TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Daga nan part dinsu ya nufa, ya shiga palo yana karewa luxurious kujerun da suka kawata falon kallo, amma last dawowar Hussain daga Japan yana shigowa palon cewa yayi “what? Wannan kujerun har yanzu ba’a cire suba? Wadannan ai sun zama old models yanzu sam ba’a yayinsu” Hassan yayi murmushi yana jin kewar danuwan nasa, Hussain sarkin rikici. Ya bude kofar dakinsa ya shiga, komai tsaf tsaf kamar yadda ya barshi. Yayi wanka ya chanja kayansa zuwa kanana sannan ya fito ya rufe dakinsa ya shiga na Hussain. Komai na dakin abin kallone, ko bakasan kudin kaya ba kana shiga dakin zaka san cewa tabbas an kashe kudi a gurin tsara dakin zuwa kayan da aka zuba a ciki. Sanda Hussain zaiyi renovating babu yadda baiyi da Hassan ba amma yaki yarda a gyara masa nasa dakin “ni dakina babu abinda yayi bana bukatar a gyara min shi, wannan ai almubazzaranci ne, Ni fa da ka ganni yanzu zan iya yin 10 years nan gaba ba tare dana chanza komai a dakina ba”.
Sai dai Kamar yadda Hassan yayi tsammani a hargitse dakin yake, kaya sun kai set goma duk a baje a kan gado kuma yasan duk a kokarin shirin zuwa gurin Gimbiya ne aka hargitsa kayan. Yayi tsaki kawai ya wuce wata drawer ya dauko takardar da yazo nema, sketch ne na sabon companyn da ake gina wa wanda kusan an gama komai yanzu, finishing touches kawai ake yi. Ya dauka ya fita, a compound din gidan ya kira wani amintaccen yaron su Salisu, salisu tun babansu yana da rai yake gidan shi da babansa, bayan rasuwar baban nasa sai Hassan da Hussain suka cigaba da zama dashi a matsayin amintaccen su wanda shi kadai yake da access da dakunan kwanan su da abincin su da komai nasu da yake personal, yace “kaje ka gyarawa Hussain dakinsa, ni zanje site sai magrib zan dawo” sannan ya ja motar ya tafi.
Site din ginin ya tafi. So yake yaje yabi ko ina ya tabbatar yadda aka yi sketching din haka aka yi aikin. Dama sunyi waya da engineer dan haka already a can ya same shi sai dai ma’aikatan sun fara tafiya gida tunda magriba ta fara gabato wa. Haka suka yi ta zagayawa sako da lungu na gurin Hassan yana yi yana duba sketch din hannunsa a tsanake duk inda yaga kuma ba’ayi dai dai ba sai yayi magana sai engineer yayi masa bayani in bayanin ya gamshe shi shikenan in kuma baiyi ba yace a gyara. A haka har suka gama, engineer yayi masa sallama ya tafi shi kuma ya tsaya ya dan yi rubuce rubuce a takarda ya saka a cikin sketch din sannan ya fito.
Sai daya fito sannan ya lura da yadda gari yayi duhu, masallatai ana ta sallah wasu ma har sun idar. Da sauri ya bude motarsa yana jin takaicin missing jam’i da yayi, ya ajiye takardar hannunsa a kujerar kusa da driver sannan ya zauna a kujerar driver yana zura key a jikin ignition.
Wani abu mai sanyi yaji ya taba wuyansa, sanyi irin na karfe. Da sauri ya kalli side mirror sai idanunsa suka sauka a kan yar karamar bindiga da ake kira da pistol, bakin bindigar a rufe da silencer. Zai iya cewa bai taba ganinta a zahiri ba sai yau ballantana ya taba ta amma yana ji a finafinai cewa karfenta sanyi ne dashi sai gashi yau ya tabbatar, sai dai abinda basu fada a films din ba shine yadda sanyin yake wucewa har cikin zuciyar mutum. Ya runtse idonsa ya bude, yana tunanin Hussain, ko yaya zaiyi copping da labarin mutuwarsa?
Murya yaji dai dai kunnen sa, cikin rada amma kuma da kakkausan amo “take your hand of the ignition and place it on your head” a hankali yabi umarnin da aka bashi, ta gefen idonsa yaga wani ya bude kofar gefen driver ya shigo, bai juya ya kalleshi ba amma daga yadda motar ta amsa zaman nasa yasan cewa katon gaske ne, yasan ba zai iya tarar sa da fada ba ballantana kuma gashi su biyu ne da wanda ya saka masa bindiga a wuya. Amma yasan da Hussain ne da zai gwada, zai gwada ko da kuwa chances dinsa na winning is 1% in yayi failing ma zai sake gwada wa, amma shi ba zai gwada ba, shi yana analysing situation dinsa ne kafin ya gwada sa’ar sa kuma wannan karon baya jin akwai Sa’a.
Yaji alamar wani ma ya bude baya ya shiga, su uku kenan, yayi shiru yana jiran yaji instructions din da zasu bashi amma basu ce komai ba sai kawai ji yayi wani hannu rike da wani tsumma ya zagayo ta baya ya rufe masa hanci da bakinsa. A jikin tsumman ya shaki kamshin wani abu, kamshin da yayi bringing back memory din lokacin da suka je South Africa shi da Hussain, lokacin da suka je kallon namun daji a reserve dinsu, lokacin da wani tiger ya tsallake shingen da aka yi masa yana kisan sauran dabbobi sai aka watsa masa wani abu mai irin wannan kamshin. Ya tuno sanda ya tambayi mutumin game da abin sai yace masa dashi suke amfani dan suyi knocking down dangerous animals, sai ya gaya musu cewa “masu satar mutane ma dashi suke amfani su fitar da mutum daga hayyacin sa dan suji dadin satarsa” ya tuno sunan da mutumin ya gaya musu “sunan sa chloroform”.
Da sauri Hassan ya dauke numfashin sa yaki shakar abin ya kuma fara amfani da hannayen sa dan ganin ya cire tsumman daga fuskarsa amma sai mutumin ya kara danna masa shi wanda ya zauna a gaban kuma ya fara kokarin rike hannayen sa, tunanin Hassan daya a lokacin, tsoron sa daya a lokacin shine kar su sace shi suyi amfani dashi gurin cutar da Hussain. Shi farko ya dauka robbers ne sai yanzu ya fahimci kidnappers ne. Yaji sunyi magana a tsakanin su amma bai fahimci mai suka ce ba sai dai kuma yaji muryar wanda yake bayan tamkar muryar wanda ya sani, wanda ya sani sosai amma ya kasa placing.
Sai yaga sun dauke hanky din daga fuskarsa sannan na bayan ya saka hannayen sa biyu yayi amfani da duk karfinsa ya shake wa Hassan wuya yana toshe masa hanyar wucewar iska zuwa huhunsa, Hassan yaji kamar zai mutu, kwakwalwar sa ta totse kirjinsa kamar ana hura wuta a ciki babu abinda yake so illa ya shaki iska amma sun hana masa, ya yi tunanin this is what suffocating feels like, this is the end of him. Regret dinsa daya a rayuwa shine baiyi aure ya bar yaya ba kamar yadda yake da buri, sai yaji cewa ashe Hussain is right akan kayi komai a lokacin da ka samu dama kar ka jira sai wani lokacin, sannan yayi wa kansa alkawarin indai har yayi surviving the first thing da zaiyi shine aure, duk yarinyar data fara kwanta masa a rai ita zai aura.
A lokacin daya gama saddakar da tafiya lahira a lokacin ne kuma suka cika masa makogwaron sa sannan suka yi placing wannan jikakken hanky din a kofar hanci da bakinsa. Farkon abinda ya fara kokarin yi shine shakar iska zuwa huhunsa da yake ji on fire, wannan yasa ya shaka da karfi, ya kuma shaki abinda baya so din har cikin huhunsa. Ya jima yana shaka, a kokarin sa na dawo da numfashin sa dai dai, a lokacin da numfashin nasa ya fara dawowa dai dai a lokacin ne kuma hankalin sa ya fara gushewa, a lokacin ya fahimci cewa ya shaki chloroform din.
Ga masu son siya zasu iya turo kudinsu ₦300 ta account
GT Bank
Account Name : Nafisa Usman Tafida
Account Number : 0139433741
Sai su turo shaidar transaction din ta hanyar WhatsApp zuwa wannan layin
08067081020
Wadanda basu da account zasu turo katin MTN na ₦300 zuwa wannan layin
08067081020.
???????? TAGWAYE ????????
By
Maman Maama
Episode Seven : Lost
Free Episode
Sai da suka tabbatar jikinsa ya gama saki, suka mammare shi a fuska suka tabbatar babu alamar motsi a tare dashi sannan suka cika shi, suka bude booth din motar suka jefa shi a ciki roughly sannan suka shiga motar suka bar gurin. Babu wanda ya gani, kasancewar babu kowa a cikin building din sai masu gadi guda biyu da sun tafi sallah basu dawo ba, dan haka basu samu matsala ba suka yi tafiyarsu.