TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL
???????? TAGWAYE ????????
Episode One: The Bad Dream
Free episode
Bismillahir Rahmanir Rahim
Ina rokon ubangiji ya bani ikon gama littafin nan lafiya kamar yadda ya bani ikon fara shi lafiya. Ina kuma rokonsa ya bani ikon rubuta alkhairi, ya haneni ga rubuta sabo.
Ga masu bin rubutu na tun a Maimoon, zaku fahimci cewa a cikin wannan labarin mun koma can baya ne mun dauko wani zaren labari da muka ajiye, yanzu zamu jawo shi mu hade da sauran labarurrukan mu. We are going far back in time. Please bana son jin “a zamani kaza babu kaza da kaza” saboda ni ban fadi a wanne zamanin labarin ya faru ba. Babu littafi na dana rubuta shekara. Just read and understand.
We are going to look at life from the villain side of the story.
Let’s be villains. Lol
ILYSM
Tafiya yake yi, yana jin jikinsa cikin yanayin tafiya amma kuma baya jin alamar ƙafafuwan sa suna taka kasa, jinsa yake yi tamkar wanda yake shawagi a sama, wannan yasa yayi saurin bude idanunsa da da suka kasance a rufe, idanuwansa suka sauka a kan fuskar ta. Yaji wani abu da baisan menene ba ya taba zuciyarsa a dai dai gurin da ba’a taba taba masa ba. Ya kura mata idanu yana son ya haddace dukkan kamannin ta a lokaci daya amma ya kasa, gashi dai yana kallon ta amma baya ganinta, so yake ta kalle shi ko yaya ne ya samu ya kalli cikin idonta amma taki kallon nasa. Wannan yasa ya bude muryarsa da niyyar yi mata magana ko Allah zai saka ta kalle shi koda kallo daya ne, ko da na second daya ne, ko yaya ne.
Amma ga mamakin sa, maimakon yaji murya ta fito daga bakinsa kamar ko da yaushe in yayi magana sai yaji kuka ya fito, kuka mai dauke da sauti irin na jarirai.
Cikin mamaki ya sauke idonsa kan jikinsa, sai a lokacin ya fahimci dalilin da yasa yake jin kamar yawo yake yi a iska, yake jin yana tafiya amma baya taka kasa, ashe shi jariri ne, ashe a rungume yake a hannun wannan matar da ta taba can cikin zuciyar sa. Sai a lokacin ya fahimta, ashe mafarki yake yi.
Mafarki yake yi da mahaifiyar sa, abinda bai taba yi ba tunda yake a duniya, wannan fuskar da yake kalla amma ya kasa gani fuskar mahaifiyar sa ce. Wannan ya saka shi ya sake rudewa tare da sake dagewa wajan tattaro dukkan karfinsa dan ya yi mata magana ya samu ta kalle shi amma sai kokarin nasa ya kare a canyarewa da kukan jariri.
Ba tare data kalle shi ba ta saka hannu tana dan jijjiga shi kadan da niyyar rarrashi, fuskarta cike wani yanayi da yayi masa kama da tsoro, fargaba hadi da damuwa amma sam babu soyayya a fuskarta ko da ta digon alkalami.
“Why?”
Yayi kokarin tambayar ta a cikin muryar sa ta kukan jarirai. Wannan itace tambayar da yake da burin yi wa mahaifiyar sa a duk ranar da Allah ya hada su.
“Me yasa ba kya so na me nayi miki?”
Maimakon ta amsa masa sai yaga ta jawo bakin dankwalin ta da tayi amfani dashi gurin rikon sa ta rufe masa fuska dashi yadda ganin nata ma ya daina. Nan ya fara kusur kusur da harbe harbe irin na jarirai a ransa yana burin sake ganin fuskar ta. Har ya samu ya bude fuskarsa, sai ya kalli gurin da suke tafiya.
Gefen titi ne, kuma daga dukkan alama cikin dare ne dan gurin yayi duhu sosai amma yana lura da bishiyoyin da suke wucewa alamar wajen gari ne. Sanyi yake ji yana ratsa jikinsa saboda kasancewar babu kaya a jikinsa sai dankwalin da ta rufe shi dashi.
Ya hango fitilar mota ta taho, sai yayi murna a ransa yana tunanin wani ne yazo zai taimaka musu sai dai ga mamakin sa sai yaga ta yi sauri ta buya a bayan wata bishiya, sannan ta saka hannu ta toshe masa baki dan hana kukansa fitowa, numfashin sa yaji yana kokarin daukewa saboda cikin rashin sani ta hada ta rufe har hancinsa wannan ya saka shi harbe harbe da kokarin kwace kansa amma bata cika shi ba har sai da motar ta wuce.
Data bude masa baki da hancin ko kallon fuskarsa bata yi ba………..
Gajiya da wahala ya saka ya kwanta lamo yana maida numfashi yayin da ita kuma ta cigaba da tafiya. Suddenly yaji ta tsaya. Ya kalli inda suka tsaya din sai yaji zuciyarsa ta buga da karfi.
Ba zai taba manta gurin ba, dan shine inda ya fara kira da kalmar “home” a rayuwar sa. “Nigerian National Orphanage”. Tsohon gate din gurin ne da kuma tsohon ginin. A hankali yaga tana bin jikin katangar dan kaucewa hasken fitilun da suke gurin, yayin da hannunta yake rufe a bakinsa. A dai dai kofar ta tsaya sannan without thinking twice ta durkusa ta ajiye shi a kasa.
Tana ajiye shi ya dage da duk karfinsa yana kuka, yasan me take yi, amma ba wannan me damuwarsa ba, damuwarsa shine rabuwa da ita, rabuwa da dumin jikinta. Burinsa kawai a lokacin shine ta kalle shi, ko da sau daya ne, ko da second daya ne, ko yaya ne.
Bata kalle shi ba bata taba shi tace “good bye” ba, asali ma hankalinta a tashe yake kar wani ya ganta, burinta shine tayi sauri ta bar gurin. Yana ji hannunta ya bar jikinsa and his heart went with it.
Kuka yake sosai, kukan da bai taba sanin cewa ya taba yin irinsa ba sai yau. Sanyi yake ji, tsoro yake ji. Cikin kukan nasa ne yaji takun mutum, wannan yasa ya sassauta, a hankali fuskarta ta kuma bayyana a gare shi tana tsaye a kansa, wani irin dadi yaji a ransa wanda bai taba jin irin sa ba, ashe dai tana sonsa, ashe dai tace
“good bye my son, ina sonka sosai zan rabu da kai ne kawai dan dole ba dan zuciya ta na so ba amma nayi maka alkawarin zan dawo gare ka”
Wannan sune kalmomin da kullum yake gaya wa kansa a matsayin wanda mahaifiyarsa ta gaya masa sanda zata yar da shi.
Amma maimakon haka, sai yaga ta durkusa ta zare dankwalin ta data lullube shi dashi, sannan ba tare data kalle shi ba, ba tare data ce komai ba, ta ruga da gudu ta shige cikin bishiyoyi……….
Wani azababben sanyi yake ji, wani irin kuna zuciyarsa take yi. Tsakuyoyi da kasar gurin suna sukar fatar jikinsa. Sai a lokacin ya lura da ko cibiya bata yanke masa ba daga shi har mahaifar sa ta yar.
Kuka yake yi, kuka wanda zai ratsa zuciyar duk wanda zai ji shi a lokacin.
Amma banda zuciyar wadda ta ajiye shi.
Banda zuciyar wadda yake ganin tafi kowa kusanci dashi a lokacin.
Wadda yake tunanin zata fi kowa son shi.
Mahaifiyar sa.
A firgice ya farka. Kukan jaririn ne ya farkar dashi, kukan sa. Ya tashi zaune gabaki daya jikinsa yana kakkarwa yana jin sanyi yana ratsa kasusuwansa tamkar yadda yaji a cikin mafarkin. Ya jawo gwuiwoyinsa zuwa kirjinsa sannan ya dora kansa akan gwiwarsa a hankali yana kiran sunan ubangiji har yaji nutsuwa ta fara zuwa masa sannan ya karanto addu’ar da annabi ya koyar cewa ayi idan anyi mummunan mafarki.
Lallai wannan mummunan mafarki ne, bai taba yin irin wannan mafarkin ba, irin mafarkin da zaka yi kaji tamkar gaske ne amma kuma kasan mafarki ne. Bai taba mafarki da mahaifiyar sa ba. Bai taba ko da tunanin ta irin haka ba. A cikin mafarkin fuskartar babu ko da digon sonsa ne, babu tausayinsa ko kadan.
Kullum in tunanin iyayensa yazo masa yana consoling kansa ne da cewa dole ce ta raba su, suna sonsa amma babu yadda zasu yi shi yasa suka yar da shi amma wannan mafarkin ya goge wancan tunanin.
Ya mike yana taka lallausan kafet din dakinsa ya wuce zuwa toilet ya wanke fuskarsa da yake jin ta dauki zafi kamar mai zazzaɓi. Sai ya samu kansa da karewa kansa kallo a cikin mudubin gabansa. A hankali ya furta “Amir, mafarki kayi ba wai gaskiya ba ne ba” wani bari na zuciyarsa yace dashi “idan kuma ba mafarki bane ba memory ne fa?”