KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

? CHAPTER 97?

RECAP

Anyi jungum jungum a parlour kowa na kallon kowa, zayya de magana daya ke ci Mata tuwo a kwarya,? ganin kamar basu damu ba yasa ta gyara zama. Parlourn yayi tsit Dan haka tayi gyaran murya tare da turo baki tace gaskiya ina magana. Wai ya naga kowa yaki ya fadamin sirrin ne? Abinda ya fito na gaba a bakinta ne yasa kowa yasha jinin jikinsa.

YA SAHIR GASKIYA FA DOLE NIMA KAYI MIN CIKINNAN EHE!

CONTINUATION

Bata rai yazeed yayi dukda bece komai ba yayin da minal ta dage goshi domin shirme zayya ya fara fita Mata akai. Zaliha ne ta e ke tashi ki bawa mutane waje bamason rashin kunya. Kallon sahir tayi ya kawo agaji amma baice Mata komai ba sai harara daya falla Mata yabar dakin. Tashi tayi a kufule tana bubbuga kafa da yarfa hannu ta tafi dakinta ta fada kan gado kuma ta sake tana fadin to ni me nayi ? Daga cewa inason na haihu shine ya zama rashin kunya? Kowa bayason ya taimaka mini? Toh AI in kunsan wata bakusan wata ba.

Wayarta ta janyo ta rambatsa ma halsey Kira dukda ko tana jin haushin katin ta da zai kare Dan international call kati yake sha kamar me…. ringing wayar ya fara yayinda take gunagunin gara ta Kira halsey Dan yeonsil sai tayi ta tsokanarta kuma bata wani bata shawara arziki ba. Dauka halsey tayi tare da fasa ihu tace besty har nayi missing dinki, nina kings yanzu na iso kasarmu wai shin kinyi magana da yeonsil kuwa? Me yas……

Zayya ne ta datseta ta hanyar cewa ni duk ba wannan yasa na kiraki ba taimako ko ince shawara nake nema. Gyara tsayuwa halsey tayi Dan a airport ma take tace toooo ina jinki.

Muryan abin tausayi zayya rasa tace kinga ni ina dawowa gida kawai sai na tarar yan biyu na tana da ciki…. halsey tace toooo? Kukam hausawa haihuwar wuri gareki daga aure? AI aurennan ma yayi wuri mukam kinga……..
Zayya tace zaki saurara ko surutu zaki min? Halsey tace toh ina jin ki…. zayya tace toh nima fa so nake na haihu… halsey tace mene? Kee zayya yar yarinya dake kice zaki haihu shekararki sha shida ne fa idan kika fara Yoon fitsari fa? Zayya tace wai ke bakisan zamanin da suma daidai irin shekarunnan suke haihuwa ba? Wasu ma basu kai ba sun mutu ne? Kuma da mutum be kai ya haihu ba ai bazai dau cikin ba nide yanzu shawara nakeson ki bani a garin ya ake samun ciki? Ajiyan zuciya halsey ta sauke tace toh mude a garin mu abinda na sani shine idan mutum yana neman haihuwa bai samu toh sai yaje wajen baita yayi sadaka sannan ya sanar a tayasa addu’a.

Zayya tace toh toh toh na gane… halsey tace ko kuma… zayya tace a ah ya haka ? Kina fatan kar wannan hanyan ta bulle ne da Zaki bani wata? Ki bari na gwada wannan mana. Kashe wayar na tayi tsabar kaguwa bata jira taji sauran zancen ba. Kiran kawarta na tsohuwar makarantar kamin ayi Mata transfer da shike kawar a kano suke.

Tana dauka race Mata ta turo Mata da account number zata tura Mata kudin da za’a ciyar da mutane 20 na kwana uku Allah ya cika Mata burinta.

Kawar Ta ta me suna fati tace ke ko menene wannan buri naki kuma ni ince wa iyayena me? Zayya tace haba fati AI kin fini dabara zakisan abinda zaki fada musu. Kinga kudin da mikewa shi a hannu kenan zan turo miki Dan Allah kiyi min taimakon nan. Fati tace toh shikenan ai. Sannan sukayi sallama.

Shiryawa tayi ta fito har lokacin su minal suna zaune a parlour amma kabir yayi bacci an kaisa daki. Sim sim ta wuce ta dauka basu ganta ba . Ba tare da sun kalleta ba yazeed yace hajiya ina zuwa? Ji tayi kamar ta fashe da kuka Dan bataso sun lura da ita ba. Tsarewa tayi zata fice minal tace kina kara taku daya zan karye miki kafa.

Kukan shagwaba ta fara kamin ta koma dakinta ta fada gado tana kuka. Sahir ne ya shigo fuskar sa a tamke. Rigarsa ya cire ya dale gado baice Mata komai ba. Jin alamun kamar an shigo dakin yasa ta dago kallonsa tayi taga ya kwata ba tare da ya Mata magana ba. Kwafa tayi tace wato kai baka damu ba ma baccin yamma zakayi bayan ni ina nan ina fafatawar yadda zan haihu……

Datseta yayi ta hanyar cewa ke ni banason shirme ance miki haka ake haihuwar? Ko ma zaki haihun a wannan haukar zaki haihu? Ihu ta fasa masa harda bori. Dama nasan ba sona kake ba kawai saboda abbana yace ka aureni yasa ka aureni. Toh ta Allah ba taka ba ko dakai ko ba kai sai na haihu….. tana kaiwa nan ta shige ban daki tare face majina.

Sakan baki yayi yana kallon ta. Shi ya dauka da wasa take ashe de batasan me takeyi ba. Dariya ma ta bashi yace toh sannu fagal dole ma sai dani in ba haja ba sunan danki shege. Ihu ta kara kurmawa yace ke ni fito ki kawomin ruwa insha. Tace anki din….

Yazeed ne ya Kira sahir a waya yace kacewa matar ka idan na karajin giunta saina karya Mata kafafu.
Zama tayi a ban dakin tasha kukan ta koda ta fito har yayi bacci. Cire masa safa tayi ta wulla a kayan wanki tana fatan Allah ya karbi wannan aikin ya bata ciki Dan aikin alkhairi baya yawa baya kadan balle na miji?.

Har tsawon kwana uku kullum sai tayi kokarin fita amma sai an kamata hakan yasa ta Nemo numban malama AMINA (untichlobanty). Tana kira aiko taci sa’a ya shiga, sallama tayi kamin suka gaisa tace dama shawara ce take nema , yaya zatayi ta samu haihuwa? Malama tace maya da fari dai shi haihuwa nufi ne na Allah wato ba’ayi masa dole. Kyautace ya bawa Wanda yaso ya hana Wanda yaso bawai Dan baya sonka ba sai Dan ya gwada imaninka. Wasu sai suyita wahalar nema amma Allah bai basu ba. Wasu kuma basu nema ba sai Allah ya basu da ko wahalar renon ciki basu sha ba. Dan haka ki dage da addu’a sannan kije ke da me gidanki a duba ku domin tabbatar da lafiyar ku. Saide kuma muryanki batayi kama da na babbar Mata ba balle ace kundade babu haihuwa da har zaku fara nema. ku kara hakuri sannan….. kamin malama ta karashe zancenta layin ya tsinke kuma babu wata hujjan Dan ba rashin network bane ashe tabawa tayi da hannunta bata sani ba koda ta dake kira busy ake ce Mata dan haka ta hakura.

Tsalle ta daka tace ashe ashe shine sirrin da aka ki a fada mini wato dai wasu suna Haifa ne wasu kuma Allah ya basu ba tare da sunyi renon cikin ba wato ba tare da sunyi cikin bama. Ita ta dauka haka malama ke nufi batasan malama na nufin ba tare da ansha wahala ba ma Dan a tunanin ta babbar mace ce shiyasa batayi Mata fashin Bali ba.

Shiryawa tayi yauwa kamar kullum ta sansado ta fita aiko Allah ya bata sa’a babu Wanda ya ganta har tabar gidan taxi tahau tace a kaita inda ake samun yara. Shiru yayi sai yayi tunani ko orphanage gidan marayu take nufi . Sai ya kaita can tan saukowa kuwa ranan ana wani celebration Dan haka iyaye da yawa sunzo da yaran su manya da jarirai domin taya marayun murna.

Wata ta gani da ganyen jariri tace la wancan ma ta samu dan haka ta tare ta gaisawa sukayi tace Dan Allah ina kika samu dan nan? Matar tace ban gane ba lafiyar ku kuwa Dana ne.. wuceta tayi tana mamakin yadda shigewarta lafiya lafiya amma kamar tababbiya zayya kam tabe baki tayi tanajin dadi tayi wa yar uwarta wayo ba sai ta wahala ba ma zata samu da.

Haka tayita bin mutane tana musu tambayar mahaukata har aka samu wasu yarabawa suka biyota da gudu sanadiyyar daukan jaririn su da tayi a karkashin bishiya a tunaninta Allah ne ya aiko Mata nata. Har tuntube tayi ta gurde kafa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button