KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

Murmushi tayi jin zantukan yazeed hakan yasa ta juyo domin taga waye sannan raji dalilin da yasa sai mutane sun fita zaiyi siyaiya amma me tana ganin yazeed ne tace wow! Daidai kenan dama kere na yawo zabo na yawo wata rana zasu hadu. Wato shine Dan wulakanci ranan nan ka dauki hoto na mai makon kace min man baki na ya baci wato ga shashasha ko?

Jin hayaniya yasa manager yazo dubawa ganin minal ke fere yazeed yasa yace security ku fita da ita hannu yazeed ya daga musu. Itako sands tamai tastas ta hankade keken siyaiyar nata wa manager sannan ta kalli yazeed tace kaikuma karka bari mu hadu a karo na uku mtsww, Sannan ta fice tana cika tana batsewa.

Feena ne tace yaya me ya faru, kauda kai minal tayi tace ashe wannan Dan renin hankalin daya Dakar mini mota na ne. Feena tace kina nufin yazeed abdulmajeed ne ya daki motar ki? Waiyo dama nice. Tsaki minal tayi tace ya akayi kikasan cewa banzan yazeed dinku ne? Feena tace da farko dai wasu yan nata ne naji suna cewa shine. Ba biyu kuma ba banza bane me kudi ne kuma…. minal ne ta datseta ta hanyar cewa karma ki fara banasonji kar kunnena suyi ciwo.

Yazeed kuwa a hanyarsa na zuwa gida ya Kira secretary dinshi yace ya batun personal assistant dinnan kowani department sun bada sunan masu hazaka? Secretary din yace eh yazeed yace this time around ni zanyi musu jarabawan da kaina Dan na gaji da canje canjen P.A dukansu kasalallu ne basa son aiki ko kadan.

Washe gari minal tana zuwa office aka miko Mata letter dinta akan cewa vacancy ne na PA din president kuma tana cikin masu hazaka idan tanaso toh karfe 10 am taje floor na Goma sha biyar wato na karshe anan zataga sauran abokan aikinta masu neman mukamin.

Karfe 9:45 ta shiga lifter domin zuwa floor din, ba kowa yake zuwa haka kawai ba sai da dalili Dan haka bata taba hawa nan ba. Lambobin ta duba taga daga floor na 14 ya tsaya. Fitowa tayi ta tambayi yadda ake zuwa sama aka nuna Mata wasu lifts guda biyu bata lura da rubutun dake sama ba kawai ta shige daya gani tayi tsarinshi daban ne harda kujera tace ikon Allah mutane da securities ne suka fadin wait! Dakata amma ina ta Riga ta danna top floor Dan haka ya rufe. Hankalin kowa ya tashi yau karamar ma’aikaciya ta shiga lift din president! Securities har wani zawo zawo sukeji.

Tana Isowa floor din ta fito abinda ta fara haduwa dashi shine secretaryn yazeed da wata assistant dinshi sun minke hannu kowa yana jira yaga wacce ta kawo hayaniya cikin building din. Harara assistant sin ta aika Mata yayinda secretary yace malama juya ki karanta saman kofan da kika fito. Karantawa tayi taga an rubuta PRIVATE ELEVATOR wato na musamman ne. Murmushin jin kunya tayi kamin tace yi hakuri ina sauri ne ban tsaya na karanta ba. Dan murmushi yayi yace ba komai amma ki kiyaye tace insha Allah.

Layi tazo tahau ta tsaya taga kowa sai gyara kwalliya ake tace wadannan ko lafiya sukewa tsoho kwalliya? Sunayensu aka fara Kira ko wacce ta shiga sai ta fito tana kuka, Kazan kuwa jiki a sanyaye suke fita sunan minal aka Kira ta shiga tana fargaban wani tambaya akeyi da yakesa mutane kuka da mutuwar jiki.

Kamar wadda kwai ya fashewa a ciki haka ta shiga saide kujeransa ba ita yake fuskanta ba baya ya bata wato yana kallon gari ne tunda ofishin nasa bangare daya glass ne. Cikin kakkaurar murya kuma kamar ya gaji da yin maganan yace idan akwai jagwalgwalon da kuke Kira kwalliya a fuskarki toh ki fita ko jarabawar baza’a miki ba idan ko babu to kalli gefenki na dama. Babu musu ta aikata hakan kujerace akai akwai laptop da kuma files guda 10. Yace kalli agogo karfe nawa ne? Tace 11:50 yace mun rasa soft copy na wadannan files da kike gani Dan haka so nake kamin karfe 12:30 ki sake typing duka idan kuma bazaki iya ba toh KEMA GA HANYA!

HHHH TYPING IS NOT EASY! KARKU MANTA KUYI COMMENTING DA KUMA SHARING.

NAJI WASU SUNA CEWA SUN ZAMA CONFUSE PLS KU FADAMIN ABINDA YA RUDAR DAKU DOMIN AYI MUKU BAYANI.

ONE LOVE?

miss Untichlobanty ?

16th April, 2020.

+2347069510076

??KURUCIYAR MINAL??

?by miss untichlobanty?

?CHAPTER 92

RECAP

Yana fita yayi dariya yace yan Matana aci chewing gum lafiya yana Mata dariyar mugunta. Itama a bangaren ta yana ficewa tace sai kace ban sanka ba kawai zan yarda cewa ka hakura. Hmm nasan so kake kabi dare ka cinye dan haka gadi zanyi sannan tayi ma kofar gwaliyo.

CONTINUATION

A asibiti kuwa ayush tasha plasta a mazaunai sannan kar ta dinga zama saide kwanciya ko tsayuwa. Tafiyar ma gwale gwale takeyi Kamar yar kaciya. Wayarta ta dauko taga missed call aciki harda na Dan iskan mijinta wai ya dawo daga Mali. Tun shekaru biyar da suka wuce ya tattari tarukucensa ya tafi neman Mata ta da harkar gabansa da sunan kasuwan ci saida ya kwaso kanjamau tukunna ya lallabo ya dawo.

Bayan sun kammala wayar ne taga cewa wata number ta Mata missed call Kira tayi bugu biyu aka dauka tare da fadin barka da war haka hajiya ayush ashe de baki canja lamba ba.

Ayush ne tace wai wa ke magana? Dariya akayi ta dayan bangaren tace hehehe su ayush manya shekaru nawa ne har kin manta da SUMAYYA? Ayush tace wace sumaiya kuma? Tace summy de guda da kika sani yar lesbian yanzu kuwa magajiya ce.

Dafe goshi ayush tayi a ranta tace mutum na fama da wata matsalar sai wata ta kunno kai. Daidai lokacin mamata ta turo kofa ta shigo dakin da take hakan yasa ta dawo daga tunanin da ta shiga tace toh summy kike ko wa ya akayi? Summy tace ya akayi? Lokacin da na yi miki aiki ba cewa kikayi idan kin samu dani za’a raba ba? Jini shiru yasa na share na bar kasona tare da ke a matsayin ajiya yanzu ko fatara nake babu kasuwa sosai Dan haka so Nike ki bani. Ayush tace turo account number ki. Summy tace ance miki cikin sauki zan karba na wuce AI wallahi gidan da kike nan zan zauna kima San yadda zakiyi ki shigar dani ayush ta kunduma ashar tace bara in kashe wayar muga tsiya. Summy tace wallahi ko bakar magana kika kara yi min wallahi sai na zo na miki tone tone.

Iska ayush ta fesar tace naji zanga yadda zanyi sannan ta kashe wayar baki daya.
Mummy tace waye ne? Ayush tace waye kuwa banda wancan yar iskar wai ita summy. Mummy tace wacece kuma summy? Tace wannan yar iskar de wacce tayi min aiki akan zakiyya tayi kokarin kwanciya da ita. Tattaunawa sula ci gaba da yi na yadda zasu tsere daga tarkon summy.

Da daddare zayya tana kwance ta rufe Rabin jikinta da bargo taji sahir ya shigo, likimo tayi tana kallonsa yaje wajen Jakarta kamin ya dawo ya kwanta. Bayan minti biyar ta tashi da sauri ta duba chewing gum dinta yananan wani paper ta gani Wanda batasan dashi ba ta dauka. Muryarsa ta jiyo yace finally zan rabu da alakakai dama Dan daddy yayi aure na aureki badan raina yaso ba. Gabanta ne ya fadi hannu na ruwa idonta ya ciko da kwalla tace sakina kayi? Yace duba ki gani ko guda nawa ne sannan yayi kwanciyarsa? ko a jikinsa.

Kafarta na rawa ta dosana mazaunanta akan gado ta bude paper ido shame Shame da hawaye ta karanta kamar haka.

“Zayya manyan Mata gara ma ki tashi Dan nasan ba bacci kikeyi ba fadin cingam kikeyi. Karki dauka Dan na aureki contract din mu ya kare dole ki karashe. Dan haka so nake yanzu ki hadomin shayi.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button