarsu sannan yay gyaran murya. Dukansu hankali suka maida garesa.
      “Idan har ta kisan wane da wane ne zamubi ta hanyar rufe sirrikanmu mutane da yawa zasu mutu a wannan gaɓar. Dan haka ba shine mafita ba, babbar mafita a garemu yanzu harin maƙiyinmu kai tsaye. Ramadhan shine kawai zamu hara kai tsaye mu sami nasarar daƙile duk wata damuwarmu. Amma dan mun kashe su Hannah kamar mun kashe macijine bamu datse kansa ba, domin kuwa kisan nasu tamƙar buɗe hanyar da masu bincike suke nemace kai tsaye muka bayar.
     A take ɗakin taron ya ɗauka kananun hayaniya. Dan kuwa zantukan shugaba sun fargar dasu abinda basu hango a farko ba. Dan haka a daren yau basai gobe ba Ramadhan zai baƙunci lahira…..

       “Idan shi bai baƙunceta ba, ku zaku baƙunceta ai”.  Cewar Alhaji Balarabe Andu daya daɗe tare da su da fuska biyu. Alhaji Balarabe Andu tsohon jami’i ne da tun komawar tsohon shugaban kasa Usama D. Hamada mulki na biyu ya shigo jikinsu. Koda yake zamu iya cewa tun a mulkin farko ma yana tare da su, sai dai basu sakin jiki da shi har sai lokacin mulki na biyu da suka tabbatat yana tare da tafiyarsu. Tun usul ya shigo tawagarne akan binciken wani gagarumin ƙulli da akai a wancan mulkin, sun buga sun buga suka kasa gane kansa. Shine yay shigar burtu ya zama ɗaya daga cikinsu. Yaso barinsu bayan kammala mulkin Usama D. Hamada, sai dai ƙullin da suka fara akan daura Alhaji Hameed Taura a mulki ya sashi dakatawa. Duk abinda suke yana biye da su, hatta da ac da suka saka poison a ciki na gidan gwamnati yaso zama silar da zai sa a cire sai Raudha ta rigasa, amma da taimakonsa su bappi suka cire batare da suma sun sani ba. Ya cigaba da tattara bayanan sirri akansu batare da sun sani ba, kuma ko ayanzu da aketa faman kama musu yara duk da saka hanunsa a ciki….
     A firgice duk suke kallon Alhaji Balarabe Andu, dan wasunsu sun ɗauki abin wasa ne ko almara ko subutar baki,
      “Alhaji balarabe kasan mi kake faɗa kuwa?”. Cewar Alhaji Haladu Gwandu.
     Alhaji Balarabe yay wani murmushi tare da rausayar da kai gefe ya tafa hannayensa yana kallon Alhaji Haladu Gwandu batare da yace komai ba. A take jami’an tsaro suka shigo falon suka zagayesu su da makaman da suka tile a tsakkiyar falon wanda a yau ɗin nan aka iso da su ƙasar NAYA…..

         ★Cikin ƙanƙanin lokaci ƙasar NAYA da kewaye ta ɗauki sabon labari na kama waɗan nan manyan mutane da wasun su ko’a hasashen zuciya bata taɓa kawo zasu aikata abinda ake zarginsu da shi ba. Bakin ƴan siyasa ya buɗe ta ko’ina bakajin komai sai kace nace. Abinda ma ya takaice kace nacen tsayawa akan jam’iyya mai mulki kawai waɗan nan mutane gaba ɗayansu suna tarayya ne a cikin mabanbanta jam’iyyu. Hakan na nufin kenan dama ƴan siyasa da yawansu a bayan fage kanwunansu a haɗe yake a zahiri kuma suyita gwara kan talakawan ƙasa da sasu luguden laɓɓa batare da sun hankalta ba. (Ƴan uwa idan zamuyi soyayya muyita dan ALLAH kuma saisa-saisa. Hakama kiyayya muyita saisa-saisa kuma domin ALLAH musamman irin ta siyasa. ALLAH yasa mu cika da imani).

     A yinin wannan rana kawai hankalin al’ummar ƙasar NAYA ya dawo kan shugaban ƙasa Ramadhan. Aka dinga sanbarka a garesa da wanke laifukan da ake kallonsa da su. Yayinda wasu keta faman bankaɗe-bankaɗen abubuwanma da ba’asan da su ba sai yanzu.
      A wani fanin Raudha na farin ciki, wani fanin kuwa tana baƙin cikin kasancewar yayar mahaifiyarta cikin tawagar waɗannan azzalumai. Ga laulayin ciki mai wahala da take fama da shi a wannan karon. Ga karatunsu ya ɗau zafi dan suna lavel 3 ne. har zuwa yanzu kuma bata taɓa kuskuren nunama wani ita wacece ba. Abdull bada shi take zuwa makaranta ba. Gida ake barinsa wajen Mama Ladi. Dama Alhmdllhi yana ɗan takawa zuwa yanzun, damma haƙora na maidashi baya idan yay zazzaɓi. Bayyanar cikin nan na Raudha kuma yasa Anne zuwa ta ɗaukesa a gidan ma baki ɗaya ya koma Taura House yaye. Sudai basu da ikon cewa komai, amma gimbiya Su’adah taji haushi dan ta ƙullama ranta itama abinda akai mata na ƙwace Ramadhan saita kwace Abdull, sai gashi Anne ta sake mata kwaf ɗaya kafin ta farga ta ɗauke ita (????????Bashin gaba lol).

★★★★★★★

           Rayuwa ta cigaba da shurawa su Alhaji Haladu Gwandu na cigaba da zama a tsare a gidan yari, a gefe kuma ana sauraren ƙararsu a kotuna mabanbanta saboda laifukan nasu sunzo daban-daban. Kowanne akwai babban laifin da yake shugabanta da ake tuhumarsa a kansa kai tsaye. Wanda sukai tarayya akai shine cin hanci da rashawa da shigo da makamai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button