KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

Bayan sun gama cin abincin ne minal tacewa yazeed tanaso taje gidan zaliha yace taje no problem.
Fita tayi yazeed yace ta tsaya a kaita a kafa tace ba damuwa zataje da kafa saboda exercise.
Riko hannun su tayi tiryan tiryan Suna tace Suna hira kankace me sun saba Idan ka gansu zaka dauka ita ta Haifa abin gwanin ban sha’awa. Dukda ko Cewa sahir ya nuna rashin kauna a gareta da farko bata nuna Mara waraiya ba kuma ai ko ba Komai ya nemi yafiya sannan yaro ne shekarunsa 7 ne kawai.
Abakin kofa ta hadu da lukman suka gaisa yake tambayarta ko yazeed yananan tace yananan.
Yace Toh tayi masa alfarma ta lallashi kawarta. A tsorace tace me ya sameta yace sabani Muna samu kamin ya wuce su safwan suka bishi da kallon rashin fahimta. Sahir yace safwan kasan menene ma’anan sabani?girgiza kai yayi yace kai da ka jirmeni ma Baja cani ba balle ni.
Minal ne tace shh bakyau sa ido kunji ? Chocolates ta dauko a jakanta ta basu sannan ta kunna musu TV already an hada tace suyi kallo zata he wajen matar uncle lukman. Zaro ido sahir yayi yace dama aunty baka matar uncle lukman ne? Minal tace aunty baka kuma? Ka dena fadan haka kaji ai baki da fari duk Allah ne yayi mu babu Wanda yafi wani sai Wanda yafi jin tsoransa. Yace Insha bazan kara fadaba amma Gaskiya bakinta dayawa ne ysoro ma take bani. Dariya minal tayi tace karka damu zata Baku sweet. Kaima safwan kaji me nace ko? Yace dama ni bana fada kuma kawatace tun a hospital Dana ganta.
Shiga dakin minal tayi ta sameta tana kuka tace kai zally me haka? Kuka sai kace yarinya ? Idan ma aurenne bakyaso kin kaini ne. Nifa a shashanci na ko mijin ban saniba ma. Dukda banyi nadaman yadda da aurensa ba amma ai sanda na wahalu tukun naji dadi ba gashi yanzu ya wuce ba? Karki damu bari in baki sirrin da zaki sato zuciyarshi da wuri.
Ki tabbata kuna samun body contact koda kuwa kuna fadane hakan ne zaisa ya saba da jikinki yadda duk ranarda baiji dumin fatarki ba zaiji Kamar bayida lafiya Daga nan zaku saba da juna with time har Ku fara lobaiya.
Zaliha tace ni rabu dani waddannan shirmen se ta kaddar Hausa ko film din India. Minal tace yo ke da kike karanta takaddun hausar kenan.
Bari kiji ni shaidace akan wannan ina miki magana ne with experience. Hararar wasa zaliha ta mata tace shegiya kawata nifa banason karyar turanci minal tace dalla tafi can yanzu kin isa ki nunan iya turanci. Zaliha tace Allah baki zanyi tunani akan shawararki. Minal tace ke kikajiyo kinsman dai ba rabuwa zakuyi ba Dan haka gara ki fara action da wuri ko duminsa kidan dinga ji. Dariya suka fashe dashi zaliha kai shegiya kwata kefa yar bara ub*ce da dukum kike ba abinda kika sani ko Dan 10yrs yafi ki sanin harkannan yaushe kika zama yar Hannu ne. Duka minal ta daka mata tace banson ashar ke matsalata dake kenan. Zally tace kinga ni muje muyi yama sunan abin matan manya ? Minal tace me ?zaliha bude ido ta turanci. Dariya minal tayi tace tourism? Zaliha tace shi nake nufi Daga mu dafo abinci. Fita sukayi suka Duba ko ina sunata yaba Kyan gidan suka Duba kitchen akwai Kayan abinci Kamar na sati. Taliya suka daura sannan suka wuce parlour minal tace kawas canjo Maya muyi photon randa kika tare gidanki ko ba haka ba ? dariya zaliha tayi kamin ta wuce zata Shiga zaki minal tace tsafta na kara dankon abin…. Kin gane ai. Zaliha tayi murmushi ta shige tasan love minal kesan Cewa amma saboda su sahir na wajen yasa ta fake.
Bayan ta Shirya cikin Riga da wando hotuna suka sha abinsu sunyi kyau sosai domin minal ma Rolling gyale tayi.
Idan naga comments daya wa Toh za’a sami update dayawa. Har hotan da su kayi ma zan turo muku.
Ina kaunarku sosai?
Takuce karamarsu babbarsu
miss untichlobanty?
14th January, 2020
??KURUCIYAR MINAL??
?by miss untichlobanty?
?CHAPTER 65?
Bayan sun gama hotunansu su sahir ma sukace a watsa musu haka ko akayi suka dinga selfies masu kyau tunda yanzu bazai yiwu a dauki hoton ba dama sahir ne ke daukansu.
Abincin su suka dibo harda su sahir suka zauna a kasa suka lafci jellof din taliyarsu. Safwan ne ya zauna a cinyan minal tare da rungumeta yace aunty minal kakci yabu dani dan Allah, ina conki. Brother kaima kana conta ko ? Daga kai sahir yayi. Murmushi minal tayi tace nima ina sanku kuma bazan rabu daku ba kunji yaran albarka. Safwan yace aunty minal ni a dakinki zan kwana. Safwan yace brother ka manta daddy Cewa yayi mu dinga ce mata mommy? Zaro ido sahir din yayi yace hakane fa na manta ne. Hira suka cigaba dayi abinsu kamin bayan sunyi sallan magrib suka Koma gida.
Tambayansu minal tayi ko sunada home work su kace mata ai sunyi Hutu Al Qur’an ta dauko ta zaunar dasu tace su karanta mata har zuwa Inda suke sai ta kara musu.
Safwan ne ya kalli sahir yace yaya sahir wannan din diccinayi (dictionary) ne?
Hararansa yayi yace dictionary akace. Nazari ya fara yi saboda tambayan Dan uwan nasa kamin yace nima ban saniba sannan ya kalli minal yace momy ai mu bama karanta dictionary a makaranta.
Kallon mamaki minal ke binsu wato Suna nufin basu masan Qur’an ba?
Shafa kan sahir din tayi tare da murmushi tace wannan ba dictionary bane. Wannan littafin addini musulunci ne. Kar duniya babu littafi me tsarki da muhimmanci irinsa kuma yanada anfani ga rayuwar mu baki daya. Da badan shi ba da abubuwa sun tabarbare mana shi yake nusar damu abinda ya dace muyi.
Kallon kurulla suke mata da alamu Suna shanye information din ne. Safwan wato karamin yace momy kinaso kice min shi Kamar guide ne?
Tace good boy you are smart shi din guide ne.
Jinjina kai yayi yace aiko mommy Idan haka ne Daga yau kullum sai na kayantashi kuma Nayi alkawari zanyi aiki daci dadai gwaigwado.
Sahir yace nima haka na miki alkawari momy.
Dadi minal taji sosai ganin yadda yaran ke son karatun addini kuma itama tayi alkawari zata yi dai dai gwargwadon ta wajen koyar dasu.
Shaking hannunsa tayi tace Toh zamu fara haddacewa yanzu zanga Wanda zai Riga haddacewa duka kuma banida burin daya wuce Idan kun haddace in koya muku fassaransa sannan zamu dinga yin saura littafai sau 2 a sati sauran 5 days kuma na al Qur’an ne.
Dadi sukaji safwan yayi saurin rarumar Qur’anin ya bude Jade fuska yayi yayinda minal ta karba tace safwan my boy yara basa taba Qur’an izu sittin kaji. Yace momy menene izu 60 kuma? Tace zan fada muku yana Qur’an yake amma dai izu sittin shine complete Qur’an oya Ku gyara zama mu fara.
Nan fa minal ta fara musu Daga suratul fatiha amma abinda ya bata mamaki shine har sun haddace Bismillah da aya uku. Idonta har cikowa yayi da haiwaye na tausayin yadda rayuwarsu ta kusa tabarbarewa saboda ba’a nuna musu addini ba dukda ko Suna da kai me Kyau. Lallai tabbas akwai abinda Allah ke nufi dasu daya hadasu fatanta dai Allah yasa alkhairi ne.
Sahir ne yace Toh momy me yasa aka rubuta kur’anin bada English alphabet ba. Tace saboda bada English aka sauketa ba an sauke ne a larabci. Safwan yace Arabic kenan tace eh yace amma ai ni ban iya Arabic alphabet ba lokacin da nacewa daddy na ya koya mana sanda muke London yace bayada anfani a garemu kuma bayida lokacin mu muje uwar mu ta koya mana kuma da mukaje muka sami mommy mukace ta koya mana tace bata iya ba.